HAUSA NOVELS SOKOTO WHATSAPP: 07068808039 Queen Safiyyert馃憫: A BAK'IN AUREN KI... 漏Feenat Ja'afar. 1_Sauri take tamkar taci da k'a, kai daga ganinta ka ga marar gaskiya, a d'ai d'ai layin da zai sadata da gidanta ta t'saya tamkar munafuka ta d'an leka, da sauri ta komar da kai tare da dafe kirjinta mai barazanar fashe mata... "Na shigesu.. Ja'afar? Ta fad'a tana mai sake lekawa, sai karaf sukai ido hud'u dashi,tuni buguwar zuciyar ta ya k'aru, bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba. "Mey yasa kika fita bayan yace ka'rki fita?... Bak'in g'yalenta tasa tana t'sane gumin dake t'sat'safo mata, cikin jihadi ta fito daga inda ta boye harda d'aure fuskarta tamkar bata ganshi ba. Kanta na k'allon gefe tazo d'ai d'ai kofar gidan zata shige ba tare da ta k'alli yanayin nashi ba.. Turus taja ta t'saya, ganin yadda ya d'aura wani mukulli kan wanda ta rufe gidan dashi, cikin k'arfin hali fuskarta na gefe tace "ya haka? Wanda bai nan ma yafita,hakan yasa ta kara fad'in "Ya Ja'afar ya haka?.. Tamkar kububuwa yake cika, ji yake tamkar ya rufeta da duka dan takaici, Ashe d'uk uban rat'suwar Salma ta mai kan ta d'aina a fatar baki ya t'saya?.. Mota ya bud'e yana ko'k'arin shiga ta mot'so da sauri, "Ja'afar magana nake fa... A tunzure ya juyo da nufin kifa mata mari tai baya da sauri gabanta na fad'uwa. Lalle yau ta ta6o ran y'an maza, cikin bacin rai yai mata k'allon banza, "kin za6i gidan suna sama da sharad'i na koh? Toh mey kika dawo yi min gida? Koh kin manta da sharad'in da na baki na in kin fita toh kin fita "A BAK'IN AURENKI?... Ido ta zaro tana dubenshi, kawai sai ta dake, cikin k'arfin hali tace "A BAK'IN AURENA fa kace Ja'afar? Daga gidan sunan shine har kake wannan kumfar bak'in?.. Ta karasa tana y'atsine mishi fuska,kawai sai ya k'ada kai ya shige mota. Ganin da gaske tafiya zai yasa da sauri t ajiye t'siwar ta fara kiranshi, ina,tuni ya juya a kalar motarahi cikin zafin nama, da sauri ta mat'sa ganin sai ya iya bi ta kanta.. Tana ganin da gaske yake hakan yasa tuni ta t'sure, hannu ta aza bisa kanta cikin nadamar fitar da tai sunan da ba'a ma gaiyace ta ba, "na shiga uku ni Salma.. Na ja ma kaina wani bala'in.. "Yanzu igiyar Aure na biyu ta t'sinke kenan?.. Tuni zufa ta kara zubo mata dan tunawa da kalaman Babanta, "d'uk randa zaki kara maimaita haka Salma sai na 6alla kafarki in kin doso gidana.... Fad'uwar gabanta ta t'sananta,t'saf Baba zai aikata mata hakan, ta k'alli gabar,da yamma, ta ma rasa ta ina zata fara? Gefen dakalin gidan ta d'an dosana, da d'ukkan hannunta biyu ta dafe kai,tuni kalaman Ja'afar ya dawo mata, "in kin fita kin fita A BAK'IN AURENKI.... Ku biyoni Bayan sallah dan jin yadda zata kaya... By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 8:46 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *3*- Kai ya k'ada mishi, _"aure ba shine mafita ba Ja'afar,ka g'yara wacce ke hannunka tukun,bana tunanin wannan shawara ce_. Murmushi yai tare da k'ada mishi kai _("I know)_.. _"Amma ka gane ba dan dad'i zanyi ba,nasan d'uk duniya ba abinda Salma taki jini irin nace zan kara aure,dole na d'andana mata mad'acin da ta d'andana min nima_. Murmushi Garba yai yana K'allonshi,wai yau Ja'afar ke maganar zai d'andanawa Salman sa mad'aci?.. Kai ya girgiza, lalle Salma tai wasa da damarta, dan yasan irin dimbin son da Ja'afar ke mata, sai dai gashi za a kaita a baro,dan ta fara sane ma abokinshi.. _"Bana tofa tawa ba nikam,nasan da kai da Salma sai Allah,ni d'ai kai tunani abokina,kar ka yanke hukunci cikin fushi azo daga baya ai nadama_... Baki ya ta6e, kan ya ciro mukulli a aljihunshi ya mika mishi, _"k'ar6i mukullin motarka,dan aure kam nayi na ma gama,kuma *Bintu* zan aura kasa ido_.. Ido waje Garba yake k'allonshi,kan ya k'yalk'yale da dariya, _"lalle ka d'ebo aiki..za kuma ka dasa ma Salma zargin ka cikin ranta tunda kasan komai_... T'saki yai kan yace _"zanso hakan ya kasance, dan zata fi jin haushi sosai_.. Kai Garban ya k'ada yana kunshe dariya, _"muje na sauke ka toh na Salma da Bintu,kai (scene) din nan zai dad'in k'allo wallahi_.. Ya karasa da dariyar keta. Murmushi kawai yai suka shiga mota,har suka isa gida Garba na mishi t'siya..da ya had'o shi da Salma zai kicin-kicin. ************************ A wajen Salma kuwa,sai da dare yai tana k'wance d'akinsu na da sai juyi take,wanda ita kanta ta rasa dalili,har yanzun haushin Ja'afar na kasan ranta na ya mata wulakanci, sai dai da ta tuna rabuwar igiyarta d'aya sai taji fad'uwar gaba. Yau gata a katifa ba ta ita da Ja'afar d'inta ba?..yau d'aya ta raba alakar matashin kanta(kafad'ar Ja'afar) sai pillow... Hannu takai kuncinta,da mamakinta hawaye take,kawai sai ta ida karasawa ta fashe da kuka.. Wanda kai da gani na k'ewar Jafaririn ta ne da t'sant'sar nadama,amma ina,zuciya taki amsar hakan.. Ga uban sauro da ya damu k'unnenta da ihu duk da da Katanga a t'sakaninta dasu(net), ga uban zafi ba wuta ba (Gen), d'uk t'siya tasan da a gidanta ne da yanzu tana shan iskar injin da Ja'afar ke k'unna mata d'uk dare ta k'wanta dan bata bidar zafi.. Ga mama tace ba mai tada mata inji Babanta baya gari, kuma bata kud'in mai... ***""* Shima hakan take ga Ja'afar, kusan a hali d'aya suke,sai dai shi kawai ya kura ma fankar d'akin da ke kad'awa a saman d'akin ido. Tabbas har yanzun baida sama da Salma koh a kasan zuciyarshi.. Yana sonta, so marar misali,duba ga yadda suka gina soyayyar tasu kamin aure.. Da za'a ce mishi a da Salma zata sauya hali gaba d'aya musamman akanshi da zai mu sa... Juyi yai ya jawo filo,d'uk t'siya tanan yai k'ewar Salma.. Dan karamin t'saki yai kamin ya tashi yai waje dan kashe inji. *By* *Feenat Ja'afar* 9/29/16, 8:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 4- Salma Umar Y'a ce ta biyu gun Mama(Haj Rabi'a) da Baba(Malam Umar),y'an asalin Yobe ne,kasuwanci ya kawo kakansu Kano da rabon su Salma. Su biyu kawai ne a gun kakan su Malam Bukar Mai buhu,baban su Salma ne karami, sai yayanshi Baba Aji, yaranshi a kallah za suyi (16),yayin da Baban Salma ke da uku,Aisha (Aunty A'i)dan tafi Salma sosai,Salma,sai Ummi. Kasuwanci ne gadon su Baba,dan koh bayan rasuwar kakan su Salma sun cigaba da juya abinda ya rage musu. Suna taimakon juna sosai,hakan yasa kansu yake a had'e, duk da rufin asiri ne kawai na Allah. Sannan d'ai-d'ai iyawa sun bama yaran su karatu da tarbiya,suna da t'sanani musamman Baban su Salma. Sai dai fa ita Maman su gani take kakarsu ta yanke saka,tunda Allah ya hore mata yara mata uku setin samira ta zuba jari,shi yasa d'ukkan wani abu akan A'i yake karewa dan ita tasa a lokacin. Ba lefi,ak'wai dan k'yau irin na ainashin mutan kanuri,sai kuma Maman dake asalin Shuwa,ba farare bane,za dai mu iya kiransu da _"black beauties"_sirrin su kuwa,diri ne da yalwar gashin ka da _"beauty point"_ _(dimples)_.. Wanda tamkar kowa diga mata ake. Hakan yasa kasuwar Aunty A'i ta daga da sauri,tuni k'wa Mama abin nema sai ya samu,hakan yasa ta kara sa ma sauran Burin da yafi na Aunty A'in.. Barin Salma dake doguwa ce cikin su. Ita kam Salma bata san ma ana yi ba. Kasantuwar shagonsu Baba ya zama biyu sai ya zamana aiki yai musu yawa, har bai samun damar dawo wa gida cin abinci sai d'ai Ummi koh Salma su kai mishi. Ranar kaiwar Salma ne,tai shirin Islamiya ta doshi shagon su Baba. Tunda ta ajiye abinci taki gaba taki baya,kamar dai da alamun an mata abu daga gida. Murmushi Baban yai kan yace tazo.. _"mey aka miki uwata?_ Hawaye ta dan matso halamar 6aci. _"Mama ce ta hana ni kud'in tara_. Kai Abban ya k'ada yana murmushi kan ya sa hannu a aljihu ba chanji,gudar naira dari ya fitar kan ya nuna mata shagon kusa dasu taje tai chanji. Da sallamarta ta shiga,ta gaida shi,shago ne na kayan k'yallin mata na sawa, attamfofi da laces,ga materials kala kala,d'uk zuwanta bata ta6a shiga shagon ba sai yau. _"Salamatu y'an mata,ina su Ummi?_ Murmushi tai mishi,dan tana ganin shi gun su Baba, dattijon na da kirki da fara'a, banda yaron shagon shi da koh k'allo bai mata ba, _"suna gida,Baba ne yace aban chanji_. Kai ya k'ada, kan ya k'allo na zaune a acikin shagon rike da littafi halamar yana dubawa. _"amm *Ja'afar*_.. Kai ya dago karon farko, _"Na'am Abba_,, sai lokacin ya kula da Salma, _"Ba wa Salma naira ashirin ta tafi kar tai latti_. Kai ya k'ada kan ya kara k'allo Salman wacce sai hange take koh za taga wani dan islamiyar su tana mika hannu. _"k'ar6i man_.. Juyo wa tai taga yana miko mata kud'i fuska ba fara'a, da sauri ta k'ar6a tana tafiya tana fad'in _"na gode Abba_. Da k'allo Ja'afar ya bita,yana ganin Ummi ce mai rawar kai ashe sauran ma haka suke. _customers_ ne suka tada shi ya shiga shagon. Washegari ma sai ga Salma,wannan karan koh shagon su Baba bata je ba tai shagon su Ja'afar. Da mutane da kusan d'uk y'an mata ne suna siyayya, yana ganin Salma ya had'e rai, sam yaki jinin a 6ata yaro da kud'i, ita kam Salma harda mishi murmushi tana dago mishi hannu da kamar abu aciki. T'saki yai,kan ya cigaba da abinda ya ke,sai da ya sallami kowa kan ya ganta tana gaida Abban shi da ya fita yana nuna mata cikin shagon. Da dan gudinta ta shigo,a tunanin shi kud'i Abban yace ta kara k'ar6a gun shi,dan da zumudinta ta gaida shi. _"dama Abba ne yace in_..... Cikin fad'a-fad'a ya katseta, _"bani da chanji nima yau,jiya an baki kinji dad'i shin_.... Shiru yai sakamakon idonta da yaga ya cika da k'walla tana k'allonshi. D'uk kuma sai jikinshi yai sanyi.. A hankali ta ajiye masa gudar naira ashirin akan benci ta juya tana goge hawaye. Ba dai kud'in shi ta biya shi ba dan ya mata fad'a? Da sauri ya d'auka da niyar k'wada mata kira ya mayar mata sai dai tuni tai nisa sosai. D'uk kuma sai yaji bai k'yauta ba. Yana nan zaune har Abba ya dawo, _"kaga Salamatu wai kud'in ka na jiya ya hau shine ta dawo ma dashi ba"_.. K'allon Abban yai da sauri, _"Abba kud'i kuma?_ K'allonshi yai kan ya k'ada mishi kai, _"sai da nace ta tafi wai A'a tana da wani,Salma ak'wai hankali, ashe batai ma magana ba?_ Shi dai Ja'afar yai shiru yana jin Abba,sai ya kara jin wani iri. *By* *Feenat Ja'afar*. 9/29/16, 8:50 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *5*- Washegari sai zuba ido yake yaga Salma shiru,dan d'uk jiya ji yake bai k'yauta mata ba. Sai d'ai Salma har k'wana biyu shiru ba koh kalar ta sai Ummi ke zuwa kawo abinci. Ranar Ummi ta kawo zata tafi ya t'sayar ta da tambayar ina Salma k'wana biyu? "tana gida Yace "ya bata kawo abinci sai ke?.. Tana zungura baki tace "sai gobe ne nata kawowar. Dan koh ita Ummi Ja'afar ke hanata zuwa gun Abba mai k'yautar naira biyar goma.. Sam baida fuska,shi yasa taki jinin shi. Washegari kuwa tun da ya ga lokacin kawo abinci yayi yake k'allon shagon su Baba,yau ga k'ananan shi a shagon baida mat'sala. Kamar ance ya dago,sai gata kuwa sanye da kayan islamiya,sai dai duk tai kicin kicin fuska ba walwala. Yana k'allon yadda ta t'suguna ta gaida su Abba kamar kullum, tana da nut'suwa ba kamar Ummi uwar bankaura ba. Tashi yai kamar mai tafiya wani gun,dai dai k'wanar da take bi gida ya t'saya,sai gata kuwa,har zata wuce ya kira ta,suna had'a ido ta had'e rai,sai ta bashi ma dariya. Hannu yasa ya ciro naira ashirin d'in ya mika mata yana murmushi, a dan sace ta k'allo shi kan ta kawar da kai tare da girgiza mishi kai. *"Salma*..K'all onshi ta kara,ganin yana murmushi sai abin ya bata mamaki,bata t'sinke da lamarin ba sai ji tai yace tai hakuri, kai ta kawar kawai, kin huce? tana wasa da hijab d'inta ta daga mishi kai, "toh ki k'ar6a in kin huce,na bar miki.. Kai ta kara girgiza mishi,kan tace "A'a ka barshi fa.. "baki hakura ba kenan Salma?.. Kai ta k'ada mishi, yace "toh ki k'alle ni ki amsa maza kar kiyi latti kinji K'anwata.. Da lallami yasa ta sakko harda dariya,har kusan makaranta ya rakata ya dawo,yana mai mamakin fara'ar shi yau ga yarinya Salma,sam shi baida sakin fuska musamman ga mace d'uk k'ank'antar ta k'wa. Tun daga ranar ya zamo in Salma ta kawo abinci sai Ja'afar ya rakata ya kuma bata ashirin d'uk bayan k'wana biyunta. Sosai sun saba,har in batazo ba baya jin dad'i, har su Abba suka kula da sabon kawancan Ja'afar da Salma,ana haka Baba yasa ya dinga ma wa su Salma _lesson_ tare da kannenshi tunda ya gama _secondary_ _admission_ yake jira. Koh a gun _lesson_ misalin Ja'afar a Salma yake t'sayawa, in k'wa duka ne koh t'sawa Salma bata ciki,sai dai yai ma k'annenshi, hakan yasa tun tana karama yaran suke ce mata Salma budurwar Ya Ja'afar. A lokacin takanyi bori kan bata so,har takai da ta kai kara gunshi,sai dai mamakinta dariya ma yai mata,yau da gobe har Salma ta saba da tsokanar k'annen Ja'afar . Karatu ake sosai za ai _coming interest_, sai dai ba Ja'afar dan ya tafi Zaria sakamakon _admission nashi da ya fito. Sosai Salma tai k'ewar shi,har hakan yasa ta d'aina kai abinci shago sai almajiri,a hankali har k'ewar ta sake ta suka gama jarabawa sai zaman jiran sakamako... Sai dai Ya Jaafar na chan k'wance kasan zuciyar ta. Yau ga Salma a _boarding_ babban burunta kenan makarntar k'wana. ************************** Lokaci ya shud'e, kamar wasa yau ga nan Salma an zana _J.S.C.E_, hutun mai dan nisa ne na yau. Mai nut'suwa ce a d'uk y'an gidan su,a layin su,dama unguwar gaba d'aya, Salma abar k'watance ce,musamman rashin yawanta,kullum kaje in tana hutu toh za ka samu Salma a gida. Batta k'warafniya irin ta y'an mata masu tashen tashi,asalima fitar ta in tai yawa toh islamiya ce ta yamma, sa6anin su Ummi da tuni tun kar ta far ta kone, dan wanka iya wanka Ummi ta iya,hakan yasa Mama ta kara d'aure mata gun siyan kayan k'arya. Dan a ganinta ta gama da kason Aunty A'i tunda har an kawo sadaki, kuma irin wanda mama ke da muradi. Ita kam Salma zai wuya ka ga tama sanya g'yale bare har ta zauna k'yali. Gata dai mama ita tafi sawa buri, ga ta kuma y'ar _boarding_. *By* *Feenat Ja'afar*. 9/29/16, 8:52 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 6-A dai-dai k'wanar su Ja'afar take,dawo warta daga islamiya kenan,sanye take da dogon hijab ruwan kasa mai yashi har kusan kasa,rataye da jakar littafai da Qur'ani a hannu,sai dan asirin _skirt_ nata na attamfa da ya fito _green_ da ruwan kasa, duguwa ce,ba zangal ba,tana da kaurin jiki,dan ta fita sahun ramammu,tafiyarta a nut'sue tafi komai d'aukar hankali. Kamar kullum ta daga kai dan k'allon gidan su Ya Ja'afar kamar yadda ta saba k'ewar shi ta kawar da kai, sai dai taku biyu taja ta t'saya tamkar an t'sayar ta. Kanta duk'e dauke da murmushi,cikin nut'suwa ta kara k'allon kofar gidan dan tabbatar da wanda ta gani.. *"Ya Ja'afar*?...ta fad'a a zuciyarta lokacin da ya taso yana mata murmushi. Ikon Allah,wai kunyarshi kuma take ji,cikin nut'suwa ta d'auke kanta daga gareshi ganin ya karaso. "Assalam Alaikum Malama Salma.... Wani irin buguwar zuciya taji ya ziyarce ta,shekara uku da wani abin ba wasa ba,hatta muryar Ya Ja'afar ta sauya mata. Cikin nut'suwa ta dago da murmushi ta amsa mishi,kamin ta gaida shi a kunya ce, shi dai kawai k'allonta yake yana murmushi, kamar mai mamakin kara girmanta,ga wata nut'suwa da ta kara shigarta. D'uk sai ya kara yaba Salman nashi,ganin shirun yai yawa yasa da hannu ya nuna mata hanya halamar su wuce. Dan satar K'allonshi tai kan ta sunne kai suka fara tafiya. "Salma koh murnar gani baki yi,ba koh tambayar yaushe nazo? Kai duk'e tace "yi hakuri,yaushe kazo?.. Kai ya k'ada da murmushi,kan yace "jiya. Tambayar yaushe gamo yake mata, yadda take kunyar tata gun bashi amsa d'uk sai ya ji shi wani iri,mace mai kunya itace muradinsa. Da haka har kofar gida ya rakata yana mata tad'in makaranta da yadda suka juma basu gamo ba. Ummi ya k'allo achan dan nesa dasu tana tad'i, sai ya tuna mata yasha zuwa ai. Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar d'inta. Ganin haka yasa yai mata sallama tai gida.. A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar d'inta yau. Sai murmushi take saka cike da kunya ita kad'ai kamar yana ganinta. A haka har Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata gami da had'a rai. "Yanzu Ummi kinyi dai dai kenan? A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale, "da nai miki mey? Iya jaraba.. Kai Salma ta k'ada kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma koda wasa baki fad'an ba? Allah kin ban haushi.. "Mtsww.. T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma K'anwar ta. "Na zata wani abin kirkin ne wallahi, toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken shi?.. Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh.. A tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan koh? Yara kamar masu ganin hanjin junansu? Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da kunya sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan uban d'acin ran kike wannan kumfar bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki.. Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar* Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 20 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 6-A dai-dai k'wanar su Ja'afar take,dawo warta daga islamiya kenan,sanye take da dogon hijab ruwan kasa mai yashi har kusan kasa,rataye da jakar littafai da Qur'ani a hannu,sai dan asirin _skirt_ nata na attamfa da ya fito _green_ da ruwan kasa, duguwa ce,ba zangal ba,tana da kaurin jiki,dan ta fita sahun ramammu,tafiyarta a nut'sue tafi komai d'aukar hankali. Kamar kullum ta daga kai dan k'allon gidan su Ya Ja'afar kamar yadda ta saba k'ewar shi ta kawar da kai, sai dai taku biyu taja ta t'saya tamkar an t'sayar ta. Kanta duk'e dauke da murmushi,cikin nut'suwa ta kara k'allon kofar gidan dan tabbatar da wanda ta gani.. *"Ya Ja'afar*?...ta fad'a a zuciyarta lokacin da ya taso yana mata murmushi. Ikon Allah,wai kunyarshi kuma take ji,cikin nut'suwa ta d'auke kanta daga gareshi ganin ya karaso. "Assalam Alaikum Malama Salma.... Wani irin buguwar zuciya taji ya ziyarce ta,shekara uku da wani abin ba wasa ba,hatta muryar Ya Ja'afar ta sauya mata. Cikin nut'suwa ta dago da murmushi ta amsa mishi,kamin ta gaida shi a kunya ce, shi dai kawai k'allonta yake yana murmushi, kamar mai mamakin kara girmanta,ga wata nut'suwa da ta kara shigarta. D'uk sai ya kara yaba Salman nashi,ganin shirun yai yawa yasa da hannu ya nuna mata hanya halamar su wuce. Dan satar K'allonshi tai kan ta sunne kai suka fara tafiya. "Salma koh murnar gani baki yi,ba koh tambayar yaushe nazo? Kai duk'e tace "yi hakuri,yaushe kazo?.. Kai ya k'ada da murmushi,kan yace "jiya. Tambayar yaushe gamo yake mata, yadda take kunyar tata gun bashi amsa d'uk sai ya ji shi wani iri,mace mai kunya itace muradinsa. Da haka har kofar gida ya rakata yana mata tad'in makaranta da yadda suka juma basu gamo ba. Ummi ya k'allo achan dan nesa dasu tana tad'i, sai ya tuna mata yasha zuwa ai. Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar d'inta. Ganin haka yasa yai mata sallama tai gida.. A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar d'inta yau. Sai murmushi take saka cike da kunya ita kad'ai kamar yana ganinta. A haka har Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata gami da had'a rai. "Yanzu Ummi kinyi dai dai kenan? A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale, "da nai miki mey? Iya jaraba.. Kai Salma ta k'ada kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma koda wasa baki fad'an ba? Allah kin ban haushi.. "Mtsww.. T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma K'anwar ta. "Na zata wani abin kirkin ne wallahi, toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken shi?.. Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh.. A tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan koh? Yara kamar masu ganin hanjin junansu? Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da kunya sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan uban d'acin ran kike wannan kumfar bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki.. Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar* Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 20 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 7_Washegari ma ta fito zata makaranta sai gashi shi da abokinshi Garba suna tafiya. Ido ya kura mata ganin tai kasa da kai tana murmushi. Sai ya k'ada kai suka karasa,cikin sanyin murya ta gaida su,Garba kad'ai ya amsa,shikam Ja'afar k'allonta kawai yake yana murmushi, kamar mai son sai sun had'a ido. "Malama Salma fa kar tai latti a mata bulala abokina.. Kasa ta kara da kai tana dan dariya, shikam gogan sai binta yake kawai da k'allo,kan ya nuna mata hanya kan wai su rakata hanya. Ba musu ta wuce suka jera,Garba sai shakiyanci yake zuba musu,murmushi kad'ai ne nasu har suka zo bakin _gate_ d'in islamiyar. Ka'ro na farko suka k'alli juna cikin ido,da sauri ta K'awar da kanta tana murmushi, shikam harda k'ada kai, tuni Garba ya harbo jirgin nasu,sai ya hau shafa ha6a yana k'allonsu,musamman abokinshi da yace bai san so ba.. Hannu Ja'afar ya kai aljihu yana lalube,ita kam sai ta hau satar k'allon shi ganin mey zai yi. Da mamakinta k'wa sai gashi ya fito da naira ashirin yana mika mata. K'alloshi tai tana kunshe dariya,sai ta k'ada mishi kai, "Kud'in tara ne fa Salma, ki k'ar6a ki sai hambididi... Dariya Garba ya fara harda rike ciki,itama wacce take rikewa ta fito fili, sai ta sa hannu a baki dan rufe sautin ta.. Shikam Ja'afar kawai sai ya hard'e hannu yana K'allonsu, musamman Garba yadda yake k'yak'yata dariya. Shikam ba kasafai ya iya dariyar keta ba irin ta Garba,shi yasa wataran yakan kularshi a abu. "La Malam Ja'afar...... Gaba d'ayan su suka juya k'allon mey magana. Ja'afar take k'allo tana murmushi halamar jin dad'in ganin shi, shikam tuni ya had'e rai yana k'allon ina ma ya santa. Kamar tasan mey yake tunani tace *"Bintu*(Na Rufaida Omar) ce,dalibar ka a day... Salma ya k'alla wacce itama ke kallon Bintu,kan ya k'ada kai, "toh Bintu.. Salma Bintun ta k'alla jiki a sanyaye ganin ko in kulan da Ja'afar ya mata,"shiga za kiyi ne Salma? kai ta kada mata, jiki a sanyaye tai gaba Salma ta daga musu hannu halamar sai anjima tana murmushi. Da k'allo ya bita cikin wani yanayi, da ko shi kanshi bazai iya fassara wa ba. Kai ya k'ada kan ya k'allo Garba wanda k'wachokam ya maida K'allonshi kan abokin yana dariya kasa-kasa. Harara ya maka mishi kan ya juya,sai k'wa Garban ya kara sa dariya yabi bayanshi. "An fad'a tarko makal ana hura mana hanci,sai anyi magana kace wani "mey nene so? Ni ban sanshi ba.. Karyan kawai,koh makaho ya laluba yaji ka afka so ai yanzu kam. Chak! Ja'afar ya t'saya tare da juyo wa gun Garba. "Mey kenan haka ke nufi?.. Harara Garban ya k'wada mishi kan yace"kar ka maida ni yaro fa malam,kana nufin baka san kana son Salma ba ko mey?.. K'allonshi kawai Ja'afar ke yi cike da mamaki,a hankali ya furta *"SO"*?... Hararar shi Ja'afar ya kara,gani yake kamar ya raina mishi hankali ne. "Kaga Malam kawai kai saranda haka,tuni tun yadda ka ke ta yawan fad'in Salma nasan a rina,ka bar wani k'wane-k'wane. Shi dai Ja'afar ya t'sunduma tunani maganar Garba,wai So? Salma kuma?. *By* *Feenat Ja'afar* 庐NWA. 9/29/16, 8:56 AM - Queen Safiyyert馃憫: [7/21, 12:28 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 8-Har Ja'afar yazo k'wanciya yana tunanin kalaman Garba,tabbas biri yaso kama da mutum, dan yana jin sauyi tun ranar farko da ya dora idonshi a Salma bayan dawowar shi. "So"... Ya furta a hankali, murmushi yai kan ya k'ada kai,dan yana da aiki a gaba,dan bai san kom ba game da lamarin. Tun daga ranar ya zamto kusan kullum da yamma yakan raka Salma islamiya,koh da yana shago zai zo ya ganta kawai,hakan na sashi nishad'i, yau da gobe har ta fara sakin jiki dashi a karo na biyu. Sai ya zamana itama in bata ga Ya Ja'afar a ranar ba batajin dad'i sam,haka zata k'wana sukuku. Shirye-shiryen bikin Aunty A'i suke,duk sun shiga _busy_. Da yamma sun fito bak'in shagunan su Abba siyayyan kayan fitar biki, tasan kuma d'uk layin ba inda ya kai shagon su Ya Ja'afar kawo kayan k'yali, amma da tayi magana Ummi sai ta tanka. Kai duk'e yana duba takaddu,kamar _papers_,chak ya t'saya da abinda ya yake yana murmushi kai duk'e, ajikinshi ya ji kamar Salma na kusan shi,itama dai satar k'allon shi take,tana ganin zai dago tai sauri ta juyar da kai tana murmushi. Fara'ar shi ta karu dan hango Salman. A hankali ta dan kara K'alloshi,sai k'wa suka had'a ido,da azama tai kasa da kai tana murmushi har suka karaso. Tuni Ummi ta had'e rai ganin Ja'afar a shagon,a takaice ta dan harari Salman ganin sai wani munafukin murmushi suke sakar ma juna,baki ta ta6e kan a ciki ta gaidashi tai cikin shago ta barsu nan. _"My_ kanwa,.. Kai ta kara duk'ar wa tana gaidashi,sai ya k'ada kai,ya rasa irin kunyar Salma gare shi yanzu,abu kad'an duk'ar da kai. "Biki ya karato ba? Kai ta daga mishi tana dan k'allon _net_ d'in gefenshi da murmushi. Tashi yai zuwa gun inda take k'alla ya fara saukar mata dasu. A hankali ta tako gun dan zabi,d'uk sun mata k'yau. Sai ta dan kallo shi, "malam Garba fa? Murmushi yai yana k'allonta, "yaje inda aka tura shi _service_ nashi yaga gun,gobe zaki ganshi. Kai ta k'ada, d'uk sai taji ta kasa za6a ganinshi kusa da ita. Kamar ya sani ya kara s'akko mata da wasu. "Bari na tayaki za6a. Kai kawai ta k'ada mishi tana k'allon kayan,kan wani _purple_ idonta ya kai,a hankali ta kai hannu zata ja shima ya kai zai d'akko shi yana fad'in _"purple_ zai miki k'y... Shiru yai ganin itama shi ta rike,ya rike rabi ta rike rabi. D'uk sai suka k'alli juna ba koh kiftawa da wani yanayi... Tamkar wanda aka lika _poster_ a gun haka suka kame da k'allon juna. Ummi ce ta kat'se su da fad'in "Ga nan wasu materials y'an leda Salma masu kaman _lace_.... Shiru tai ganin wani ikon Allah,baki sake take k'allon su,tuni Salman ta sakar mishi tai baya tana sunke kai da murmushi tare da amsar kayan hannun Ummin tana sunyi k'yau ba dan ta gani ba. Murmushi ya sakar mata shima,har yanzu yana rike da _net_,ya rasa mey ke damun K'wak'walwar shi akan Salma. *By* *Feenat Ja'afar* [7/21, 8:05 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 9_Baki ta dan ta6e,kan a y'atsine tace ma Jafaar d'in "mun zabi wannan, zamu nuna ma Baba sai ya bada kud'in. Murmushi yai yana k'allon gun Salma,itama idonta na kusan hannunshi. "Koh na tafi ne Salma? K'allo Ummin tai,kan ta k'ada kan suka yi hanyar fita a shagon,a hankali ta dago mishi hannu halamar _bye_. Kai ya k'ada mata shima ya dago mata nashi. Tai k'walli da Ja'afar ta ji dad'i,har aka je gida bata umm ba um um,sai Ummi ke ta zuba kamar kanya, yadda zata zuba wanka a bikin Aunty A'i har ta kule. Da dare sai ga yaro wai ana kiran Salma. Rai had'e ta k'allo yaron, "je kace bana nan... Shiru tai ganin yadda mama ke mako mata harara, "anya yarinyar nan kalau kike kuwa? Wato sai dai ai ta min asarar hoda da kazal a banza ina tufka kina min warwara koh? "Farin jini Allah ya bayar kina ma kanki bak'in ciki? Haka zan ta barar miki ni baki ban bare na maida g'urbin abinda na fitar Salma?.. Maman ta k'allo da mamaki,toh rokon samari mama take so ta fara komai? Allah yaga ta t'sani fita zance. Amma ganin yadda mama ke wanke ta yasa ba shiri tace ma yaron "yace ma waye?.. Kai ya daga mata,"wai ince inji "Ja'afar in kin tambaya... Ai koh karasa wa nai ba ta mike,tuni murmushi ya maye g'urbin 6acin rai, da k'allo mama ta bita, kamar ba ita ce yanzu ba. Yau kam ga su Salma harda mit'sika hoda da _lips stick_ har ta d'au hijab ta kara k'allon madubi,kawai sai ta janyi g'yalen Ummi tai waje. Shine kuwa yana jingine da gidan,wani murmushi ta saka na farin cikin kara ganinshi a daren. Da sallama ta karasa d'uk da ba wani haske gun sosai,amma sai dan sinke kai take kamar rana. Bayan sun gaisa kowa yai shiru kamar basu abin fad'a. Chan dai ya nisa ya miko mata ledar hannunshi. Kamar mai neman ba'asi ta t'saya bata k'ar6a ba. "Ajiya na kawo kimin zuwa gobe ne,ba wani abun ba naga kina tsoro. Murmushi tai kan ta amsa tana k'allon Ummi zata wuce,koh ci kanku bata ce ba ta shige gida. D'uk sai Salman taji wani iri,Ummi sam taki jinin Ja'afar ta rasa dalili. Ba jimawa yai mata sallama dan ya rasa abin fad'i shima. Dama da Garba ne yau kam da zai iya fad'in komai ga Salma. *** Tunda daga lokacin Ja'afar ke zuwa gun Salma jefi-jefi,d'uk da har yanzun bai furta mata so ba,amma ita a ganinta d'uk acikin so ne. A k'wan a tashi gashi har ta kammala secondary, wannan itace tafiya mafi tsawo da Salma tai bata ga Ja'afar ba,kusan wata bakwai. Tun tana damuwa har ta hakura ta rungumi karatun ta na fita. Gasu yau sune a gida,d'uk an rame anyi baki. By Feenat Ja'afar. [7/21, 10:10 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 10_Babban tunaninta bai wuce d'uk t'sawan lokacin nan da aka diba ba Ja'afar ba labarin shi ba,tasan yakan je mata ziyara makaranta koh a t'satt'saye ne,ga ita ba waya ba balle ta neme shi koh lafiya? K'wana biyu da dawo wa yau d'ai ta kudiri niyar fita jin ba'asi,koh Garba in ta gani. Hijab d'in _mss_ d'inta har kasa ta sa harda nikaf. Sai d'ai har ta gama zagayen layin ba wanda ta gani ciki,kawai burinta ganin Ja'afar ne. Iyanzu kam tasan tai nisa kan sonshi ba kad'an ba,sai d'ai ita yanzu ta fara tantama. Har zata juya ta tuna da shago,d'uk da tasan yanzu ba kasafai yake zama ba tunda ya samu g'urbin koyarwa. Sai dai tai chan d'uk bata tunanin ganin nashi. Daga d'an nesa ta t'saya kusa da wata bishiya ta d'an kare ba mai ganinta, da sauri ta juya tare da dafe kirji,zuciyar ta sai bugawa take da k'arfi. Yanzu ta samo amsarta da kuma kokwantan ta da ya zama gaskiya... Bata aune ba sai jin hawaye tai na bin kuncinta cikin nikaf d'in. A hankali ta fito daga bayan bishiyar tare da kara k'allo shagon. Murmushi yake harda darawa, ita kuma budurwar sai washe mai baki take tana ta mai zuba,rike yake da hannun wata y'ar k'yak'yawar yarinya fara kamar yayarta. Ji tai wani abu ya tokare mata kirji,da sauri tasa hannu ta dafe gun,ga hawaye yaki ya d'aina malala. Lalle tai wautar kin kula kowa sai Ya Ja'afar da bai furta mata so ba. Ido ta rint'se ganin ya d'akko mata wani had'adan net purple yana bata,wato har kalar da yasha sanar mata yana so ya bata? Tai imani mai irin wannan zankadediyar budurwar fara ba abinda zai da ita Salma baka. Hannu tasa ta cikin nikaf d'in tana goge hawayen dake zuba mata. K'allo sun da zatai taga Ja'afar ya zuba ma inda take ido,har budurwar na k'allo itama,da sauri ta juya gabanta na fad'uwa, kar dai ace ya gane ta? Tab,da k'wa ta bada kanta wallahi. Juyo wa ta kara,sai karaf suka kara had'a ido da Ja'afar. Ba shiri ta tare mai adaidaita ta shige,tana k'allo ya bi napep d'in da k'allo yana girgiza ma budurwar kai. Kawai sai ta sa kuka mara sauti tare da cire nikaf d'in. Lalle tai wautar zurmuwa ga soyayyar Ja'afar, soyayyar da ba'a ma bayyana mata ita ba... Ya Ilahii. ************************** "Oh! Man Ja'afar, dama kana k'allon mata har haka? Bafa koh kiftawa? Murmushi yai mata tare da girgiza kai, "Hala tai kama da Salma ne? Danma da hijab ga kuma nikaf.. "Kusan hakan ne, jikina ya bani kamar Salman ce kam..amma nasan ba ita ba ce ma. Dariya ta danyi har hakorinta farare suka baiyana,kan tace "sannu _Romeo_ toh, ni sallameni kan Amal ta fara neman mamanta, amma ina mamakin yadda ka iya zaben kaya da color, halama kana son _purple_? Murmushi kawai yai mata,kan ya k'ada mata kai halamar eh. Ita kam Salma tana zuwa gida ta taho da yaro a kofa ya kaima mai Napep kud'in shi. Allah yaso ba kowa t'sakar gidan mama na d'aki. A katifa kawai ta zube ta sau kuka,sai da tai mai isarta tai shiru tana maida numfashi. Chan kuma kamar wacce aka t'sikara ta mike zaune. Tabbas Ja'afar bai ta6a nuna yana sonta ba kam,d'uk zuciya ke yaudarar ta. Asalima da "K'anwata" yake kiranta, kila hakan ne tun da,ita kad'ai ke kidanta, gaba d'aya ta gama kore masu sonta ita a dole ta riki Ja'afar. Hawaye ne ya kara zubo mata tunawa da yadda yake washe ma budurwar nan baki. Tasan yadda Ja'afar yake a gaban mata baya wargi,baya sake fuska ma bare har yai musu irin wannan tad'in. "Tabbas budurwar sa ce,nai wauta ni Salma... "Lafiyar ki kuwa kike maganganu ke kad'ai ya sabuwar kamu? Kai ta dago jin batun Ummi tana wannan y'atsine matan. Sai dai ganin irin yadda idon salman yadda yai ja,ga kuma hawaye yasa ta mat'so "Mey ya faru kike kuka haka?.. Ai kamar mai jira a ta6ota ta kara sa wani kukan mai sauti. Tuni kuma sai Ummin ta zauna tana lallashi da fad'in lafiya? Ita de sai kukanta take baji ba gani. Tashi Ummin tayi,"bari na fad'o ki da mama toh,kila k'ya fad'a mata ita... Da sauri ta rike mata riga, "ni ba komai.. Marata ke ciwo da bayana kawai. T'saki Ummin tayi, "Allah kina da aiki a gaban ki Salma,kukan jinya sai kace wata yarinya. Ita dai tana jinta ta karaci kardinta tai waje,a hankali ta zame ta k'wanta,sai sauke ajiyar zuciya take. *By* *Feenat Ja'afar* 庐*NWA* [7/22, 12:02 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 11_Kan safiya har ta gama tunanin abin da zai fisshe ta. Hakan yasa t'saf ta tashi kamar ba ita taci kukan nan ba. Aunty A'i yau za'a kaima wuni,tun (12) suka fice ita da Ummi. Chan suka yini har dare,a kafa ta ratso ita kad'ai sakamakon Ummi da ta biya kar6an _style_. Tunda tazo layin su Ja'afar d'in taji gabanta na fad'uwa, duk da bata koh k'alli hanyar gidan ba. "Abokina ina ka tafi ne daga lissafi kai shiru? "Ba kaga kamar Salma ba waccan mey tafiyar? Ido Garba ya k'wara, da mutum,amma a duhun nan bazai tantance ba,kawai sai ya k'ada mishi kai, "A cikin duhun daren nan ne har zaka gane wake tafi.... Shiru yai ganin Ja'afar d'in yai gaba,da sauri yace "wai mey ke damunka ne? Ina za ka?.. Binshi yake shi kuma yana bin mai tafiya a duhun. "Salma"... Chak! Ta t'saya dan jin kamar an kira ta,a hankali ta juya,da dan tazara a tsakanin su kad'an, amma hakan bazai sa ta kasa gane ya Ja'afar ba koh a cikin dubu,hakan yasa cikin sauri ta juya ta chigaba da tafiya,har dan gudu- gudu sauri-sauri take. "Mey zai fad'a min kuma? Ta fad'a cikin ranta. Har kusan layinsu ya bita, tsammanin shi koh tsorata tayi,amma tabbas wannan Salma ce,kawai sai ya t'saya a dai-dai layin nasu yadda bazata ganshi ba,da hasken inji a layin, yana gani ta t'saya ta waiga,kan da sauri ta shige gida. "Amma fa baka aiki sam Jaa, wai har nan ka biyota kage ma koh aljana ce a daren nan? Juyawa yai yana girgiza mishi kai,"Allah Salma ce,toh yaushe ta dawo?.. Baki sake Garba yace "hadda rantsuwa? In Aljana ce fa mai siffar ta?. Harara ya sakar mishi kan ya juya suka tafi. Ita kam tana zuwa gida Abba da Mama suna t'sakar gida ta shigo sai haki,tuni k'wa Abba fad'a ya karu, kan mey yasa sukai dare? Tuni tai zuru zuru,fad'a sosai tasha,saura Ummi,d'uk da laifin Ummin har sukai daren. Washegari kusan yamma sai ga nan yaro kan ana kiran Ummi da Salma inji su isma'il. Harara Salman ta k'wada ma Ummi, kan tace "yanzu sai da kika fad'i ma mutanan gidan mu kika huta koh? Allah ban san yayi6e ni. Hararar itama Ummin tai mata,"arziki na binki kina guduwa,kowa yazo kice bai miki ba,ki mayi karatun ta nut'su wallahi,dan aure zanyi ni ba jira.. "Keai Kowanne dan chaburos ma yazo Ummi a shirye kike, toh ba dani ba. Yankan farcen Ummin ta bari tai hanyar d'aki tana fad'in"sai kiyi ta zama kar kiyi aure,har mahadi ya baiyana. Cikin kuluwa zatai magana sai ga Mama ta fito a d'aki, ashe d'uk tana jin su, "toh k'wa maza ki wuce ki je tun kan na sa6a miki,daga yau na d'aina zuba miki ido ba fus bare ass Salma... Yarinya sai taurin kai,ace koh kishin yadda y'ar uwarki take shiga take fita da y'an k'wabai ba kiyi? Toh na gaji da gafara sa dan ban hangi kaho ba... Maza ki shiga daga ciki ki g'yara ki wuce... Kai kasa Salma tace "toh.. Ita kam tana mamakin halin Mama har kullum akan su,sai dai tana tuna Ja'afar tuni taji tana da muradin fita,tunda wanda take danshi bai ma san tana yi ba. G'walo Ummi tai mata,kan tai waje tana sai ta fito. Bata aune ba taji mama a d'akin nasu, bani waje ki ga,da kaina sai na g'yara ki... Baki sake take k'allon Maman,aikwa ta zage ta hau cha6a ma Salma k'walliya irin wacce bata ma san mama ta iya ba. Fad'i take "na rasa gane wace iri ce ke Salma,arziki na binmu kina zura da gudu,d'uk wani buri da na sa kanki kin rushe shi, in banda haka a jiya kad'ai kina ga irin bajintar da Ummi ta shigo dashi daga gun isma'il yake ko wa? "Haba k'alle ki a madubi man,san kowa kin wanda ya rasa... Tana yi tana g'yara mata d'aurin dank'wali. "Maza ki fita kan Abban ku ya dawo ya hana ruwa gudu.. Kai ta daga zata d'au hijabi,da sauri Mama ta warce, "g'yale zaki sa matar Malam,koh a Shari'ar a haka ake son a ganki,ta ina za'a yaba in kin maka hijabin? Toh ba walima nace kije ba.. Kai ta k'ada, ta zama tamkar rakumi da akala,sai yadda mama tace. "A'a, ko ke fa,k'alli kanki a madubi ki ga man,ai da banbanci, maza je ki... Kai ta kara k'ada mata, har zatai waje da sauri Mama ta kara kiranta. Turare ta fesa mata,kamar tace ba k'yau mama,sai dai taja tai shiru. "Ki murmusa man Salma,haba..murmushi ma ado ne ga fuskar Y'a mace... A yadda maman take yi bata ma san sanda abin ya bata dariya ba. Allah ya gama su da uwa "LASHE MONEY", har ta fita kuwa tana murmushi, mama sai barta. Suna t'saye gaban wata jar _CRV_ tare da Ummi,d'uk dinsu sun zubo mata ido. Ita kanta tasan tayi ne, fari da manyan ido kawai budurwar Ja'afar zata fad'a mata tasan. Doguwa ce ita dai dai misali,farin jinin samarin zamani,fatarta a goge take mai launin Wankan Tarwada(black beauty), tana gashi ga gashin ido,gata fuska doguwa,gata tana da diri dai dai so,d'uk komai ya ji ba bau ba. Ya dace kam tai amfani da lokacinta tun yanzun. Cikin takun da ba irin na Salma ta da ba ta karasa gun su Ummi,ga murmushin nan dan _beauty point_ din nan sai lot'sa wa yake. Tuni ta kara tafiya da imanin Muzammil,har yake ji kamar ya taro ta kan ta iso. By Feenat Ja'afar. [7/22, 4:57 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 12_Ita kanta Ummi tai mamakin Salma da sakewar ta. Sun gaisa da isma'il saurayin Ummin su kuma suka zaga dayan bangaren motar, Kusan kawai d'aurewa take tana mishi yake, amma ita sam taki jinin saurayi mai shegen surutun t'siya. Hakan yasa d'uk taji ta gagu su k'auce, ga tasan Abba gaf yake da zuwa da magriba tayi. Kamar ance daga kanki, Ja'afar tagani kusan su kad'an, tamkar gunki yaja ya t'saya, ga nan wannan budurwar da ta ta6a ganin su itama tana k'allo su,sai ta k'alli Ja'afar, kawai sai ta d'auke kai kamar bata gansu ba. Harda kara bawa Muzammil wani _attention_ na daban tana murmushi. Cikin sanyin jiki ya juya,tana dan satar k'allon shi,a baya budurwar tabi shi tana waiwayen Salman,ji tai kamar ta k'wada mai kira,So ba k'arya bane Salma. Da k'allo Ummi ta bisu lokacin da suka zago ita da isma'il, sallama sukayi,suna kokarin jan mota sai ga wata bakar mota ta _parker_. Ganin su Garba yasa da sauri Salma ta daga ma muzammil hannu tana mishi murmushi. Ja'afar dake k'allonta ta glass din ya rint'se ido da sauri. Ganin zata juya yasa Garba fad'in "Salma" da sauri. Juyo wa tai lokacin da yake yafito Jafar da hannu halamar ya fito. Koh ta kansu Ummi bata bi ba tai gida. Yake tai mishi lokacin da suke karasowa,sai dai koh inda Ja'afar yake bata k'alla ba shi da budurwar shi. Cikin barkwanci Garba yace "duniya da alkawari kuwa Malama Salma?.. Murmushi tai mishi iya le6e, "ashe kin dawo amma koh mu sani.. Karon farko ta k'allo gun Ja'afar, idonshi k'wa a kanta girrr...ba koh kiftawa. Da sauri ta d'auke kai daga kanshi. Gaidasu tayi,budurwar na mata an dawo. Lafiya? A ciki ciki ta amsa,Garba yace "yaushe a gari? An gama lafiya _hope_? Da mamaki take k'allon shi,yanzu dama da wanda zai ce bai san y'an makaranta sun dawo ba? Kawai dai sai ta maze, "yau kusan satin mu da dawo wa. K'allo Ja'afar d'in Garba yayi,kan ya dawo da K'allonshi ga Salman. Ba wannan dawowar ba,yau k'wana uku da zuwan mu K'anwarki tace mana kinyi tafiya... Da sauri ta dago kai da mamaki,tana k'allo gun Ja'afar d'in ya d'auke kai. Garba yaci gaba, "zuwan mutumin kenan daga Zaria yace sai ya zo ya ganki ya miki murna,ashe ke har kin ma fice a garin. Batta bakin magana,dan bata san amsar basu ba,amma Ummi tana mata daya a rayuwa..wai tai tafiya? "Ga nan mutumin jiya har sururu yake yaganki da dare ina mishi t'siya, ashe ke ce. Kai ta daga,kan ta kara k'allon Ja'afar, d'anna wayarshi yake kamar bai wajen. Cikin wasa Garba yace "toh ni zan gabatar mata da ita ko mey da kai mikis?..kasan ba kunya zan ba ni. Murmushi budurwar tayi kai duk'e, dan sam bata ga fuska gun Salman ba. K'allon Ja'afar din take,yayin da yake k'allon Garba yai shiru. "Toh,mu bama sanya, sai ya juyo gun Salman, "Salma ga nan budurwa,kuma matar... Da sauri ta rint'se ido,kan ta karasa da "Ja'afar"... Na sani Malam Garba... D'uk ido suka zuba mata har Ja'afar baki sake,jin shirun yasa ta bud'e ido akansu,yadda suke k'allonta tasan tai su6ul da baka... Cije le6e tai,amma ta bada kanta wallahi.... Dariyar keta Garba yasa harda k'yak'yatawa, sai ta dago tana k'allonshi. Sai da yai mai isarshi kan ya k'allo Billy, "Haba,Yanzu na ji batu,ni fa naga kowa yana sassahan kamshi,ashe-ashe...uhm uhm _Jealousy_... "Toh wannan Matar Garba ce bata Ja'afar ba,sassauto madam. Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta,har batasan sanda murmushi ya su6uce mata ba. A kunya ce ta k'allo Billy,sai ta mat'sa kusan da ita kan tace "sannu da zuwa... Dariya suka sa mata banda Ja'afar da ya dan dara,idonshi kir a kanta,bazai iya fassara mey hakan yake nufi ba, shin Salma na son sa da kishin sa ne koh mey? Ita dey sai dan satar K'allonshi take,amma bazata iya fassara ina ya dosa ba. Mota su Billy sukai suka barsu,ga nan magriba ta gabato,gaidashi ta kara yi itama ciki ciki,t'sayuwa ya g'yara kan ya amsa,tare da mata murnar kammala karatu,shiru ba mai cewa uffan,kowa miskilin kanshi,kawai sai sukai sallama kan gobe zai zo. Tana shiga gida dan takaici kasa ma Ummi magana ta cikin fad'a."yanzu Ummi kina k'yauta min kenan a rayuwa? Mey Ya Ja'afar ya t'sare miki ne ki ka ki jinin shi? Rai ta had'e, kan tace "oho,kawai bai min bane... Ga nan sakon daga Muzammil,kinga in da ake harka ai... Kai ta k'ada dan takaici tai d'aki batabi koh ta kayan ba. Washegari dan kalata sai ga su sun dawo, ana la'asar, mama ta fita unguwa. Ado Ummi ta ciwo da tafi na jiya,sakare tai ganin Salma koh mot'sawa batai ba. "Koh ba zaki bane Salma? A tunzure tace "ba zani ba.. Baki Ummin ta ta6e,kan ta daga kafada, "mat'salar ki ce wannan kuma... Sai tai waje. Aiko yaro sau biyu ana yi daga waje daga Muzammil amma fur taki fita. A ka'ro na uku ne yaron suka shigo da Mama da ta dawo daga unguwa. Dole ta tashi badan rai naso ba,sai dan ganin Ummi ta shigo ta had'a ta da Mama kan taki zuwa gun Muzammil. Tana had'a rai ta fito,sai dai da mamakinta taga Ya Ja'afar t'saye yana aiken yaro kan tazo. Da sauri ta koma cikin zauren kan ya ganta. Jim tai kad'an bayan fitar yaron kan ta fito,kanta t'saye tai gun Ya Ja'afar, kan tace ya bata minti biyu dan Allah. Kai kawai ya k'ada mata,sai tai gun su Ummi,a mutunce suka gaisa,kan tace da Muzammil sakon shi sai gobe.. Bata jira amsa ba tai gaba. Shi kam Ja'afar k'allonta kawai yake,amma tuni har yazo wuya. Tabbas dole ya bayyanawa Salma yau ranshi ba sai an k'wana ba,dan wannan samarin tsaf sai su iya kasa shi yana k'allo. "Bissmillah, muje zaure... Bai yi musu ba yabi bayanta. Har ya dan saki fuska, dan sam ba kaunar zaman ta a layi yake ba. Bayan sun gaisa yake bata labarin abinda yasa bai je mata ba. "Kinsan Mamana tana a Zaria ne,sun rabu da Abba tun ina dan shekara biyar,hakan ya zamana Abba ya k'ar6e ni a dalilin tai aure,nakan kai mata ziyara haka,sannan dan ita na zabi zuwa Zaria karatu. A _time_ d'in da za ai _visiting_ aka aiko bata lafiya,chan naje har t'sawan wata uku. "Taji sauki sosai,har tana ta fad'an na koma bak'in aiki na,ana haka y'arta K'anwata ta dawo sun gama makaranta,hakan yasa na tuna da Salma.. Nan nai shiri na dawo,duk dan na ganki,sai aka samu akasi, Ummi tace kinyi tafiya... Shiru yai kai duk'e, itama tai tsam tana sauraren shi. "Salma"...kai ta dago ta dan k'alleshi, shima idonshi a kanta. "Yanzu kam lokaci yayi da zan sanar ki wani sirri,sai d'ai ina fatan wani bai rigani yad'awa ba... "Salma"... Cikin wata siga ya fad'i, kan yace "na jima ina dakon son ki azuciyata,tun ma kan Salman tasan itace... K'allonshi take baki sake,shikam ya zage sai tona sirrin ranshi yake a gare ta ido bud'e.. Dad'i, farin ciki har ya kasa misaltuwa a gun Salma,So d'aya ne, tasan Ya Ja'afar tai ma. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 8:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 13_Har yai shiru ita kam idonta na kanshi,kan dafa bisani tai kasa da kai cike da kunya,kawai shima sai ya zuba mata na mujiya yana murmushi. Magana suke jiyo wa kasa-kasa,duk sai suka zuba ma kofar ido. "Ba mutunci ace kowa yana wuce wa yana ganin ku a t'saye a titi, gaba na fad'a miki ki nemi koh zaure ne koh cikin gid... Shiru Abban yai dan ganin Ja'afar a zauren da Salma. D'ukawa ya danyi kan yai ma Abban sannu da zuwa. Cikin sakin fuska Abban ya amsa,Salma ma ta mai kai duk'e. Sim-sim Ummi tazo ta wuce,dan duk iskancin ta tana bala'in tsoron Abban su sosai. Yana shiga gida shima yai mata sallama da alkawarin gobe zai zo dan jin amsar shi. Da t'sananin farin ciki ta shiga yau, haka dashi ta tashi. Tun jiyan Ummi ke ci mata kunu, tasan kuma d'uk akan Muzammil ne,shi yasa koh bi takanta batai ba. Washegari tun kan Ummi ta shiga wankan yamman ta na kullum Salma ke gaban mudubi, sosai take k'yali, yau d'aya ta bata lokaci dan Ja'afar d'inta. Ummi da tun dazu ta fito tana jira ta ta6e baki, ''kiyi kare ni ki ban waje na zauna Malama... Juyo wa tai da tana yage mata baki, "dan Allah Ummi nayi k'yau?.. Bar zancen wasa. Baki ta ta6e kan ta juyar da kai gefe, "oho miki ni kar ki daman. Murmushi tai kan ta tashi ta bata gu. Bincike ta fara,a babu babu Mama kala 5-5 ta musu kayan _candy_ na ke ce sa'a, ciki masu ruwan _purple_ ne kusan duk. Cikin nishad'i ta ciro attamfa wata mai _purple_ da rat'sin _yellow_ riga da siket, murmushi tai dan tuna wa da kalar da Ja'afar yafi so kenan. Tunda ta zura kayan ta nad'a d'auri take bin kanta da k'allo a mudubi ta gefen Ummi. MashaAllah tai k'yau, gashin da ya fito ta kasa take turawa cikin dank'wali,ta kai dubenta ga Ummi wacce sai ko'k'arin fiddo nata take tabi dank'wali ta kansu. Murmushi kawai ta mata,tasan da tace ta mayar su ciki ma a iska. Sai dai tana d'akko turare ta hau feeeee ba ko kakkautawa. "Haba Ummi,turaren nan kinsan haramun ne sashi ki fita koh?.. Ga gashi kullum sai ance ki alkinta shi.. Allah kina *TABARRUJ* da yawa.... Galala take k'allonta, kan ta ja t'saki tai waje. Iya wuya Salma tazo, ta bala'in t'sanar t'saki. Ba'a jima ba Ja'afar yazo.. Tabarma yau ta d'aukar musu,shima yasha wankan farin kaya da farin takalmi _half cover_ sosai yai mata k'yau. Yadda yake fara'a da bin k'allonta tasan itama ta wanke shi. Suna t'saka da gaisawa cikin nishad'i yaro yazo,wai tazo a waje inji Ummi. Tuni ya sauya,dan yaga zuwan su Muzammil. "Minti biyu kawai.. Kai ya k'ada mata da dan yake. Tana fita suka ware gefe,tsakani da Allah ta fad'a mishi yai hakuri. Baki sake yake binta dashi har ta kule cikin gida. Amma Ja'afar ya bala'in k'wada shi da kasa,dan haushi koh isma'il bai jira ba yai gaba. Ita kam tana zuwa ta bashi amsa gamshasshiya, wanda tasa fara'ar Jafaririn ta dad'u ba shiri. Tad'i suke kamar ba gobe, mot'si kad'an yace "kinyi k'yau..... Itama cikin kunya tace yayi shima. *************** ************** "Naga sai zarmewa kike fa akan Ja'afar salma,sam kinfi k'arfin shi kima ji da wai,gaba ake son ci ba baya ba wallahi,d'uk da ban san wacce iriyar amsa kika bawa Muzammil ba... Da harara Salma ta bita, kan tai k'wafa, "ina ruwan ki da sha'anina? Ke har kin isa ki fad'a min wanda ya dace dani Ummi? Baki Ummin ta ta6e, "ke dai kika sani,dama ni meye nawa? Ni koh ana saurayi mey zanyi da Ja'afar mai shegen dacin ran t'siya... "Wai ku baku zama inuwa d'aya ne da juna Salma? Mey yasa baki iya daga ma Ummi K'afa sai kin tanka mata kullum kuna sa makota na jin ina daga murya.. Kasa Salma tai da kai kawai,tasan yanzu in mama taji ta kad'e.. Kamar k'wa wacce Ummi ta karanci zuciyarta ta amshe.. "Wai fa mama daga shawara ta tsaya min masifa,yau akan wannan dan gidan Malam Kabiru mai shago ta kori Muzammil,daga fad'a mata gaskiya ta hau ni da masifa.. Dan Mama daga ganin yadda Muzammil ya tafi rai 6ace nasan cewa tai bata son shi... "Eh bana son shi,koh ana son dole?.. Ja'afar d'in da kika rena ni shi ya min ki ji da wai.... "Kunga ku min a hankali,koh yanzun nan na sa6awa mutum... Shiru sukai,yayinda Salma taci ka tai dam. "Ke ummi wani dan wajen Malam Kabirun kike fad'a? Da harara Ummin ta k'allo Salma kan tai ma Mama bayani,"yanzu haka mama Malamin makaranta ne wallahi yana chan yana kokawa da alli.. Jim Maman tayi kamar mai tunani,chan ta nisa tace "Ikon Allah..anya yarinyar nan Salma ba'a min misanye dake ba a layin jarirai a haihuwa ba?... Mutum arziki na binshi yana ki?...Ina laifin yaran nan?har kasa suka gaida ni,ga mota ga boko..amma in banda abinki mey na sama yaci bare ya bawa na kasa? Da shagon uban zaku dogara koh da kud'in malami?..... Shiru Maman tayi ganin yadda Salman ke hawaye... "Au,au,Salma kuka? Daga fad'an gaskiyar? Kai ta k'ada ma Maman. "A ni tawa mai sauki ne Salma,ina d'ai hanga miki gaba ne kawai... Amma banga abin kuka.... "Wa ke kuka?... Assalamu Alaikum. Shiru sukai salman na goge ido,sai Mama da ta amsa mishi sallama. "Sannu da zuwa Abba. Kai ya daga musu kan ya amsa. D'uk suka tashi sim-sim sukai d'aki. Sai da Abban ya gama komai yasa Mama ta kira su. Kowa tai ladab kai kasa suna saurarar Abba. "Ni ke Ummi na ma kasa gane alkiblar da ki ka kama sam,kullum da wanda za'a ga yazo gunki,sai aukin shegen zance a titi ba wanda ya iya yazo ya samu iyayen ki.. "Ga nan yayarki yau d'in nan yaron nan na wajen Alhaji Kabiru yasa Baban shi yazo muka zanta kan yana son Salma da aure,kuma har sun sasanta da ita.. "Koh ba ai haka ba Salma?... Kai duk'e cike da kunya ta daga kai halamar anyi. "Haka shine musulunci, ta haka kuma ake gane da'ar yaron da zai auri y'arka... Shiru kake ji Ummi anyi lakwas. Nan ya kara ja ma Ummi k'unne kan tara samari da zancen waje,ya kuma ja mata k'unne kan ta fidda na aure koh ya fiddawa mutum. ***** *** Zancen aure dai ya kank'ama tsakanin Ya Ja'afar da Salma. Itama Ummi Isma'il yace da gaske yake.. Mat'sala d'aya tafi damun Salma,yadda komai Ja'afar ya bata na alheri a rene yake gun su Mama, barin Ummi. Dan ita fachaka isma'il yake mata kamar ba gobe. Tun abin bai damunta yau da gobe har ta fara ganin kamar Ja'afar mammako yake mata. Zuciya bata kashi. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 24 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 14_Anyi bikin su Garba. Ana haka saurayin Ummi ya d'allo mata wata sabuwar waya,ita kam tun wata Zain da ya bata,nan habaici ya karu gun Ummi. Biki ya kusa sukai shirin zuwa Borno dangin Abban su. Sunyi sallama da Ja'afar ta shigo gida rike da farar ambalan,d'uk suna zaune t'sakar gida har Aunty A'i da yaronta. Hannunta Ummi ta k'alla, kan cike da shakiyanci tace "ta Ja'afar mey aka samu ne haka har a farar takadda?.. Harara ta dan mata kan ta mikawa Mama. Kai Maman ta k'ada, kan tace "a rabani da kayan haushi,rike abinki kawai ki kirga... Dariya Ummi ta sa,wanda tuni ta kara kular da Salma. "Mama ba ma sai ta kirga ba,dan wallahi ba kaffara nasan kud'in nan bai fi dubu biyu ba... Kanta Salma ta yiwo a tunzure mama tai musu iyaka. "Meye na jin haushi?.. K'yautar tashi tana wuce nan ne?... Ba dai d'an d'an kasuwa zaki aura ba? K'wafa tai,kan tace "baki fara ganin komai ba ma Salma. Aunty A'i ce ta k'ar6a ta kirga,ai kam sabbin hamsin hamsin ne ta dubu biyu. Mama tace "Ahab,na sani ai. D'aki Salman tai tana hawaye,sam bata kaunar abinda ake ma Ja'afar,amma shima da laifin shi,dubu biyu ina zata kaita? ****************************** Biki kam yazo,gashi yau har anje jere, k'warai sunyi mamakin gidan Ja'afar da gina kuma da kanshi. D'uk da ba wani babba bane,dan koh t'sakar gidan karama ce,babban _parlour_ ne sai _bed room_ da band'aki aciki,ga _kitchen_ a ciki karami,sai d'aki d'aya daban a waje, d'ai d'ai zaman mutum d'aya de,rufin asiri dai ak'wai shi,Alli da shago sunyi rana. Sa6anin Ummi mai tafkeken gida da mai gate yasha alatu. Yanzu lefe ake wat'sa ido aga na Ja'afar, dan tuni na Ummi yazo san barka,sai zuzutawa ake. Salma in ta tuno gabanta har fad'uwa yake,fatan ta Ya Ja'afar ya fitar ta a magana. Dan tun a kud'in anko taga tasku,dan isma'il ankon k'yauta yai ma k'awayen Ummi da dubu ashirin nata na fitar biki. Shikam sai hakuri yake bata,kan shi bai d'aura ma kanshi abinda bazai iya ba,bare daga baya ya dame shi. Kawai sai ta toshe k'unnenta gun su mama,komai ta samu ta samu,wanda ta rasa tasan bai da hali. Mamaki kam Ja'afar ya bama su mama, dan ak'wati shidan nan y'ar yayi sai da aka bat'se ta da kaya, ga uban _cosmetics_ har a jakar Ghana must go. Aciki da swiss d'aya, holland biyu,engla biyu,sai su code dav'ior,sauran kam duk kana na ne su dangin material. Salma baki har k'unne jin ba wanda ya kushe a dangin sai d'ai ace na Ummi yafi t'sada. Anyi biki lafiya kowa ya wat'se an bar amare da halin su a gidan su. Kauna ziryarta taga gun Ja'afar mai t'sayawa a rai,sosai sukai amarcin su cikin kula da tarairayar juna,musamman ga Ja'afar d'in. _kitchen_ tare,wanki tare,shara tare,duk aiki in dai ba ya fita bane yana a makale da Salman sa, d'uk wata kulawa tana ganinta a gun Ja'afar,shi yasa sai abinda yace take aiwatarwa matukar bai sa6a Shari'a ba. Yadda ta fuskanta ma kamar bai kaunar tai nesa dashi,koh dan ganin har wata biyu kenan da bikinsu amma ba inda taje sai barkar Aunty A'i da makotansu da taje tun tana sati daya da zuwa. Sai dai tai ta jiyo shewar su ta katangar gidan halamar ana ta _chapter_. *Farin Bacin komai* Yau tun tashinta sallar asuba ta kasa komawa bacci,sakamakon tun dare da yace yau ta shirya da wuri zata gida. Dan farin ciki ji take kamar a wani garin zata je musu. Waya tai da Ummi kan zata fito yau gida. Gaban madubi take tana yi tana k'allon agogo har sha d'aya saura. Karar _machine_ d'in Ya Ja'afar taji a kofar gidan,sai ta cigaba da shiryawa. Sallamar shi taji,daga d'akin ta amsa tana fara'a. Yana shiga ya jingina da kofar d'akin yana mata murmushi,ta mudubin ta mishi tana d'auri. Kan ya tako gaban madubin ya t'saya ta bayanta. "Sannu da dawo wa.. Kai ya daga mata,sai kare mata k'allo yake, kayan sun mata k'yau, "Kinyi k'yau... Tashi tai da jin dad'in kalaman shi,sai ta dan ja mishi kumatu kan tace "na gode... Muje koh?.. Ta fara nad'a lifaya. Sai ya rike mata daya gefen tana nad'a dayan da murmushi. Da kanshi ya yafa mata akai ya rufe ko'ina ruf. "Ba dan kin nace sa abar nan ba da hijab d'inki za ki sa zai fi min k'wanciyar hankali.. Murmushi tayi kan ta lang'wa6e kai, "ai ba g'yale bane Ya Ja'afar, Allah ina son lifaya. Kai ya k'ada mata yana d'aukar mata jaka. "Toh naji,amma ni banga maraba ba. Murmushi kawai tai tana d'aukan mukulli. Machine d'in ya karkata mata kirar lifan,a hankali take ko'k'arin hawa sai ya dan girgiza machine din,da sauri k'wa ta dafa kafad'arshi suna dariya. In kagansu g'wanin k'yau suna ta nishad'i har suka zo gida. Tana g'yara lifaya tace "bazaka shiga ba?.. Kai ya girgiza mata da murmushi,"ki gaida su Mama, anjima in nazo d'aukan ki zan shiga, yanzun makaranta zan koma. Kai ta k'ada mishi,kan ta bashi hannu,sai ya bata suka gaisa suna dariya. "Abincin ka yana a kitchen a bisa faranti,na had'a komai, a dawo lafiya... Kai ya daga yana mata murmushi,jin yaki tafiya tace "kaje man.. Kafad'a ya make yana nuna mata gefen fuskanshi, kai ta k'ada mishi cikin kunya. "A layi muke fa... Shima sai ya kada kan tukun ya tada sukai sallama. Har ya kule tana daga mishi hannu,kan tai cikin gida. Da dan gudunta ta shiga tana kiran Mama. D'uk suna d'aki, Ummi an hakimce a kujera ana d'anna waya. "Har kun rigani ashe d'uk saurin nan nawa?.. K'allonta Ummi take ganin tana since lifaya,ga flasks da jaka an ajiye. "A ina zaki zo da wuri,ke dad'i miji ce ai.. Banza tai da ita tana gaida Mama, itama Maman a dan ciki ta amsa mata. D'uk sai taji ba dad'i, jikinta yai sanyi,da murnar ta tazo amma sun dakushe mata. "Sai ya barki ki waiwayo mu?.. Maman ta k'alla, kan tai kasa da kai, "ai na zata irin ta y'an da zai miki,sai kin shekara koh kin fito yawan arba'in.... Baki Ummi ta ta6e,kan tace "d'uk mai irin halin Ja'afar ai dole yai k'ulle Mama,in banda haka wata biyu wai sai yau za kizo gidan ku,ni nazo yafi a girga,wallahi tun wuri ki mawa tufkar hanci.. Dan in kika sabar mishi da haka zai mike. Dagowa tai da niyar yi wa Ummi magana Mama ta tari numfashinta. "Y'ar uwar ki ce,dole ta fad'a miki gaskiya, ke zaki nema mana mutunci a gun miji ki ma ji da k'yau. Kasa tai da kai tana murmushi, duk da a zuciyarta bataji dad'i ba sam. "Mama baza'a a sake ba inshaAllah. Da haka aka ware kuma zancen nawa ta tara a banki. "Ni fa ba'a ban kud'in cefane Mama, komai yana kawo min har katin waya,sai dai in ina da bukata yana cewa na mai magana... Baki Ummin ta ta6e,kan ta zuge jaka, sai ga nan kud'i tumi. "Kinga kud'in cefane na,nima ai ba abinda na rasa,ina ruwana da wani ni kud'in kati? Kawai naji dumus ni... Gashi nan na banki ne dana sa Mama ta sai min. Kai Maman ta k'ada, tabbas Ummi tasan ta kan maza,shi yasa take burgeta sosai. Itade Salma an sata duhu,dan sun raba hankalinta biyu. T'saka mai wuya kenan. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:00 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 15_Sai dare yazo a dalilin yadda take fad'in bata gama ba,har cikin gidan ya shiga,kawai kuma sai yake ma Mama k'warjini, dan fuska sake ta amsa mishi,kan suka tattara suka tafi. Koh da Salma tazo k'wanciya maganganun su Ummi take ta tunawa. Ita babban haushinta ma yadda aka fa fad'in koh tsoron Ja'afar take. Washegari ma haka ya yakaita gidan su Abban shi,nan ya wuni suka biya gidan Garba. Yau tun (7:30) ya fita, sakamakon an fara jarabawa a makarantu. Sha d'aya ta gama aiki ta fara jiyo hayaniyar y'an unguwa a makotanta,halamun sun hallara za'a fara chapter. D'uk yau sai hankalinta yai gidan,duk da ba sabawa tai dasu ba. Waya ta d'auka,ta d'anna kiran Ja'afar _no answer_.. Ji take kamar ta zaga in ya dawo ta fad'a mishi,sai dai ta daure. Da yamma kam kamar kullum yazo fita shago tace zata leka makota. Jim yai ba amsa,sam tarbiyar matan unguwar bata mishi ba,baya so Salma tai sabo dasu a samu mishkila,amma kawai sai ya k'ada mata kai, "Sai kin dawo. Cike da murna ta rakoshi har bak'in kofa ta koma d'aki. Da sallamarta ta shiga,tun daga bak'in kofar gidan zaka fara jiyo karad'in matan. Da fara'ar su suka amsa,d'uk sun baje a tabarma, wasu ba koh dank'wali. A dan kunyace ta gaida su, dan ganin duk sun girme ta,sai wata mai kamar shekarunta da D'a a goye. Chan hira taci gaba, zabiyar ciki sai karanta musu makamin kama wuyan maza take. Salma tai shiru tana jin su,tabbas babban burinta shine Ja'afar ya so ta har karshen rayuwa. "Su amarya yanzu ai farin take gani kan a juya mata bak'in bayan.. K'allo matar tai,bata gane nufinta ba,sai dai bazata iya tambaya ba. Haka firar yau ta tashi kan makamin rike miji har Salma ta fito. Tunda ta zauna a gida take tariyo firar sun. Tabbas shawarar nan tayi ta makamin rike miji, ta hakan kam ba yadda Ja'afar zaiyi ya raina ta... Toh amma Ja'afar yana sonta,batajin zai mata dabi'a irinta mazajen sauran Matan da ke fad'i. Nan ta jefar da dayawa a hudubar da taji a makota tai kitchen dan k'unna ritio. Sai d'ai Washegari ma da yamma Salma ta sake tambayar shiga makota. Karan nan kam kir ya fito yace mata a'a, da ido kawai take binshi, "Ya Ja'afar yafi zaman kad'aici ne,ba jimawa zanyi ba ka ji... Ta langwa6e kai. Ba dan yaso ba ya k'ada mata kai. Minti biyar bata kara ba tai makota,gidan chapter. Yau kam a sa'a taje,dan suna a kan firar rashin fitar matar gidan,sai bata dabaru suke akan yadda zatai mijn ya rika barinta fita. "Kar ki fara tambayar unguwa kina fara'a, sosai zaki dake mishi,mud'in yaga 6acin rai toh jiki na bari zai barki. Ni da farko haka Salisu ya t'siro min da k'ulle,tun farko nai ma tufkar hanci,da yace A'a yana fita zan arce, gashi yanzu har ya saduda yana barina duk inda na tambaya. T'sam Salma tai,tana tariyo maganar Ummi da Mama ta ranar,ga nan ta makotanta. Daga ganinsu sun san takan duniya. Tabbas ta yarda itace tun yana d'anye ake tank'wara shi. Tun yanzu ya dace ta takawa Ja'afar birki koh dan ta t'sira daga zargin wai tana tsoron shi. *Wasa farin Girki.* Daga ranar Salma ta tsiri dan hali,fita makota,tambayar fita gida,ga wani t'sarewa da take in tana tambayar. Kamar kullum tazo rakiya taja ta t'saya a gefe, "Ya Ja'afar... Jiyo wa yai shima rai ba dad'i,tare da zuba mata ido,yasan abu daya zata tambaya. "Zan leka gidan Maman Ummi gobe suna za ai k'ulli... K'allonta kawai yake, yadda tasha mur tamkar wanda take bashi umarni. "Anya Salma wani abu bai shiga kanta ba kuwa?.. Gaba daya ta sauya mishi hali k'wana biyu in dai akan fita ne.. G'wara tun wuri ya taka mata burki dan yaki jinin yawan fita sam shi. "Kiyi hakuri Salma,ki bari ki leka goben tunda suna ne... Tuni ta k'ank'ance ido, "gaskiya kar ka maidani saniyar ware a unguwa ya Ja'afar, yau k'ulli kowa ya je sai ni ce bazani ba?.. Ai sai a chake ni gobe dama suna fad'in ni dad'i miji... "Kuma ma ba wannan ba,nima sai ina zuwa za'a zo min in nawa yazo ai.... Shiru tai ganin yadda ya zuba mata ido yana kallo, chan ya nisa "amma Salma kin fuskanci kin fara sauya hali kuwa?... Kin koyi ja dani,kin koyi gantali k'arfi da yaji.. K'alloshi tai a wani iri, "au gantali ma nake Ya Ja'afar?.. Fisabilillahi wace fita ce nake yi ba dalili? A satin nan sau biyu koh uku ne fa na fita kuma dubiyar Ummi ne ba wani waje ba, koh shi ka ke nufi da gantalin? Kai ya k'ada,"kar mu rika ja in ja dake Salma,kiyi hakuri kawai gobe ki je... Juyawa yai ganin tana neman wata maganar yai waje, baki ta ta6e,kan tai cikin d'aki. Tana jin tashin machine d'inshi ta zaro hijabi ta k'ulle gida tai cikin gidan k'ulli. "Ai na zata bazaki zo ba,da har zanyi aike naga machine din maigidan. Hijab ta cire ta jawo jarka, "bari ke dai Maman Ummi,dak'yar na fito fa.. Murmushi tai kan ta d'akko wani abu a bakar leda,"yanzu saratu ta fita an kawo sabbin kaya dakakku wallahi,tai ta jira baki zo ba zata tafi na dau miki wannan... K'ar6a tai tana dubenshi kan ta kunce ledar,roba ce karama da wani abu mai d'anko. "Takalmin Kaza ake fad'a miki,nasan yafi haka,kawai ta mana sauki ne.. Amma abin ba magana,sai an g'wada akan san na k'warai... Dariya suka sa aka tafa harda shewa. "Wannan ne kawai makamin wulakancin D'a namiji,tunda kuka d'aurani kan _network_ nake son raina Allah. "Dari biyu ai ma yai araha... Bari yazo dari biyar zan tat'sa, dan asusu nake kan zuwa watan haihuwar Ummi na tara da yawa... Sai da aka gama k'ulli ana firar duniya,a debo gulma har aka gama,ana kiran magriba ta tuna Ja'afar, da sauri-sauri tai gida dan yau abinci ta zarce tayi. Kamar kullum ya dawo bayan magriba ana kiran isha'i, sai dai sam ranshi ba dad'i,nan tasha jinin jikinta,koh ya dawo bata gida ne? Har yaje masallaci akai isha'i bai dawo ba har ta gaji da jiranshi ta k'unna inji. Sai chan kusan tara ya shigo,har yanzu jiya iyau,sam kuma sai taji ba dad'i, tun kan ya fad'i lefin da tayi,amma de sai ta dake. Komai yayi,dan har abinci ya ci,sai dai fur yaki sakar mata. "Wai Ya Ja'afar mey nai ne ka ke ta shan kanshi?.. K'allonta yake da mamakin anya Salman shi ce wannan?.. Bai da amsa,sai a gunta kawai,saboda haka ya tashi yai hanyar d'aki. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:03 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 16-Ya fito a band'aki ya ganta zaune a gad'o,kai ya dauke yana goge jiki da _towel_,d'uk sai jikinta yai sanyi,tabbas tasan Ja'afar kila zuciya yayi,har ya gama shirin bacci uffan bai ce mata ba,tuni ta fara kuluwa ganin ya ja filo bai bi takanta ba. "Wai mey in ma ina ta maka magana tun dazun?.. Kai ya dago ya k'alleta da tuhuma, "mey kika ce ban amsa miki ba?... Baki ta turo gaba kad'an, kai ya kada,tukun yace "Salma!... Salma!!.. Dagowa tai ta bashi hankalinta dan jin kiran da yawa. "Na'am.. Ido ya tsura mata,sai tai gefe da nata. "Ina kika fita dazu har magriba?.. Jin tambayar tai ta bazata,hakan yasa ta kasa K'allonshi, sai da ya maimaita tukun ta amsa a hankali da "gidan k'ulli... "Gidan k'ulli?.. Mey mukai dake toh kan na fita?... Duk t'siya ta ki jinin kuma taga ran Ja'afar ya 6aci, sai dai an rinjayi zuciyarta. "Kai hakuri... Itace Kalmar da ta fad'i. Tashi yai ya jingina da pillow,kan cikin nut'suwa ya fara mata magana. "Ba wannan ne ba karon farko da ki ke fita ba'a son raina ba Salma,nasha aiko yaro da sako yace gida a k'ulle yake,amma nai ta daga miki kafa. Duk gantalin da take bada yardar shi ba sai da ya sanarta,ga t'sinuwar mala'iku dake binta har ta dawo... "Sam wannan ba Salman da nasani a wata 5 d'in baya ba... Wannan cikin wata d'aya ta sauya,bata jin magana ta,duk abinda tasa kanta take ganin shine d'ai dai shi take... Sosai ya kasheta da kalamai,har ta fara hawayen wai bata jin magana. Murmushi yai kawai,kan ya dan taso ya janyo ta ya hau kuma lallashi,da alkawarin bazata kara ba,sosai ya ji dad'i,dan yana son mutum mai gane kuskure in ya yi. Washegari _week end_suna ma haka tai shiru,sai dai kasan ranta ji take kamar tai filfilwa taje gidan. Tasan iyanzu an kusa sauke abinci ana ta cin chapter ba ita. Sai dai tai ko'k'arin ganin bata tambaya ba. Shi kuma ganin haka yasa yaji dad'i,fatanshi yasa Salma ta g'yara ne. Ce mata yai yana zuwa,yana fita ta kasa zaune ta kasa t'saye. Anya bazata leka ba kan ya dawo?.. Dan tasan yanzu ana chan an kafa da ita uwar son miji. Sau biyu tana k'wata fita tana dawo wa,a na ukun taji dirin machine d'in Ja'afar ta koma. Sai gashi da leda baka a hannu. Sannu da zuwa ta mishi,burinta ya fita ta fice, amma fur yaki. A jima kadan ta k'alli agogo,kafarta har kaikayi take,da ya k'allota ta sai ta sau mai murmushin dole. Kamar ya kula sai yace bari yai wanka,yau sha biyu yake son yaje shago. Ita dai ta samu ya fice,Allah koh satar hanya sai taje gidan sunan Maman Abba. Toh sai ma ya barta harda mika mata ledar riga ta barka. Abu kamar gaske Salma kamar anyi hankali, sai hali ya dawo sabo. Shiga makota kam Ja'afar har yai hakuri ya zuba ma Salma ido, Gashi yanzu su Salma har ketare ana t'sallakawa,kusan duk yanzu unguwar sun san da Salma,ga surutu da t'sabar manyance da ta koya zama cikin manya. Ranar Garba suka zo gidan a 6ame da mukull,sai ya d'au waya ya kira Ja'afar din. "Ba kowa fa a gidan nan Aboki,dan da mukulli a 6ame.. Daga chan Ja'afar yai t'sam, kan yace "oh,sorry pls,na manta tace zata je dubiya, ga wayanta ba chargy... Kai Garban ya kada "toh dai mun fita,dama ita ke mitar madam shiru,yanzu kam ma had'u suna. Murmushin dole ya k'akalo,yana cewa ace Billy tai hakuri. Bayan sun gama ya ajiye waya,Salma tasa ya tafka karya,dan da abin kunya ace yana mai gida amma bai san matar gida bata nan ba... Toh mey zai wa Salma ne?.. Ya mata d'ukkan nasiha,yayi fad'a, yai lallami,amma tamkar a iska yake zubawa. Sai tayi kamar ta d'aina, gobe ta fidda sabon hali. "Assalam Alaikum... Kai ya dago,ganin mey sallama yasa ya fad'ada murmushin shi, cikin girmamawa yace "a Abba,sannu, yana sunne kai, murmushi Abban yayi,kan yace ''yauwa Ja'afar,ka ga na dawo,zan dan zaga ne, baya,dayan shagon nan ba kowa ne, nazo arar Sadi minti biyu.. Kai kasa yace "Bari na zauna kan ka dawo nan bana komai. Yasan zai samu ma damar yau amar da abin da ke ranshi. Yana shagon Baban ya k'wance ya d'aure, ya fad'a ya je gida ya shiga uku gun Salma.. Shawara d'aya ya yanke, gun Mama, dan yaga ita batta zafin Baban. Tun yamma ya tashi,bayan sun gaisa da Maman faran faran yake sanarta halin da Salma ta t'suro mishi. Kamar abin kirki harda bashi hakuri,da fad'in zata t'sawatar mata. Sai d'ai tana fita Ummi da tun shigowarshi tai zamanta a d'aki ta fito. "Kai amma mama mutumin dan rainin hankali ne,wai kinji fitar Salma tai yawa? Matar da sai tai sati biyu wataran ba tazo gidan nan bama bare har fitar ta tai yawa.... K'wafa Maman tai,kan tace "ke lefin shi ki ka ga?.. Ai lefi na gun Salma da ta zauna yake juyata kamar waina... A zamanin y'ancin kai ake yanzu, bana tsawalawa dana.. Kaza kaza,har Abba ya shigo zaure ya dan t'sinci wani zancen,amma bai gane kanshi ba. Kullum Ja'afar na sa ran yaga Salma ta sauya,sai dai shiru,sai yai tunanin fad'an Maman ma bai shige ta ba. Ranar Garba yace a gidanshi zai magriba yace Salma tai musu irin gurasar nan tun tana amarya. A gabanshi ya kirata, a lokacin an zube ana ta firar kashe wando a makota bayan layinsu, Koh da ta sauke waya ta cigaba hirarta. Chan kusan magriba ta kusa ta tuna da zancen Ja'afar,kusan ma d'uk y'an firar an wat'se amma Salma matar gida ta riketa wai suna firar su zata tafi? Yaron gidan tasa yai gudu bayan layinsu ya siyo mata gurasa mai siga ta karbi kud'i gun matar gidan. Cikin nishad'i suka zo sai dai gida a 6ame,ga yau ta bar mukullin shi a ciki. Ranshi in yayi dubu ya 6aci,basu jima ba sai gata tanan,duk tabi ta burkice, duk da koh k'allon inda take Ja'afar bai ba. Sai da Garba take magana tana ko'k'arin bude gida. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 17_Shi dai Garba har suka shiga gida yana zungurar abokinshi kan ya saki fuska. D'aki ta shiga tana mai adu'ar Allah yasa a samu gurasar nan,in ba haka ba yau ta kad'e har ganyenta a gun Ja'afar. Suna t'sakar gida suna alwalar magriba sai ga yaro yai sallama rike da k'wano,da sauri ta fito ta amsa,har ta shiga Ja'afar na bin bayanta da ido,k'wafa yai kamin yai ciki, shi dai Garba duk ya gane da wata a kasa. Kitchen ta sameta tana jera su a faranti. Tasan shine amma fur taki daga ido ta k'alleshi. "Nagode Salma, kinji? Na gode,amma ba zanci gurasar titi ba ki sani... Kofar kitchen din ya rufo sukai waje. Ita kam koh a jikinta,tunda de ta t'sallake fad'a ai shikenan. Yau dai ya kasa d'aurewa, har sai da ya sanar da Garba halin Salma ba ragi. Sosai yai mamaki,wai Salma ce da halin nan? Sai dai kawai ya bawa abokinshi hakuri, da kuma ya rage saurin fushi... Haka ya wuce gida ba tare da shima yaci ba. Da dare ya d'au pillown shi ya koma parlour,baki ta ta6e tai k'wanciyar ta. Sai dai koh minti ashirin ba ai ba ta hau juyi,ta ture pillow,dan Allah yaga bata saba k'wanciya ba'a hakarkarin Ja'afar ba,duk fad'a kuwa. Ba shiri tazo bada hakuri dan tasan ya bala'in jin haushi. Shi kuma haushin shi d'aya da hakurin Salma,tunda ba wai zata g'yara bane. Kuka ta fara mishi harda shura kafa kan wai ya juya mata baya yaki kulata. Juyo wa yai yana k'allonta, duk da a kule yake da ita amma har kusan dariya yaso saka. "Ba nace kai hakuri ba,Allah kasan ban ta6a kin yi maka abinci ba da gangan... Tashi yai ya zauna a kusa da ita. "Toh naji na hakura,bar borin...ya sa hannu zai goge mata hawaye sai dai kamas... "Au kukan ma na karya ne ashe?... Dariya ta fara ta d'au mishi pillow sukai d'aki. "Ina a gidan nan Allah ba kai ba k'wanan parlour. Murmushi yai yana mai tausayin kanshi, ina ma Salman shi ta da ta dawo mishi... Ina ma zai yuwu ace kullum yaso ganin Salma zai sameta a gida haka?... Ya sani da yana son Salma,so ba na wasa ba,amma k'arfi da yaji so take tafi k'arfin shi,ga ko kadan bai kaunar yaga fushin ta. Ina ma itama haka take nannan da nasa fushin... Yasani da *Mai Hali Baya fasawa* **************************** Sauri take tayi,dan yau gidan mai gumama suka je,tasan kuma tabbas Ja'afar yana hanya. Aikwa tana zuwa ga nan machine d'inshi a kofa halamun yana ciki. Duk da tana jin dan shayin shiga su ar'ba, haka ta d'aure ta shiga. Takaddu yake nema, da sallama ta shiga, a chan ciki ya amsa yana cigaba da abinda yake. "Sannu da zuwa... "Uhmm.. Kawai yace, sai ta ta6e baki. "Gidan fa mai gumamar nan da na fad'a ma jiya ta aiko mana za'a kawo muka je..kaga zuwan banza mukai ma wai sai gobe. A dirare ya k'alleta lokacin da yake tashi, ganin yai banza yasa tace "ni fa nan kad'ai naje,sai gidan Maman Ummi dana biya mata muka tafi.. Kai ya k'ada, kan yace "yayi k'yau... Maman Ummin ce mijin ki koh mai gumamar?... Ido ta zaro,sai ya kada kai, "no ba wannan ba ma, wai d'uk inda kike azarbabin zuwan nan wa kike gani yana zuwa gidan ki yafi minti goma aciki?... Koh d'uk suna da aikin yi sai ke kad'ai ce bakki shi?.. Salma ki nemi mutuncinki da hannunki,a ganina zai fi mu.... "Ka ga malam,ba sai ka zage ni ba zan san dama kana kule dani ba,daga fita nan da nan din shine har zaka na cemin wata gantalalliya?... Haka kawai,in ma kayan ne naga kai zan sawa ba wani ba,toh meye abin zafi aciki?. Kai ya k'ada kan yace "babu... Amma wallahi kar gobe ki sake ki kara fita gun wata mai gumama,in ba haka ba zan mugun sa6a miki... Waje yai rai 6ace, "Ja'afar?... Ni zaka sa6awa?... Chak! Ya t'saya ya kasa gaba, a hankali ya juyo fuskarshi d'auke da mamaki. "Salma... Yau ni kike kama sunana garangatsai ba koh rufi?... K'ugu ta rike tana girgiza, "ai sunan ka ne naga.. Kuma muna kama sunan Allah ma bare wani chan... Na gaji ne da hancini. Kai ya k'ada yana murmushi, tabbas ba abinda yai saura da gantalin Salma bai gur6ata ba,ciki kuwa harda iya fit'sara. Sai ya k'ada kai ya fice,dan yasan komai zai iya faruwa in ya tanka. ~~~~~~ Washegari haka aka tashi kowa rai ba dad'i, yau ce ranar farko da har aka waye gari ba'a shirya ba. Ga yau week end,yana gida yaki fita shago. Har yamma ba bayani, sai dai yai bacci,ya je masallaci ya dawo. A sama take,dan gani take da gayya yaki fita dan ai ba ita gidan gumama. Ya dawo daga masallacin la'asar ya shiga wanka. Maman Ummi ta turo tazo suje kan a za6e,yana jin lokacin da tace dan aiken yace tana zuwa. Yazo fita ta biyo shi,dan tambaya a ganinta ta wanke lefin jiya ya barta. "Ya Ja'afar zamu gidan wannan mai kayan Maman Ummi na jirana. Ja yai ya t'saya, kan ya juyo ya koma parlour,ba musu ta bishi ai wacce za ai. "Tun jiya ai mun gama magana dake,babu fita... "A gaskiya sai na je, gashi nan ai kai ka ke jawo komai, da lallami na tambaya ba zaka barni ba,sai na fita cibi ya zama kari... Haka kurum yanzu haka jirana ake ka ce wani bazani ba..ta karasa tana kunkuni. "Sai kinje koh?.. Cikin fusata tace "eh.. Murmushi yai ya k'ada kai, "Bazan hanaki ba toh, sai dai wallahi ki sani, mud'in kika sa kafa kika fita,toh *A BAK'IN AURENKI*.... Bai jira komai ba yai waje,yana jiyota tana ai wallahi bazaka sani kaffara ba,fita kam nayi na gama. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Like 路 6 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Ummu Maryam Tahir Sannu da qoqari 6ter Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Kareema Wakeeli Tnx Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 18 _Kitchen_ kawai ta leka,ta d'aura guntun ruwa a tukunyar silver a _hot plate_ nata karama nepa suka d'auke wuta. Kamar zata kashe,kawai ta bari,a ganinta ba komai. Kan su kai gidan gumama kuwa 5 tayi,fatansu Allah sa ba'a za6e ba. Kaya kam gasu masu k'yau, tuni ta fara daddagawa tana ware na wara. "NEPA"... Cewar yaran gidan, sai dai da halamun su Salma hankali yayi kan gumama. Suna nan a gidan har kusan k'arfe 6,amma basu gama da mai kaya ba. Kamar ance daga kai sama,sai ga nan dan hayaki na yin sama halamar daga nesa ana gobara a wani gu. "Ina ga wutar dazu tai ma wasu aiki,hayakin nan gobara ce duk yadda akayi.. Kai Salma ta k'ada, "koh taya ake konawa ba... Sai dai kan su farga ihun gobara har kusan layin da suke. Maman Ummi tace suzo su je,in yaso daga baya sa dawo suyi bayanin. Da sauri Salma ta tare, "A'a Manan Ummi,nasan yanzu Ya Ja'afar na hanya 6 saura. "Muje dai koh gobe tunda ta kirga wanda muka d'auka ma dawo ai sabon lissa... "Umma!..Umma!!... Da gudu yaron mai gumama ya shigo, matar tace "lafiya irin wannan gudu? Ince dai ba daga gun gobarar ka ke ba? Yana haki yace "a gidan Aunty Salma ne fa Umma.. Ana ta neman inda za'a shiga a k'ulle, yanzu aka kira Malam Jaaf... "Na shiga uku... Ni Salman koh wa?.. Kai yaron ya daga,ai ina,da gudu ta fice ta wat'sar da kayan a nan ta bar Maman Ummi da kira. Kamar wata sabuwar kamu haka ta iso wajen,kofar gidan cike da jama'a wasu na kok'arin sanya t'sani su haura. A ka ta d'aura hannayenta d'uk biyun,tama rasa ihu zata kurma koh kuka. Baban Ummi ne yace ina mukullin gidan?.. Nan ta fara tunanin mukulli?.. Innalillahi, ta barshi shima gidan gumama... Baya ta fara yi ganin Ja'afar da Garba sun faka mota a chan gefe, a gigice suka karaso, "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un"... Itace kalmar da Jaafar ya iya fad'i. Ina kan ta farga sai ga hawaye na zuba tana girgiza mishi kai,mukulli Garba ya tambaya, kan cikin azama ya lalubo a aljihu ya bashi. Salman ya k'allo cikin tausayin kanshi, har yanzu hannu na ka tana k'ada kai tana kuka. "Shikenan kin zaunar mu Salma... Burin ki ya cika sai ki zuba ruwa a kasa ki sha.... Tuni ta kara fashewa da kuka. Fad'in "A kashe meter... Ne yasa yai cikin gidan da sauri. Ba ka ganin koh ina sai dusu-dusu dan hayaki. Da taimakon Maman Ummi ta bar kofar suka shiga daga cikin gida. Sai dai har yanzu kuka take baji ba gani. Yau tasan ta kad'e har ganyenta. Motar kashe wuta ce ta iso,da taimakon dak'yar wuta ta mutu. Ilahirin kitchen da bedroom ya kone ya laso parlour ta silin Allah ya t'sayarta. Fito wa tai bayan taji komai ya dan lafa ta leka gidan,sai ga nan Ja'afar din sun fito rike da barbadin _documents_ nasa a hannu. Kamar munafuka ta dan ra6a ta shigo kai duk'e tana jan hanci. Sai da yazo dai dai ita ya t'saya. Kanta kasa tana sharar hawaye,a hankali ya saki burbudin takaddun ya fice jiki duk yayi sanyi. **************************** Zaune suke a bak'in masallaci shi da Garba bayan komai ya lafa yana tausarshi,yan unguwa sai jajanta mishi suke suna tafiya. "Dan Allah ka'r ka ce zaka d'au mummunan mataki akan Salma, kai hakuri,ubangiji ya mayar ma da alkairin da ka rasa. Shiru Ja'afar d'in yai,zuciyar shi sai tafasa take,dan ma yana ta kok'arin neman kariya daga zugar shedan. Zuwa chan dai ya nesa, "Babban ni takaici na Garba Takaddu na ne,tun jiya ake _verification_ gobe ne namu,ni bana ta Salma,dan a bakin aurenta ta fita... "Ni ga nan d'akin waje zan iya maleji. Kafad'arshi Garban ya dafa,lalle kowa da jarabawar shi a rayuwa,shi kuma abokinshi ta mata Allah ya bashi. "Yanzu toh ya za ai?... Murmushi Ja'afar d'in yai wanda yafi kuka ciwo... "Ya k'wa zanyi Garba?.. Kana sane da gamnatin nan tamu, wa zai k'ar6i uziri na gobe?.. Shiru yai mishi,dan tabbas yasan bai da abin fad'a ma abokin. Gida suka koma,tana nan inda suka barta a durkushe ta tasa takaddun a gaba tana shesshekar kuka. Ja yai ya t'saya yana k'allonta, muryar ta har ta dashe. Abin haushi wai kuma zuciyarshi ta fara tausayinta. Da sauri ya d'auke kai daga k'allonta dan jin zuciya na ingiza shi yaje ya lallaso ta, Salma ce fa... Dake wa yai ya daure tukun yace "toh meye ne na kuka kuma Salma?..ki tashi kawai kije gida dan sharad'in dazu yana kan ki.... Da sauri ta dago ta k'alleshi, tuni taji kukan ya kafe,sai ido da ta kafe shi dashi, shaf ta manta wani sharad'i ne ma? Tuni ta tafi duniyar tuna abinda ya afku ka ta fita. Garba ne ya katse mata tunani da fad'in "haba dai dan Allah? Wannan sharad'in bai k'yautu a gun ka ba Ja'afar.. Aure ya fice wasa fa.. Ka janye sharad'in nan tun kan kowa ya ji ku koma auren ku.... Da sauri ta k'allo Garba,duk ta kasa ta6uka komai, Mey Garba yake nufi da su koma auren su? Yaushe Ja'afar ya sake ta?.... Bai furta ba sai dai in yanzu.. Cikin muryar kuka tana ka'rkarwa tace "bai sake ni ba Garba, auren mu na nan... Koh yanzu ya furta?.. Banji ba Allah... Ni bai sake ni ba...bai sake ni ba.. Sai ta karasa tare da fashewa da wani kukan mai ban tausayi. Ido kawai suka zuba mata, tamkar zararriya haka take magana. Duk sai ta karya musu zuciya, barin gogan,har bai san ya je gareta ba,da zummar dago ta yaje ya lallashi abarshi,sai dai kamar wanda aka t'sayar ya d'auke hannunshi, baya ya koma yana rint'se ido... Tabbas yanzu saki ya gifta a tsakani,bai da _right_ na ta6ata,tabbas bai dashi. A hankali ya furta "Salma kin cuce mu... Kin fara dasa katanga a tsakanin mu... Ban san da abinda na rage ki ba Salma...ban sani ba, dazu a yadda nake jin zuciya ta,wallahi dan banzan doka naso na miki,Allah ya kareni da yin kuskure. Baya ya juya mata,kan ya k'allo Garba. "Dan Allah ka kaita gida gani nan zuwa... Waje yai ya barsu nan,Shikenan ta tabbata,ba makawa Ya Ja'afar ya sallama ta.. Ai tuni ta kara jiniyar kuka,dak'yar ta tashi sukai waje da Garban. Sai duba Yayan nata take koh zata ganshi. "Muje Salma,InshaAllah komai zai daidaita,.. Juyowa tai ta sadakar da yai nisa... Yana k'allon su har suka kule kan ya fito a inda ya 6oye a bayan bishiya. Harda goge y'ar k'walarshi... Salma kinyi aiki. By Feenat Ja'afar 9/29/16, 9:06 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?... Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima. Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar, kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta. Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar, "Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya dago,mama in banda harara ba abinda take sakar mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama, kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba... Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada. "Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma... Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma? Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka, "Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce... Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai yace bari yaje gida shima ya d'au machine sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace "sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?... "Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na 6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi, ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya 6alla tan. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Zeenat Yakubu tnx 1st 2 cmmnt Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?... Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima. Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar, kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta. Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar, "Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya dago,mama in banda harara ba abinda take sakar mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama, kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba... Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada. "Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma... Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma? Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka, "Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce... Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai yace bari yaje gida shima ya d'au machine sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace "sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?... "Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na 6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi, ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya 6alla tan. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 20_Koh da Ja'afar din yazo haka ya kara bashi hakuri kan suka d'au hanya. Zaune take a d'akin da ya rage musu,duk ta dawo kalar tausayi. Waya yake amma yana k'allon yadda ya takure kanta tana K'allonshi. D'anna wayar ya cigaba bayan ya gama, cikin nut'suwa ta hau bashi hakuri, kan Allah bazata kara ba. Sannan bazata kara fita ba izinin shi ba. Shiru yayi,hakan yasa ta fara kuka tana rantsuwa kan haka. Sauka yayi akan 1sittern dake a d'akin ita kad'ai sai karamar katifa da filo daya da ledar t'sakar d'aki. Yasan dan so yana ma Salma,sannan yana matukar ganin darajar Abba cikin idonshi, sannan yana mutunta soyayyar da ta mishi a da chan baya. "Salma kin d'aina so na yanzu sam,shi yasa ki ke ganin damata a yanzu... Ki duba kiga abinda yawan ki ya wanzar mana...nayi imani a garin saurin ki fita ne har kika manta wani abu a k'unne a kitchen... Ki duba irin kinjin magana ta abinda ya jawo... Salma takadduna sun kone kaf...sai guntu, sanin kanki gobe muna da _verification_ da za'a gunar mana. "Ba wanda zan je ma hannu Rabbana ya k'alle ni... Kinga meyiwa na rasa aiki,dan zan shiga _miss call_... Kinga kin zaunar mu... Ba gida ba aiki.. Cikin kuka ta mat'so tana bashi hakuri, "kai hakuri banzan kara ba Allah.. Murmushi yayi kamin ya janyota da sigar lallashi. "Ina sonki Salma,kisa a ranki komai zanyi zanyi ne _for your own good_... Bazan ta6a miki abu dan tuzarci ba... _cos I love you_... Kank'ameshi ta kara cikin jin dad'i... Tabbas tana son mijinta, zata jure komai dan 6acin rana irin wannan. Koh da yazo k'wanciya ita tana gefe yaga bata niyar k'wanciyar tunda ta fito a bayan gidan waje. Daga k'wancen ya mika mata hannu halamar tazo. Har wata kunyarshi ce ta da tazo mata yanzu. Da rarrafe ta isa gareshi,sai ya nuna mata kafad'arshi kamar kullum,nufunshi ta sa kanta. Da murmushi ta g'yara, kan cikin nut'suwa ta zame ta k'wanta. Duk kusan tare suka sau ajiyar zuciya, bata ta6a saba bacci a kafad'ar Ya Ja'afar ba... Haka shima bai ta6a sa6a bacci,ba tare da Salma na hakarkarinshi ba. A daren ta tabbatar mishi da lalle har yanzu tana son nashi,har ma tai kok'arin mantarshi wasu abubuwan. *Hmmm..Allah sa da gaske ne Salma*... *************************** "Haba dai? Yaushe?.. T'salle ta doka lokacin da ta sauke wayar a k'unnenta... "Ya Ja'afar.... Da sauri ya katseta da "Ummi ta haihu... Yana murmushi. Hannunshi ta kamo,sosai tana a farin ciki. "Yaushe zamu ganin baby?.. Murmushi yayi,kan ya k'alli agogo, shida da rabi,harda wasu y'an mintuna. "Yanzu kam dare kinga ya gabato... Gobe da safe kan ma an sallamota sai kije koh?.. Kai ta k'ada tana wani tunani... Jin ya kai hannu cikinshi yasa ta dan murmusa.. Gira ya daga mata,kamin yace "saura mu koh?... Murmushi tai mishi ta k'ada kai. "Mun kusa ai...k'wantar da hankalin ka sarkin son yara... Dariya sukai,kan yace "sosai ina son su kam...in naje yaron Garba kamar nace su bamu aro... Kai ta k'ada, "lalle a gaishe ka.. Ni kam nafi son mu shekara kan na haihu da... Murmushi yai yana kada kai kawai. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ "MashaAllah, ganshi kamar dan larabawa... Ta g'yara mishi hular kanshi... Dagowa tai cikin wasa tana"um um,su Ummi an iya haihuwa... Shiru tai ganin yadda Ummin ta 6ata rai. "Mey akai kuma ki ke wani 6ata rai ina magana?.. Baki ta ta6e,kan ta ja k'wanon namanta ta fara ci. A y'atsine tace "ya bazan bata rai ba?... Saboda t'sabar wulakanci tun jiya na haihu amma sai yau zaki wani zo kina nad'e taburmar kunya?... K'allonta take ba kiftawa, sam Ummi batta kunya.. Sai dai kawai ta basar. "Dadina dake Ummi baki bada uziri a koman ki.. Yanzu ina laifin kin haihu da magariba nazo da sassafen nan?... Baki ta ta6e kan ta had'iye naman bakinta. "Ki ce kinbi order mijinki dai Malama, amma bare nawa ne suka zo tun a jiyan?.. Karara tsoron mutumin yaci k'arfin ki k'wana biyu na fuskanta... Shiru tai dan bakin ciki, ba abinda ta t'sana irin a dinga cewa tana tsoron Ja'afar...K'wafa tai cikin ranta. Zuwan Aunty A'i ne yasa aka dawo mutunci kuma. Kullum tana gidan Ummi,duk dan gudun magana. Yau kam Ja'afar yace ta hakura gobe tunda aiki jibi kuma suna,yau masu g'yaran gida zasu zo. Ba tace toh ba,haka bata ce a'a ba. Sai dai duk ta sauya,tunaninta muddin yau take zuwa gidan Ummi,toh ba makawa sai sunce chaketa,hakan ya tabbata kenan ita mai tsoron Ja'afar ce. Tabbas lokaci yayi da zata nuna musu bata tsoron Ja'afar. Hakan yasa da k'warin g'wiwarta ta tashi ta bishi d'akin waje. Shiri yake yana son fita wajen ciciku cikun neman takaddun shi da ya kone. Yanayin da ya ganta ta dan kama kai yasan yau abin ya mot'so. Kawai sai ya kau da kai. Zama tai gefen gado tana k'allon shi ta gefe, "Haba Ya Ja'afar dan Allah... Yau daya kar kamin haka dan Allah, ka barni naje tunda an g'yara kitchen ga kuma d'aki muna dashi a waje bayan suna suyi aikin.... Ido kawai ya zuba mata,sai da ta kai Aya tukun yai magana. "Ke mey yau din zata miki in baki fita ba?.. Kullum fa tun haihuwar nan kina fita Salma,dan yau kad'ai nace ki hakura sai gobe shine ba zaki iya ba Salma? Fuska ta y'atsine, kan tace ita dai kawai ya barta ta fita toh. K'allonta yake,abu yai sauki yanzu tana son dawo da hali? "Son ranki za'a bi yanzu koh nawa Salma?... A gida na ban isa nace ga abinda za ai ba sai ace a'a?.. Meye haka kike son kawo wa kuma da ya wuce?.... Hawaye ta fara mishi,tabbas yau in bata fita ba,toh gobe fa sai dai ta toshe kunne. Haushi tai bala'in bashi,akan wannan shine harda kuka?.. Sam bai son abin da ya wuce a dawo dashi. Nan ta zaune mishi tana mishi kukan gardamar sai ya batta. Haka yanaji yana gani sai shi ya sauke ya barta yace ta shirya su je. Da murnarta ta shirya suka fita ya sauke ta. Sai dai shi sam baida walwala. Haka tai ta fita har ran suyar nama,washegari ma wai zata wanke gida,anan suka hau suka fad'o.. Ya ja ta ja,harda fad'in dama ance tsoronshi take ji. Ya rant'se da in har ta fita,toh zai maimaita mata abin ranar,wato ta fita a bakin aurenta. Tuni ta nut'su ta dawo hankalin ta. Tuni ya kashe bakin t'sanya,har ya fice ya barta tana kuka,harda dariyar mugunta... Ya k'wa gano lago ai. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 21_Ranar ta fita a Napep ta layin su Ja'afar taga wani kamar shi tare da wata, har zasu wuce ta gane Bintu ce,da sauri tace mai Napep ya t'saya. Sam a yadda suke ba kace ba masoya bane,dan sai wani sunne kai take kasa halamar kunya. Tuni zuciyarta ta hau tafasa,ba shiri tai wajen gadan-gadan,dai dai suyi sallama harda dago mishi hannu. Kan ta karasa har ya juyo itama ta tafi... Ganin yanayinta shima ya dan tsorata,amma sai ya maze. "A'a, har kin fito?.. Harara ta sakar mishi kan ta k'allo Bintun da har tai mata nisa. "Ban sani ba... Ashe dama zance ka fito shine kace na hau adaidata koh?.. Kuma da Bintu?.. Har kana wani yage mata baki... Hannu ya kai kan bakinshi halamar tai shiru yana duba layin, "Haba Salma,a titi fa muke,kiyi hakuri ba abinda ki ke zata bane ba... Harara ta kara sakar mishi,kan ta farga har ido ya ciko da hawaye. Tabbas yau ya tabo jaraba... Dan sarai yasan Bintu kam sonshi take,kuma Salma ta sani. Akan kishiya k'wa, yasan sai Salma taki ci taki sha. Tuni ya hau lallami harda rantse rantse kamin ta yarda bayan anje gida. Wataran yakan yi tunanin koh Salma na da Aljanu,in ta tashi sauya hali tafard daya ne,sai dai in ya bud'e mata wuta su shirya. ~~~~~~~~~~ "Shiru ake jinki makociya,koh dan ziyarar yamman nan an daina zuwar mana sai jefi-jefi, koh mutumin har yau yana nan da kullen?... Baki ta dan ta6e,kan ta bawa maman Ummi amsa. "Ai sai abinda yai gaba, yanzu tunda akai abinnan na farko abu kadan sai ya kafan sharad'i kan in na t'sallaka a bakin aurena, ina gudun rabuwar mu,yanzu ma minti goma ya ban na dawo. Baki Maman Ummin ta ta6e, "lalle kina da aiki in dai mazan nan ne, saf zasu mayarka marar y'anci in bakai ma tufkar hanci ba,harda lokaci? Tab aiki.. Ga gobe sunan _nurse_ din layin chan (Maman Nuwaira),ke koh barka baki je ba, ke kinsan za'a watsa karya kiyi kok'ari ya barki muje. Kai ta k'ada, "Ai dole,dan wallahi baza ai bani ba,ko bai bari ba naje koh minti ashirin ne a wat'sa warishan nan dani. Hannu Maman Ummi ta bata suka tafa harda shewar su,ana haka Ummi tai sallama,kan tunda ta shiga Jafar yace tana nan ta fito,wai sai had'a rai yake,shi yasa ta bar mishi gidan, nan ta daura kan na Maman Ummi, Zuwa chan Maman ummin tace "Kiyi kok'ari hudu ki biyo min zuwa 5 dawo. Da wannan suka baje har ta wuce ka'idar Ja'afar. *Washegari*. "Wai dan Allah Salma na tambaye ki zaki ban amsa? Y'atsine fuska tai kan tace "ina ji.. "Shin dad'i ki ke ji in kin t'saya muna musayarya magana dake?.. "Mey yasa in na ce ki bar abu sai dai nai son ranki,amma ni ban isa ba? "Ita maijegon ta ta6a tako kafarta cikin gidan nan da sunan tazo gunki?.. Ki ban amsa? Baki ta saka,kan tace "oho,kana nufin gyaiyar sod'i zani kenan?.. Tunda ga areni muje biki koh?.. Kai ya kada, "Ke ki ka kira kanki haka,ba Ja'afar ba,abu daya na sani,ko na fita ba jimawa zanyi ba, saboda in ma kin fita,toh kisan inda dare ya miki... "Mey ka ke nufi? Kana nufin yau ma zaka ce a bakin auren nawa Ja'afar?.. Da sauri ya kada kai, "K'warai,tunda abinki naga na yanzu har so yake yafi na da, in har kam kin fitan,toh kisani,kin fita *A BAKIN AURENKI*... Sai ki zabi wanda ya fi miki, aure? Koh gidan suna?... Kofar ya bugo mata yai waje tare da barinta baki sake. "Eh lalle yau zan nuna ma tabbas ba tsoron ka nake ba Ja'afar... Wannan kurin bakin wallahi bazai hanani fita sunan ba,daga yau kalmar nan ta *A BAKIN AURENKI* tabar bakinka. Daki tai tana balbalin masifa ita kadai kamar yana k'allonta. Kaya ta fito dasu tana duba wanda zata sa, _lace_ din sunan Ummi ta dakko wani karamin _swiss_ da aka sashi siyanshi dan dole. Sunan na manya ne, dan haka sai da kure adaka. Ba koh shakku ta fice, yau tun dazu taji gidan su Maman Ummi t'sit kamar ruwa ya shanye su,halamar mai gidan yana nan kenan,amma tunda ta fara jiyo hayaniya tasan yai waje. Gidan suna kam ya kayatu, sun samu abinda ake so tuni aka baje a faranti ana ci ana kora wa gulmar wata. Kan ta farga har 5 da yan mintina. Haka kawai taji gabanta na fad'uwa hankalinta yayi gida. Tashi tai ana fad'in ta t'saya k'ulli ya kare a k'ulla mata tana a bawa Maman Ummi. Sauri take ta zubawa, dan da y'ar tazara a t'sakanin su. Adu'ar ta daya,Allah sa Ja'afar bai dawo ganin koh ta fitan ba. Ta rasa dalilin da ya sa hankalinta ya tashi,bayan ita ta zabi hakan. Lekawar da zatai shine taci ka'ro da Ja'afar suka had'a ido. *WAIWAYE*... *************** ************** Haka yai ta juyi har kusan k'arfe biyu. Washegari haka ta tashi sukuku, ga fargabar Abba yau zai dawo,ga wani mugun mak'on Ja'afar da yake taso mata. Kai in ma ba wai bata kula bane gani take zazzabi ne a jikinta. "Salma... Dagowa tayi ganin mama a kofa,da mamaki fal fuska ta karaso ciki. "Wai har yau kukan nan ki ke Salma?.. Mey yaron nan yai miki ne haka?.. Hannu ta kai kan fuskrta,sam ba tasan tana kuka ba, da sauri ta goge tana k'ak'alo murmushin dole. "Mama ina k'wana.. Kai kawai ta kada mata. "Haba Salma,kar fa ki rako mata duniyar nan...kar ki zamo mace mai kulafucin D'a namiji duk k'wa wulakancin da ya mata man... Ashe ni ina chan jiya nai baccin farin ciki da aka rabu lafiya ba rabo bare ya kawo cikas a zawarci ashe ke kina nan kina kukan an rabu? Haba Salma, karan nan ne fa ki ke da dama ta biyu,tunda har ya sallame ki. "Maza goge hawayenki ki biyoni daki yanzu. Kai ta kada,a gaskiya ta fara mamakin irin kiyayyar dasu mama suke ma Ja'afar, wato har ma godiya ake ta rabu da alakakai?... Allah yaga tafi jin haushin kanta sama da haushin Ja'afar, in ma taji haushin shi toh bai wuce yadda ya k'ulle mata gida ya kuma tafi koh ajikinshi. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 22_"Toh wa ya jawo?... T'sam tai yayin da zuciya ta tambaye ta, "Ni ce... Tabbas ni najawo, amma ba laifi na bane. Kuka ta fashe dashi,tabbas anci k'arfinta,ta ko'ina an mata dabaibayi da huduba gur6atacciya. "Gashi na jawo wa kaina saki biyu ba tare da na samo kan ba(kan Ja'afar).. "Oh ni Salma.. Ina tunani na yake da har na aikata wannan wautar?.. Ina son da nake ikirarin ina ma Ja'afar?.. Ina ya je... "Salma... Mama ce ta kat'se mata tunanin gaskiya da kira. Hannu tasa ta share hawayen ta,ta daga kai tare da fitar da iska dan daidaita nut'suwar ta. "Na'am.. Ta amsa kan ta tashi tai waje. "Gani mama, Kan gado ta nuna mata kan tazo ta zauna. Ba musu ta karaso. Kafad'arta ta dafa kan ta numfasa, "Kina ji koh Salma? Kai ta daga mata. "Baban ki yau nasan zai dawo,tabbas ya rit'saki nasan zai cid'a ki ne a banza. "Yanzu abinda nake so kiyi shine,ki je gidan A'i,dan mijinta baya gari ya tafi sari,ki barni in na gama lalla6a shi sai ki dawo,dan karan nan kam sai dai ai wacce za ayi, amma aure kin gama... G'wara a chanja hannu,tunda wannan d'in ba fus, bare ass,sai dan banzan dacin rai ba koh gidan kai... Hawaye ne ya zubo mata,ba da ban suna matukar kama da Mama ba,da tayi shakkun akan haihuwar ta... Mama na da kamasho a ta6ar6arewar aurenta kashi 70 acikin dari... Tabbas uwa uwa ce, amma su kam tasu uwar sai g'yaran Allah.. "Au,au,kuka ki ke? Dan nace baida gidan kanshi?.. Koh shi ya siya ya gina da gumin ajin?.. Yarinya ki duba yadda ake harka,y'an uwanki na shiga ta alfarma amma ke kin zama y'ar k'allo.. Ki farka a bacci Salma,dan rayuwar nan ta zo mu fafata ce. Kai ta k'ada tana goge ido,sai ta mike tai hanyar waje, "Bari na shirya zuwa gidan Aunty A'in, naga 10 tayi. Kai Maman ta daga harda washe baki, "Yauwa,ko ke fa.. Maza aje a shirya,ga nan abincinki a kitchen. Kai ta k'ada kan tai waje, da kallo Maman ta bita, ba abinda y'arta ya gaza a gareta,wa ma zai ce ta ta6a aure in ta fito da ita gari?.. Dole kud'in da ba taci ba da yanzu taci gun Salma. *************** ************** A k'wance take kan _3sittern_ Aunty A'i,in banda ciwan kai ba abinda take, "Tashi ga maganin kisha... Kai ta dago,Aunty A'i rike da kofi da _paracetamol_. Bayan tasha ta g'yara zama,d'uk gidan bata jin da wanda bai ta6a kushe mata Ja'afar ba sai Abba da Aunty A'i. Hawaye ne ya zubo mata,kan kai duk'e tace "ban san mey Ya Ja'afar ya t'sarewa su Mama ba da sam basa kaunarshi... Yanzu ki duba Aunty A'i Mama yau tace murna take an sake ni.. Harda fad'in g'wara da bamu samu rabo ba... Kuka ne yaci k'arfinta,tuni ta hau yi ba kakkautawa. Taso wa Aunty A'in tayi zuwa kusa da ita ta hau lallashi,chan ta numfasa itama harda hawaye ta fara fad'in "Kinyi wauta Salma matuka,samun irin Ja'afar a yanzu wallahi sai kin tona,irin halin da kika dinga karta mishi duk na samu gun Abba,kinsan nima ba wai Mama nayi dani bane sosai,dan ban fiya shiga irin shirgin nan ba. "A gantali har gida sukutum ki ka kona mishi Salma.. Naji ance ya kuma shiga cikin y'an _missed call_..Bana tunanin har yau ya gama tattare takaddun da ya rasa kuma duk a dalilinki fa,amma dai dai da rana daya bai ta6a hanaki ci koh sha ba?.. Duk da baki san ta ina yake samu ba. "Maimakon ki zama mace ta gari mai k'wantar mishi da hankali har ya manta bakin cikin da yake ciki na rasa aikinshi,a'a sai ma kara hura mishi wutar masifa ki ke a gida. "Salma kina da ilimi fa,kinsan d'ukkan hukunci a game da matar da take sa6a umarnin mijinta, bare ke da kusan kullum cikin shi kike?.. Ina ki ka bar islamiyar taki Salma?.. Da har kika bari rudin su Ummi da chan wasu jahilan makotan suke hure miki k'unne,wanda in zaki titsiye su ba mai iya rashin mutuncin da ki ke Salma.. "Nayi imani zaman cikin gidan ki ya fiye miki alkairi sama da zaga makota yawan gulma da ki ke.. "Ya sanar ni shi sai a shafe wata nawa,baiga makotan naki na zirya gidan ki ba sai dai aiken bani taliya bani mai, shin sun fiki sanin ciwan kansu ne Salma? "K'wanaki haka har gida na samu yana fad'a kina fad'a, amma dana shiga nai miki fad'a, sai kika nunan wai maza sai da wuta.. "Kan kiyi aure Salma ni nayi da shekara hudu, ba zaki fad'an halin maza ba,amma a lokacin na biki da murmushi ne kawai. "Ki dube ni nan Salma... Dago tai ido jajir hawaye na zuba. "Wallahi tunda nake akan fita unguwa ban ta6a sa'inasa da Abban Aslam ba,kar kara in naja,ya ja,hakura nake na barshi,wani sa'in sai kiga har ya fita,amma sai ya dawo yace in shirya ya sauke ni,ina fara'a za'a gama komai ba bacin rai, duk wanda zai fad'a miki ana tank'wasa namiji ta fad'a da bala'i wallahi karya yake miki,sai dai ma kullum yai ta baud'e ga uwa uba sane mishi da ki ke. "Zuciya nason d'ukkan mai k'yautata mata Salma,sannan a kullum tana kara nisa ga wanda ke munana mata... Ki gane wannan, tunda dama taki,shine ya koma miki ta hagu, ki fita a bakin aurenki Salma, tun da kuruciyar ki wai har kin zama bazawarar k'arfi da yaji? Ranar da kanshi Ja'afar din yazo gidan nan,akan irin yadda ba k'ya jin maganarshi,nai mishi alkawarin zanje har gida na miki fad'a sai gashi Allah ya kawo wannan. Sosai tai mamakin Aunty A'i,da yau ta zauna fed'e mata biri har wut'siya.. Tai imani duk maganganunta ba wanda ba ita ke da laifi ba tabbas. Wata muguwar nadama ce ta sakko mata,kuka kam ba kama hannun yaro, har sai da taji ba dad'i. Bataki koh yanzu ta nemi gafarar Ja'afar ba kan ya maidata aurenshi,tai alkawarin d'auwama acikin dakinta har sai yace Salma fito. Aiya Salma, Ja'afar baya tataki,yanzu ta Bintu yake.. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 23_Zazzabi harda amai take,duk zatan Aunty A'i akan kukan da taki dainawa ne. Washegari ba zato ba t'sammani Aunty A'i ta t'sinkayi sallamar Abba a t'sakar gida. Lokacin dawowarta daga band'aki kenan ta gama zuba ma Salma ruwa a amai na tun jiya da yaki t'sayawa,sai dai tana jin Abba ne ta mike tare da yin waje da sauri. Hannu Aunty A'i ta d'aura aka,ganin zabga- zabgan bulalin da Abban ya shigo dasu gidan, fad'i yake "Ina take Aisha?.. Tuni idonta ya raina fata,fatan ta Salma taji ta buya. Cikin in'ina tace "Abba wa d'in?.. Hannu daya marar bulala ya nunota dashi, "Kinci gidan ku... "Bani hanya na wuce,yau mai rabani da Salma sai Allah a gidan nan.. Da k'arfi Aunty A'i tace ta gudu,hayaniyar ce ta fiddota a band'aki ta had'a uban zufa dan azabar amai, har bata danji sosai, lekawa tai ta labule jin an ambaci sunanta... Ido waje ta koma da baya tana neman ma6oya,tuni ta ware tai bayan kujera tana rufe baki da duk hannunta biyu jin Abba a parlourn. "Dan Allah Abba kai hakuri,wallahi bata da l... "Aisha,koh ki fito min da ita koh bulalinnan su kare a kanki... Ido Salma ta rint'se da sauri,kirjinta sai d'ukan tara tara yake. Sai dai mey? Kamshi turaren kayan Abba ne ta busu hancinta,take taji amai ya taho tai kokarin ta mat'se sai dai ta kasa,tuni k'ak'arin aman ya taho sai dai ciki ba komai. Bata zata ba sai jin magiyar Aunty A'i tai tana dan Allah yai hakuri... K'wak'waran mot'si batai ba taji saukar bulali tai ajiki ta ko'ina. Ihu take da iya guntun k'arfin daya rage mata tana Abba zan mutu, ina,kawai lafta mata yake,da Aunty A'i ta rike sai ya cika ya hau zuba mata wata. Makogaro ba ruwa,duk ya tafi a amai,tuni har muryarta ta dashe,sai k'ak'arin amai da take. Kamar an hullo mama sai ganinta sukai a kid'ime,ganin yadda yake jibgar Salman ta bala'in tsorata, da sauri tai waje dan kara kiran yayanshi Ganin Abba zai kisa,yasa da sauri Aunty A'i tai ma Salman rumfa tana yai hakuri cikin kuka,ganan Salma koh k'wakkaran mot'si batai,bai bi takanta ba ya hau zuba musu tare, "Abba ciki ne da ita,wallahi zai zube.... Chak ya t'saya da bulala a hannu sai zufa yake, yai dai dai da shigar Mama tai katari da zancen Aunty A'in. Bulala ya yarda yana haki,tamkar yasa kuka dan bakin ciki,tunda yake basshi da fadanshi amma bai ta6a sa hannu ya dakesu ba sai akan Salma,wannan shine karo na biyu gareta. So take tafi k'arfin kowa a ganin shi,toh shi bazata fi karfinshi ba. "Ba mai fin karfina a gidana ban maganin shi ba... Yau kin t'sira a dalilin zancen A'i,da na lahira ya fiki jin dad'i.. Duk da laifin nafi daura ma uwarku data zuba ido kuna abinda kuke so... "Mun shiga uku... Da sauri Maman tai kan Aunty A'i mai magana. Jijjiga salman take tana kira. "Salma!... Salma!!.. Mama bata mot'si wallahi... Tuni suka hau jijjigata Aunty A'i na kuka. "Shikenan Malam ka kashe min Y'a ka huta... Babu yadda banyi da kai ba akan kai hakuri kar kazo,kar kaje,ga nan irinta ka... "Ki rufe mana baki, koma meye ke kika jawo, ruwan k'anin Aslam ya gani a jarka da sauri kuma ya dakko wai su mat'sa agun,ido duk hawaye suka mat'sa. A hankali ya dagota tare da yayyafa mata, a hankali ta kawo numfashi sai dai ido a rufe. "K'unnen k'ashi gare ki ne Salma,shi yasa baza mu shirya ba sam sai kin g'yara hali. Kuka ta fara kad'an kadan lokacin da suke dagata, sosai ta lillisu,duk jiki ciwo. Wayar Aunty A'i,da Ja'afar suke magana wai yaji Abban su yace Mama ta bugo kan Abba zai kashe Salma... Cikin kuka tace "Kazo gidana suna nan. Duk ya kuma kid'ime, tabbas ba d'ukkan wasa yasan Abba yake ma Salma ba,tunda Aunty A'i take kuka. Garba ya kalla,"dan Allah kaini gidan Aisha yayar Salma. Da mamaki yake K'allonshi, "amma dai kasan yanzu _chairman_ zai zo yama signing koh?.. "In bazaka kaini ba na fita na hau abin hawa. Kafad'a ya daga, "a muje, ni meye nawa. Mijin Aunty A'in ya kira koh yana gidan,yace su shiga kawai,Abba ya sanarshi komai tun dazun. Abba ya fita lokacin da suka zo,mama ta tafi nemo abin hawa. Aunty A'in ce ta shiga dasu,ganin bulalin wajen duk sun kakkarye ji yai kamar yasa kuka,yanzu duk bulalin nan a jikin Salman sa ta kare? Jiki a sanyaye suka je parlourn,duk ta kudindina tana rawar sanyi,da sauri ya karasa gunta yana kira,tana jinshi ta kara rushewa da wani kukan. Hijabin ya yaye mata,yana ko'k'arin cicci6ota ya tuna da sakin dake t'sakanin su,sai ya zame hannu tare da zama. Bai san wani irin so yake ma Salma ba,wanda har yake rawar jiki akanta duk da abinda ta mishi, gashi har taja jiya ya bada kai gun Bintu bori ya hau. "Mey yasa Salma?.. Mey yasa ki ka zabar mana irin rayuwar nan?.. Gashi yanzu kin dasa min son kara aure koh na samu maslaha aciki... A zabure ta tashi,duk da yadda take jin jiki tana cije le6e dan azaba. "Mey kace Ya Ja'afar?.. Aure?.. Da sauri ya k'allo ta,sam bai tunanin zancen ba a ciki yai ba. Ganin bai bata amsa ba yasa ta yarda da abinda taji,hannu tasa duka biyu ta dafa kan ta zamo kasa tana cije baki,g'wiwa biyu ta durkusa duk tai kalar tausayi. "Ka rufamin asiri Ya Ja'afar dan Allah,wallahi, na rantse bazan kara ba..Dan Allah kar kamin kishiya.. Dan Allah, wallahi bana sonta.. Allah zan g'yara..nai alkawari,.. Ido ya rint'se, had'i da cije le6e,ba yau Salma ta fara mai magiya da rantsuwa kan ta d'aina ba,amma ba abinda ya sauya zani.. Yanzu komai ya kare musu,aure gareshi ya zama dole. By Feenat Ja'afar. Juma'@ Mubarak. 9/29/16, 9:07 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24-Kai ya kada tare da mikewa, "kiyi hakuri Salma.. A baya na baki d'ukkan wata dama taki kinyi watsi da ita.. K'arfi da yaji so ki ke ki mayarni wani iri,dame zanji Salma?.. Na fita waje na samo 6acin rai,sannan na shigo gida nan ma wani 6acin ran ne,maimakon a lallashe ni..A'a ni kullum ni nake lallashi. "Kiyi hakuri,Allah ya baki lafiya.. Garba ya k'allo yai mishi halamar su tafi. A hankali ta mike tana jin wata irin hajijiya na debarta. "Nasan ni na ja ma kaina komai Ya Jaafar... Ja yai ya t'saya, jin taci gaba yasa ya juyo. "Tabbas na chanchanci d'ukkan wani hukunci da zaka min in dai zaka yafe min.. Kasa tai da kai,tai matukar zama abin tausayi a gunshi,sai dai kawai ya kasa gane nadamar Salma a yau,dan ta saba, ga kafa sai ka'rkarwa take. "Amma dan Allah wa zaka aura?.. Ba dai Bintu ba?. A yadda ta t'sareshi da ido yasa ya kasa magana,sai ya kalli Garba,kafad'arshi ya daga mishi halamar ba ruwan shi. Sai da ta maimaita kan ya daga mata kai. Murmushi tai da yafi kuka ciwo,a hankali take neman juyawa wani kanta ya sara gami da ganin duhu. "Kar ki min fassara Salma,ba abinda ya had'ani da Bin... Luu ta fara halamun zata fad'i, cikin zafin nama yai taku daya ya taro ta. Gaba d'aya jikinta ya saki,ga wani irin zafi kamar garwashi. "Salma.. Jijjiga ta ya fara,da sauri Aunty A'i ta shigo,sai ga Mama na fad'in ta taimaka su sa Salman a Napep gashi ta nemo.. "Mey zan gani haka... Da sauri suka juya ganin Mama da tai turus ganin yadda ya mammakale Salman,ita k'wa k'allonshi kawai take hawaye nabin gefen idonta. Garba ke mishi da hannu kan ya saki Salman amma kamar yana zigashi,sai kara naneta yake. Gaida Maman sukai da girmamawa tai banza dasu. Sababi Mama zata fara Aunty A'i ta jata sukai waje. Garba ne ya tsayarshi ganin yana neman cicci6ar Salman. "Kasan dai yanzu ba a mat'sayin matarka Salma take ba,kar ka nemo mana magana dan Allah.. Harara ya sakar mishi,kan cikin fusata yace "na mayarta toh.. Koh da magana? Kai ya k'ada mishi, kan ya bud'e mishi labule, "Dan Allah kaimu asibiti... "Auntyn mu.. Aunty A'i ya k'wada ma kira, da sauri suka fito ita da Mama dake huci. "Asibiti zamu kaita, dan Allah Mama ki yi hakuri na kaita.. Harara ta sakar musu kamin tabi bayansu ta sallami mai Napep sai asibiti. Murna ta koma ciki,da d'ukkan hannu biyu mama ta dafe kai,jin rahoton likita kan tabbatar da cikin Salma,dan haushi ba tasan tai waje ba. Shikenan an 6ata mata shiri, ciki?.. Kai amma an sha da ita, sam ta zata fad'in A'in ne dan a bar Salma. "Mama kiyi hakuri zata samu lafiya,bari naje na siyo allurori mu dawo. Kala bata ce musu ba, asalima ji tai kamar ta rufeshi da duka koh ta huce. A gun Garba ya k'ar6i kud'i,basu juma da tafiya ba sai ga Ummi da Aunty A'i sun zo,tuni k'wa ta ware tana surfawa Ja'afar Ummi na tayata. Kai Aunty A'i ta k'ada, fatan ta a kullum Allah ya ganar dasu Mama alkairin Ja'afar, alkairin da batajin koh su wanda suka auri masu halin suna musu. "Mama Salma fa matar Ja'afar ce har yanzun,don musulunci ya mallaka mishi,matukar batai idda ba,bare da kunne na naji yace ya mayarta wallahi, dan Allah Mama ki sassauta, in har da mey lefi aciki toh fa Salma ce.. "Ke dama ina kika ga kishin kai?.. Ai guntunki ta tsotsa, shi yasa sam kusan halin ku daya... Aure kuwa in dai ni nai nakudar Salma toh ya kare ya gama.. Ba ruwana da wani ya mayarta,sakaryan yaro kawai,sam bai da zuciya wallahi. Ummi ce ta amshe tana k'wafa. "Ai wallahi dad'i yake ji dan yaga Abba na jibgarta,dama garin d'ukan yaja ya rasa cikin ai da shi ya jiyo... "Ummi mey yasa ke sam baki da mutunci ne?.. Baki Ummin ta turo, "Ja'afar fa ba sa'anki bane,in bazaki g'yara ba toh kar ki 6ata... Salma ita ta chanchanci komai ba Ja'afar ba,gashi taja yace aure zai kara... A zabure Mama ta jiyo, "Aure?.. Shine ki ke kuma fad'a min ya mayarta?.. Kai ta k'ada, "eh lalle Ja'afar, toh k'wa zama da kishiya ba dai y'ata ba, karan nan zamu banje da Malam wallahi akan maganar komen nan,sam naki jinin yaron nan wallahi.. "Ni kam Mama bana ganin aibun Ja'a.. "Kimin shiru,kar ki gani din,amma aure angama. ****************************** Yau k'wananta biyu aka sallame ta,fur Mama taki bawa Ja'afar fuska,daga ina wuni lafiya shikenan. Su Abban su Ja'afar harda y'an cikin gida sunzo sun jajanta abinda ya faru. Kowa ya bawa bangarenshi rashin gaskiya, take Baba yace ya mayarta. Kai duk'e yace ai tun ranar chan ya mayarta,nan ya ja mishi kunne kan sarar ki fita A BAKIN AURENKI. A gaban su Abba ya kara tasa zancen zai kara aure,cikin fusata Abbanshi yace "Ba mun gama maganar nan da kai tun jiya?.. Wane aure kuma bayan wannan da aka mayar? Kai yai kasa dashi yai shiru, murmushi Abban su Salma yayi,kamin yace "Kamin dai dai Ja'afar, fatana Allah yasa auren shi zai zaunar da Salma a dakinta ta rungumi ibada. Ja in ja sukai tai t'sakanin Abban Salma da Abban Ja'afar, dak'yar Abban Ja'afar ya yardewa Ja'afar kara aure. Ana watse wa koh gama jan mota basuyi ba Mama ta fara sababi,ita a fafur ba inda Salma zata,bata zauna da kishiya ba,saboda haka ba mai zama da ita a yaranta. Itade Salma bata um bata um- um,sai hawaye kadai ke zuba,ita kad'ai tasan ya zuciyarta take hautsina mata,ta faru ta kare,tunda har manya sun amshi magana. "Ja'afar? kishiya? Kuma da Bintu kawarta?.. Tab da matsala. By Feenat Ja'afar 9/29/16, 9:10 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24_Daaga sosai akai da Mama akan komawar Salma,sai da Abba ya bud'e mata uwata sosai kamin harda Yayanshi ta saki aka ta koma din. Ita kanta Salman yanzu ba kaunar komawar take ba sai ta mot'so mata ga laulayi. Ga Ja'afar tunda ya ji batun ciki ya kasa sukuni,kullum yana zaryar dubiya da leda. Shi dai bai mat'sa da sai ta dawo ba lokacin, dan g'yaran gida sosai yake wanda Ummanshi ta bashi ya zauna aciki. Har gida yau Abba yaje gun Abban sun kan lalle yau Jafar yazo ya dau Salma. Da dare k'wa ta koma dakinta. G'yaran nan gidan ya t'saya chak,sakamakon aikinshi da aka mayarshi aka bashi albashin da ya wuce shi,bai da mat'salar kud'i yanzu,auren shi kawai yasa a gaba. "Ina k'wana.. Cikin sanyin murya ta gaida shi kai duk'e, kai ya daga kamin yace "ya jiki?.. Shiru tai ba amsa. "Ki tashi ki zauna man.. Kai ta dago ta k'alleshi kamin ta kada mishi, "A'a magana nake son muyi da kai. Zama ya g'yara yana sauraranta. "Mey yasa ka ke son auren Bintu?.. Da ido ta kafeshi tana jiran amsa. Murmushi yai kan yai baya kad'an harda d'aura kafa daya kan daya. "Saboda tana so na ne Salma.. Kai ta kada, ''kaima kana sonta?.. A bazata tambayar tazo mishi,ga takafeshi da ido hawaye taro a idonta. "Ki gane Salma, ba wai.. "Eh koh A'a?.. Amma nake son ji kawai. Ba koh shakku yace mata "eh.. Amma.. Hannu ta daga mishi tana hawaye, "Barni haka dan Allah,amma kasan Bintu k'awata ce da koh?.. Ya zaka min haka? Kai ya kada harda dariya, "A sani na banta6a ganin Bintu a gidan ki ba,asalima... Sallamar Aunty A'i ce ta kat'se mishi maganarshi,sai ya tashi dan dan bud'e mata kofar,da kallo ta bishi tana mamakin kalamanshi,sai kawai ta k'ada kai ta mike tana goge ido. "Bissmillah mana Auntyn mu.. Yana gaba ta biyoshi a baya, sosai suke dasawa da Aisha,dan tasan abinda take sosai,shi yasa baya 6oye mata komai. Bayan sun gaisa ya mike yana zai fita, kai kawai ta k'ada mishi,sai Aunty A'i ce tai mishi a dawo lafiya. Zama Aunty A'i ta g'yara tana ma Salman k'allon tuhuma. "Ashe Salma baki fara g'yara ba har yanzun?.. Da rashin fahimta ta k'allo ta tana hawaye, "Fita fa yayi jiyan nan dawowarki amma har kin fara nuna mishi baki sauya ba. "Aunty A'i ba abinda na mishi fa Allah.. Katseta tai da fad'in "Amma zai fita babu koh a dawo lafiya?.. Haba Salma,nan ki ka dinga rantsuwar kin shiryu, koh har kin leka makotar ne yau d'akko sabon darasi?.. Kuka ta sa mata tana girgiza kai, "Haba Aunty A'i,k'awata fa zai aura fa,taya bazanji zafinshi ba?.. Da mamaki tace "wacce kawar taki? Cikin kuka tace "Bintu,dalibar shi ce a Day school fa. Ita dai ta hanga bata gano wace Bintu bace a k'awayen,tasan sarai k'awayen Salma basu fi biyu ba wanda tasan su. "Wace Bintu kuma cikin k'awayen naki? Amma basan ta ba koh?.. Kai ta daga mata, "islamiya mukai tare fa.. "Mtsww, t'saki Aunty A'in tai tana k'auda kai, "har wata kawar islamiya K'awa ce?, bana jin ko hanyar gidan ku ta ta6a zuwa balle ta zama kawarki, koh ta halarci bikin ki?.. Kai ta kada mata tana goge hawaye. Cikin lallami ta fara lallashinta. "Kar fa ki bari tun kamin ta shigo taci galaba akanki Salma, yanzu ba lokacin t'sayawa kishi bane a gunki, lokacin g'yaran kuranki na baya ne Salma... Ki d'auka baki ma ta6a sanin wata Bintu ba rayuwa,dan ba gaminki da ita sam. "Ki kuma fidda zancen auren nan a ranki,dan koma meye ke ce sila Salma. Nasiha tai ta mata tana kuka har ta gamsu da bayaninta. Ta bata shawara masu k'yau, ta kuma d'auka. Da ya dawo ya ga chanji,sannan bata kara mishi maganar Bintu ba. Yau satin ta daya da dawo wa,amma banda Maman Abba ba wanda ya leko mata har Maman Ummin, Ga sai wani kama mata kai Ja'afar din yake bare tace zata leka,abu daya ta sani,shine ta daina zuwa gidan kowa sai in ta kama. Washegari har kofa ta rako shi zai fita tace zata leka gidan Maman Ummi.. Yana fita yace mata sai ta dawo kawai. Da k'allo ta bishi,sai ta ga kamar gat'se ya mata,dan haka ta koma ciki tai k'wanciyarta. Mukullin gidan da ake g'yara zai fitar musu dashi sai ya dawo. A k'wance ya sameta ido rufe a parlour,sai yai jim,ganin bata fita ba har ya dawo. "Har kin dawo ne?.. Kai ta girgiza mishi,sai yai d'aki yana tunaninta, haka ta saba mishi kan gaba ta fand'are mishi,shi dai yasan yai alkawarin mud'in ta tambaye shi fita ya d'aina hana ta,yasan duniya makaranta,da sannu zata gane abinda yake gujar mata. Koh da zai fita sai ya kara nanata mata kan taje kawai. Bai jima da fita ba ta fito,tana dan jin hayaniyar su kasa-kasa. Har zatai Sallama sai ta ja ta t'saya jin wata gulmar da suke. "Ai yanzu ya zamarta mai gadinshi, tunda ta dawo ba inda taje tana d'aka,koh duk sururin zai kara auren ne?.. Tana jin Maman Ummi tace "oho mata,ba ita areni muje biki ba,mijina baya fad'a.. Muryar Maman Abba tajiyo tana fad'in ''ni tausayi ma take bani wallahi, ranar chan dana shiga duk ta rame tai baki,kana yaronka da kai an ma saki 2.... Baya tai cikin sanda danjin wani na shirin fitowa. Gida ta koma ta cire hijab tai dabar a kujera, tun yaushe haka take faruwa da ita?.. Ashe ita k'allon mara wayo suke mata acikinsu?.. Kai ta daga sama, lalle ta gane mey Ja'afar yake nufi da mutunci yake nemar mata.. Yau ta gane ashe in an yi gulmar wani da kai yau gobe da kai za'a kafa ai taka. "Allah na gode maka daka sa na ji na kuma gani. Tabbas Ya Ja'afar babban gata yai mata. Toh a ina ma suka samu labarin za ai mata kishiya?..har dare tana neman amsa. Ranar har kukan bakin ciki tai na taraiyarta dasu Maman Ummi. Tuni ta tattare kowa ta wat'sar shi,duk da ba duka aka taru aka zama daya ba. Ranar Maman Waleeda da suke kira uwar tsoron miji ita ta zo mata harda nasiha har gida,matar da koh gidanta sai tai fita ashirin bata leka ba,kuma makociya ta kusa,har misali tai mata da Maman Ummi. "A kaf unguwar nan bana tunanin da matar da take cikin takura irin na Maman Ummi Salma, ke shaida ce,in kinji gidan yai shiru ba koh tarin yaro kasan uban na gida. Sannan in zai shekara ba taje ko'ina ba shine dai dai a wajenshi,duk fita in zatai satar hanya take tasan in ya fita da yamma sai dare,amma a gun kuri tafi kowa iya dadin magana,da ina cikin su,daga baya na gane taraiyyata baza tai dasu ba,sai na zabi zaman gidana ya fiye min alkairi sama da yawan gulma. "Ka'rkara in abu ya faru in leka a tsatssaye in dawo, dan Allah ki iya kafarki Salma,dan zasu kai ki su baro ne kawai. Kai ta k'ada mata, "Na gode Maman Waleeda,Allah bar zumunci,kuma InshaAllah naji bayanin ki,duk da mun kusa tashi a unguwar ma duka InshaAllah. Anan ta sanarta za ai mata kishiya,k'warai ta jajanta mata kan ta kara da y'an shawarwari,tun daga ranar mutunci da Maman Waleeda suke,kusan duk yamma tana turo mata su Waleeda taya fira,har lokacin tashinsu yazo. ***************************** Cikinta yana da wata biyar lokacin auren Ja'afar saura sati. Sam bazaka zata Salma bace, dan tamkar bai dameta ba haka tai a auren. Har ranar Ja'afar yana fad'in wai ta daina sonshi gaba daya,koh kishi bata yi zai kara aure,murmushi kawai ta masa,dan tsaf ta kula da rawar kan da yake k'wana biyu. "Ba k'ya shirye-shiyen komai gashi lokaci ya taho fa... Tamkar ya choka mata abu makogwaro taji wani iri,kawai sai ta sa mishi ido tana k'allo. Tabbas rawar kan Ja'afar karuwa take akan auran nan,banda haka wani irin tambaya ce wannan?... Shikam tunani yake yadda Salman ta g'yaru har kullum,a ganinahi halin ko'in kula da yake nuna mata ne akan fita. "In da hali zan fita kar6o wasu kayana unguwar Ummi. Kafad'a ya daga mata,kan yace "sai kin dawo... Yai waje. Baki sake ta bishi,tun bayan dawowarta ta kasa gane inda Ja'afar ya dosa,abu yake mata tamkar ya kosa da zaman ta a gidan. Gashi tun kamin amarya ta tare har ya sallamata,wai ko'ina nan gaba in zata kawai taje,dan yanzu bai son 6acin rana irinta da. Toh mey yake nufi? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:11 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci. Har yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu. Kuka take yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan ba mai chazan hawan jini. Kai ta dago tana mishi k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a wa matarka baka so na?.. Ni nace ina son ka koh?.. A haka za ai zaman lafiyan?.. "Ke kinga bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?.. Da sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan kaina.. "Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita... Waje yayi zuwa dakin Salman. Kai Bintu ta k'ada, "ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada mata mari tukuicin sharri. Ita kam tanajin bud'e kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance ido. "Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a gidan nan?.. Yaushe nace miki Bintu ce tai min tallar kanta na aura?.. Harara ta sakar mishi da k'allon kar ka rainan hankali. "Ka nad'e taburmar kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?.. Baki ya saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla mishi a gun y'ar uwarta ashe?.. Bai da tace wa, kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba kai ka fad'i ba... "Idan kuma habaici da iyayi kake neman matarka ta dinga min dan ka huce haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana sa kafar wando daya da kowa a gidan nan wallahi.. Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki ta barshi t'saye baki sake. Titi ya fice ko ya samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa. Tun daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya mata magana ita y'ar dika take,daga shi har amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi. Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai... Ta fada tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su aciki... Chak! Taja ta t'saya rike da labule a hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar su. "Sai yau Aunty Ladi zaki zo min? Har nayi fushi ai.. Baki sake Salma take k'allonsu,tana k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma Bintun kuskus tai baya da sauri. Ido ta rint'se tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu ta gane inda Bintu ta samo duk wasu _information_ na zaman aure nata ba agun Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar, har rantsuwa yai mata amma taki yadda. Karshe har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya. Zama tai tana jiyo shewarsu a dakin Bintun. Har kullum bazata daina nadama akan taraiyarta dasu Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta. Har hawayen bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina sa6awa mijinta ko da taji haushin shi. T'sakar gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya. Ganinta a t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau inda-inda, "dama kina ciki?.. Sannun ku da gida.. Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita. Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai za tai rakiya waje ya bata izinin fita. Bokiti ta zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja t'saki ta shige band'aki. "A toh na zata koh rafka mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan wannan da gani zatai kishin hauka... Dariya suka sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki tafiya. Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin saukar ruwa sukai akansu har Bintun. Bokitin ta d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture suka fita waje da gudu. Tana haki ta leko kofar gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi, InshaAllah kema dubinki ta kusa cika. "Ke kuma yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai Allah, yau zaki ga karyar iskanci. Gida ta koma tana hakin daga ruwa bucket guda da tsohon ciki. A t'sakar gidan ta zauna tana maida numfashi a hankali, ta jima da zama kamin taji tafiyar Bintu cikin sand'a, kofar ta zubawa ido tana harara, kai ta leko dashi dan ganin koh Salman bata nan sai suka had'a ido. "Wallahi baki isa ki ce zaki hanani shiga ba, in gaske ne ki bari na shigo na shirya in fad'an ki ke nema dani ba hauka ba. Murmushi tai daga inda take, "Lalle kinyi kuskure in kina zatan zan iya had'a jiki da karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's "Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?.. Gidan ki ne da har zaki kafa dokar wa zai shiga ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace "eh wallahi, da da halin duka ma sai na miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada, kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi, "Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira.. Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara.. Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:14 AM - Queen Safiyyert馃憫: *漏 Feenat Ja'afar*. 25_Yau amarya ta taro gidan Ja'afar,suna chan d'aki yan d'anna kirjin Salma. Tai kuka yau harta gode Allah,tukun daga baya taje ta d'au wanka. Tabbas ba'a iya dake wa kishi,koya sai ya tona ka,dak'yar ta samu ta saita kanta kamin y'an kawo amarya suzo kawo amana. Kowa ya wat'se, daga ita sai amarya, kowa tana dakinta. Karadin Garba ta kiyo a parlourn ta,tuni taji gabanta ya sara, tabbas tasan tare suke da ango. A hankali ta yaye labule tana k'allon su har suka shiga dakin amarya had'i da parlour mai k'allon nata. Zama tai ido tuni ya ciko da k'walla, sai tai ko'k'arin had'iye wa. Tana jin Garba yana bazai shiga ba yaje tai tanadin ta6aryar duka, tana suka sa dariya harda tafawa. Kwafa tayi,wato ga mahaukaciya sabon kamu. Tana jin rufe kofar gidan tai sauri ta k'wanta ta rufe ido. Da sallama ya shigo parlourn, ba kowa sai kamshin turaren uwar gida y'ar Borno jikar Shuwa. Ko'ina yaji sabon abu,kamar itace amaryar, labule da kujeru purple da baki, su Mama anga ba sarki sai Allah,kawai sai aka fito da tsohuwar ajiya,baba ya cika aka sai mata kayan parlour,ragowar nata na da suka siyar,gado k'wa tace bazata siyawa wani gardi ba,harda kukan Salma. Sai ma kuma gashi ashe yana da niya,gado barawan Italian da katifa yai mata a kud'in da Ummanshi ta turo mai daga Zaria. D'akin ya shiga,nan ma shiru ba amsa,tai rigingine kamar mai bacci. K'allonta ya t'saya yana yi kamin ya ajiye ledar hannunshi,sosai cikin ya kara fito mishi da k'yan Salma warai. Tai k'yau cikin attamfa ruwan purple da pink,tasha k'walliya sosai gun Ummi,idon nan yasha (mascara/eyeliner). Da komai Salman sa ta fi Bintu sau dubu agunshi,sai dai ta nuna mata hasken fata. Hannu ya kai kan cikin yana shafawa a hankali, tana jinshi yana yan surutanshi ma cikin. Ajiyar zuciya ta yi,sai ya k'allo ta,a tunaninshi baccinta ne yai nisa. A tashi yai yana k'allonta,kan a hankali ya duk'o tare da nufin kai bak'inshi nata,tana jin hucinshi sai ta juyar da kai da sauri. Murmushi yayi kamin ya shafo kanta da suka sha yiriyirin kitso. "Asbha ta ga Salma.. Ki yafeni kinji... Bargon kusa da kafarta yaja ya lilli6eta,kamin ya kashe wutar dakin yai waje. Ido ta bude tana nanata maganar shi a zuciyarta, mey yake nufi da ki yafeni?.. Saboda ya tafka miki t'siya mana.. Cewar wata zuciyar, le6e ta cije,yau gata a gidan Ya Ja'afar,akan gadon su,amma ba shi ciki,yau zasu fara raba matashin kafadar Ja'afar da wata chan.. Tana son Ja'afar, sai ma yanzu ta gano t'sant'sar son da take mishi,ji take kamar ta had'iyi zuciya ta mutu dan kishin mijinta, tuni tasau wani dan marayan kuka a hankali,kamar tace Ja'afar dawo. **** Ita k'wa amarya tuni ta mike ta fara zarya a d'aki, dan a idonta ya shiga bangaren Salma,tuni ta fara cika tana bat'sewa. Tana ko'k'arin fito wa a parlourn ya shigo,da sauri ta koma ciki har tana tuntu6e,duk ba tasan ya ganta ba. Ba laifi,tazo da tarikice dayawa,sam sai t'sarin na Salma yafi burgeshi,dan shi bai son tarkace a gida da sunan k'walliya,ga wani kala blue da pink na kayan labule da kujeru,sam bai mishi ba. "Ki fito da sallaya parlour.. Kawai sai yai waje dan yin alwala a band'aki. Assalatun farko ta farka,cike da mafarkin Ja'afar wai yana ta mata fara'a. Kasa tashi tai,tabbas da gaske yanzu tasan bakinshi kamar gonar audiga dan fara'a, tunda yai k'wanan d'akin amarya. Hakan ne yasa ko da gari ya waye taje kitchen ta d'aura abin kari,dan tun asuba taga text din Aunty A'i kan ta k'auda kishi tai musu kalacin da safe,dan Allah.. Wannan Kalmar ce tasa ta shiga dan dole. T'saye take tana juye abincin a flaks,ba abinda ta tsana irin hada kitchen da band'aki da kishiya,harar bangaren kayan jeren amarya tai tana gunguni ciki-ciki,bata nufa ba taji shafo wuyanta ta baya. A zabure ta juya dan ganin waye. Murmushi yake mata kanar dai a mafarkinta,da sauri ta d'auke kai daga K'allonshi zuwa gefe. "Kamshi duk ya karad'e gidan nan K'anwata.. Hannunta yake neman kamowa ta mat'sa tana "An tashi lafiya.. K'allonta yake daga sama har kasa,tana sanye da rigar banci _sky blue_ nai filawa purple, sai ta d'aura zani da dank'wali akai, tai mishi k'yau sosai,ga dan kurcicin cikin ya fito yai d'as. "Ya gajiyar jiya?.. Na shiga kinyi bacci ban son tashinki. Yawu ta had'iya tare da fad'in "ummm. Fur taki k'allon fuskarshi balle ta fassara mata bakin ciki. Dan da ganin yadda ya fara mata zagwadin nan ta faru ta kare. "Ga abincin ku,zan wuce.. Hannu yakai zai karbi natan tayi saurin janye wa ta wuce,kai ya k'ada bayan ya dawo daga k'allonta. Dakin amarya ya koma,tana kudindine cikin bargo, sai baccinta take narka abinta. Parlour ya dawo ya zauna,Salma nuna mishi halin ko in kula take tun satin biki, sam bata koh kishinshi,sabgar gabanta kawai take. K'wafa yai ya kada kai,dan ba karamin haushi hakan yake bashi ba. Motsinta yaji a t'sakar gida,ta window ya dago yana k'allonta zata wuce band'aki da bokiti da kwandon wanka,watoh daga shi har amaryar shi basu isheta ma kallo ba?.. Dan wai koh hanyar d'akin bata kalla ba,k'wafa yai kan yai waje gun band'akin ya t'saya kamar maigadinta. Har ta gama wanka yana t'saye,tana bud'e kofa sai ganin mutum tai a t'saye ya bake hanya,kai ta k'auda da nufin ta wuce ya riko bokitin,yaja ta taja,kawai sai ta sau mishi,k'wandon sabulun yake neman k'ar6a tai baya dashi. "Wanka zanyi man Salma.. Wani k'allon ta watsa mishi kan ta had'e rai, "Bana _sharing_ din soso. Baki sake yake k'allonta, cikin fusata yace "da da wanne muke yi?.. Kanta gefe tace "toh yanzu na sake t'sari... A tunzure yace "Wai Salma meye haka?.. Bana.. "Kai Dear J,ga soso nan kai wankan. Juyawa sukai gun mai magana, Bintu ce daga ita sai y'ar yaloluwar rigar bacci ba koh zani balle dank'wali. T'saki Salma ta ja,kan tace ''Malam ban waje na wuce,tuni ya kara kuluwa, shi take ma tsakin?.. Yai mata k'yau,kawai sai ya dungurar mata da bokitinta ya shige band'aki,da sauri Bintu tai kitchen ta d'akko mishi nata,koh ta kansu bata kara bi ba ta zari bokitin ta kara mai,a ranta tana "karamar y'ar iska kawai. Sam Salma taki dad'i, dan fur taki bawa kowa fuska a gidan,dan taga da mugun falli amaryar ta shigo mata. Har girkin amarya ya kare ya dawo ga Salma amma ba sauki. Zata gaidashi tai komai,amma ba magana duguwa, sai ma haushin sa dake kara ziyartar ta. Tuni ya kai kara gun Aunty A'i,wai Salma taki sake masa fuska. A ranar tai mata waya ta kare mata tass,tuni ta hau kuka,wai ai dan ita bata kishiya ne,bazata gane lamarin ba,ga kusan kullum Bintu na chakalarta tana kaucewa. Shiru Aunty A'in tayi,dole wannan ba zancen waya bane, "Ki bari zan zo koh zuwa gobe ne. Ranar girkin Bintu ne,yau tun safe take fallin fararo a t'sakar gida,sai ya6a mata haibaici take ita kad'ai kamar sabon kamu. Salman tana zaune kan taburma a kofar ta tana yanke farce. Harara ta sakar mata,kan taja t'saki, "Wawiya kawai.. Shewa Bintun tayi harda guda. "Kece babbar wawiya wacce zaman gidanta ke mintsininta.. Ehee, naji komai ai,saki daya ya rage miki duk a dalilin gantali gardi. A masife ta tashi,sai dai nan da nan ta k'auda bacin rai dan ya6a ma Bintu magana dai-dai ita. "Ahaiyee,, naji,tunda banyi k'wantai a layi bare ina bi ina tallan kaina agun d'a namiji ba ehee, ke har kin isa ki ce kin san komai?. tunda dey ni ba matar tushe bace ba... Dan tuni akasan da matar tushe dai bata k'warjini... Karya uwar bin maza kawai... "Eh naji ki ce komai,igiya uku ce a kaina kinga na fiki matsayi a... "Ke... Bana son shashancin banza wallahi.. Juyawa sukai danjin mai gidan yai shigar bazata. "Ihu har titi mutanan unguwa ana jinku sai kace wasu karnika?... Harara Salma ta sau mishi da t'sabar tuhuma a k'allonta. "A ni ba karya bace, dan har gidan mu ka samo ni..chan ka nemi karya tun wuri.. Jiki ta kad'e tai dakinta ta barshi baki a sake. Ita kam Bintu lukwas tayi,tabbas Ja'afar kadai zai iya fad'a ma Salma cewa ita tace tana sonshi,da kuka tai d'aki dan bakin ciki. Itama haka take gun Salman,sosai taji zafin maganar Bintu,tasan kuma babu mai fad'a mata sai Ja'afar. Toh fa Ja'afar, ka shiga t'sakiya. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:16 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci. Har yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu. Kuka take yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan ba mai chazan hawan jini. Kai ta dago tana mishi k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a wa matarka baka so na?.. Ni nace ina son ka koh?.. A haka za ai zaman lafiyan?.. "Ke kinga bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?.. Da sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan kaina.. "Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita... Waje yayi zuwa dakin Salman. Kai Bintu ta k'ada, "ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada mata mari tukuicin sharri. Ita kam tanajin bud'e kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance ido. "Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a gidan nan?.. Yaushe nace miki Bintu ce tai min tallar kanta na aura?.. Harara ta sakar mishi da k'allon kar ka rainan hankali. "Ka nad'e taburmar kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?.. Baki ya saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla mishi a gun y'ar uwarta ashe?.. Bai da tace wa, kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba kai ka fad'i ba... "Idan kuma habaici da iyayi kake neman matarka ta dinga min dan ka huce haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana sa kafar wando daya da kowa a gidan nan wallahi.. Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki ta barshi t'saye baki sake. Titi ya fice ko ya samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa. Tun daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya mata magana ita y'ar dika take,daga shi har amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi. Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai... Ta fada tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su aciki... Chak! Taja ta t'saya rike da labule a hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar su. "Sai yau Aunty Ladi zaki zo min? Har nayi fushi ai.. Baki sake Salma take k'allonsu,tana k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma Bintun kuskus tai baya da sauri. Ido ta rint'se tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu ta gane inda Bintu ta samo duk wasu _information_ na zaman aure nata ba agun Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar, har rantsuwa yai mata amma taki yadda. Karshe har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya. Zama tai tana jiyo shewarsu a dakin Bintun. Har kullum bazata daina nadama akan taraiyarta dasu Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta. Har hawayen bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina sa6awa mijinta ko da taji haushin shi. T'sakar gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya. Ganinta a t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau inda-inda, "dama kina ciki?.. Sannun ku da gida.. Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita. Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai za tai rakiya waje ya bata izinin fita. Bokiti ta zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja t'saki ta shige band'aki. "A toh na zata koh rafka mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan wannan da gani zatai kishin hauka... Dariya suka sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki tafiya. Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin saukar ruwa sukai akansu har Bintun. Bokitin ta d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture suka fita waje da gudu. Tana haki ta leko kofar gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi, InshaAllah kema dubinki ta kusa cika. "Ke kuma yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai Allah, yau zaki ga karyar iskanci. Gida ta koma tana hakin daga ruwa bucket guda da tsohon ciki. A t'sakar gidan ta zauna tana maida numfashi a hankali, ta jima da zama kamin taji tafiyar Bintu cikin sand'a, kofar ta zubawa ido tana harara, kai ta leko dashi dan ganin koh Salman bata nan sai suka had'a ido. "Wallahi baki isa ki ce zaki hanani shiga ba, in gaske ne ki bari na shigo na shirya in fad'an ki ke nema dani ba hauka ba. Murmushi tai daga inda take, "Lalle kinyi kuskure in kina zatan zan iya had'a jiki da karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's "Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?.. Gidan ki ne da har zaki kafa dokar wa zai shiga ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace "eh wallahi, da da halin duka ma sai na miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada, kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi, "Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira.. Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara.. Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 27_Tun kan Napep ta t'saya ta mika mishi kud'in, da sauri ta shige gidan Aunty A'i fuska duk hawaye. "Toh kiyi min bayani man ba kuka ba Malama,mey aka mi... Wayan Aunty A'in ne ya hau ruri Aslam ya miko mata. A takaice ta k'alli Salman sai tai waje dan amsar wayar. Tana ji tana waya da Abban Aslam kan zata shigo da Ja'afar. "Dan Allah karki shigo dashi,wallahi ban san ganinshi,gwara in na huce da kaina zan koma. Baki sake take k'allonta hijab a hannu, "Ok,kina nufin yaji kika yi kenan?.. Shiru tai mata tana ci gaba da goge hawayenta. Bata kara bi ta kanta ba tai waje. Ba'a jima suka shigo tare,kai ta kautar gefe, tana jan hanci,ido yayi luhu-luhu dan kuka. Abinda ya faru ya t'sarawa Aunty A'in, tuni ganin duk ita ya d'aurawa lefi yasa ta hau musu bori ba shiri. Ido kawai Aunty A'i ta sa mata. "Auntyn mu kin gani koh? A gabanki ma kenan,wallahi na rasa rikicin Salma sam yanzu,abu kadan yanzu zata hau balbalin bala'i sai dai ni na bar mata. "Yanzu da banzo ba Allah kad'ai yasan mey zatai ma y'ar mutane,k'alli a halin da take fa,amma Salma taki k'wantar da hankalinta ai zaman lafiya.. "Ni fa kar ma ka zata kishi nake da kai koh kuma waccan amaryar taka,sam ba haka bane,ni mud'in za'a tada min hankali toh lalle na kowa zai tashi... _period_. Aunty A'i ya k'allo halamar tasa baki. Tambayarta take mey ya had'a su?.. Amma fur taki magana a gaban shi,har aka gama sulhu yace ta taso su koma tace sai dare. Da kai Aunty A'in tai mishi kawai kan ya k'yaleta. Ba musu ya tashi kan sai ya zo,yana fita ta mike tai kitchen. Tana cin abinci Aunty A'i na mata fad'a, kan ta d'aina fada Ja'afar na fada,dan ta fuskanci Bintu ta iya bariki. Nan ta fad'a mata ainashin abinda ya faru,harda irin habaici da sharrin da Bintun ke mata kullum. Baki ta ta6e. "Ni fa Aunty A'i Bintu bata gabana, abu daya na sani na tsani a gabana yana biye mata tana mishi abinda taga dama.. Yana konan rai ne,shi yasa yake rasa kaina. Murmushi tai mata, "Lalle Salma kina so Bintu ta kai ki ta baro, kin kuma yi saken da kika bari kishiya har ta gano lagon ki,dole yai ta ganin bakin ki ke kadai,dan ke kadai ki ke iya daga jijiyoyin wuya agabanshi akanta,in sharri ma ta miki ki barta da Allah kawai,shi zai isar miki,kar ki manta igiya daya tai saura a t'sakanin ku da Ja'afar, kuma kince ta sani,toh wallahi ki sani ingiza mai kantu ruwa kawai zata miki,so take tai ta tunzuro ki har ki tafka kuskuren da za ai mai dika, kinga taci galaba kenan. "Gaba koh abinsu suke kina d'auke kanki a kansu, sannan abu in kinga zai ja ki fad'i wata magana musamman kan Ja'afar kiyi shiru kar ki tanka dan Allah Salma. "Ja'afar na sonki,kiyi amfani da hakan sai ki ci galaba kan Bintu.. Har ta gama mata fada tana ta nazarin abin,toh Allah yasa ta iya k'auda kan. Ita kwa Bintu murna fal rai,dan tana lekensu ta k'auran zauren, fatan ta Allah yasa yadda ya figi machine din nan in yaje kawai ya dankara mata saki. Shi yasa tun kan ya dawo taje ta t'sant'sar wanka ta hau kananan kaya, duk da ba ita ke dashi ba. Ita a ganinta an sau Salma an gama,.. K'warai ta gode da shawarar su Aunty Ladi ta waya da ta yau,tabbas da BARIKI kadai zata mallaki Ja'afar ba boka ba Malam. Sai dai har dare ba Ja'afar ba dalilin sa,kawai sai ta zata bai gama hucewa bane,tasan mutumin ak'wai saurin zuciya. Dirin machine dinshi taji,da sauri ta kara fesa turare ta haska touch light tai zauren da zummar taro shi yasha Bariki. Turus taja ta t'saya gabanta na fad'uwa, ganin ya mike yana fad'in ma Salma "Dafani man toh,ban san ki fad'i ne garin sauka. Da kamar kar ta kulashi,amma ganin hasken fitilar Bintu yasa ta hau shagwaba. "Toh ni kam tsoron sauka fa nake tunda cikin nan yai girma,in zaka iya ka sauke ni toh... Ta karasa da kalar tausayi. "Toh toh,amma ki kokarta,ki rikeni gam, koh ki bari na fara sauka... Kofar Bintu ta saka da sauri ta koma ciki dan bakin ciki. Tana jiyo su a t'sakar gida Salman na fad'in "Wash.. Allah Ya Ja'afar kafata rikewa take fa.. Tuni gogan ya hau rikicewa abinda aka jima ba'a mishi ba yau yake gani,bar zuciya da abinda take so. "T'saya na d'auke ki toh ai kina ma kok'ari.. Tana jiyo Salman na fad'in "kai Ya Ja'afar, anya zaka iya kuwa?.. Nayi nauyi fa yanzu. A zabure ta mike ta tana lekensu ta window ta cika tai ham. Dariya suke k'yak'yatawa kan yace"bari ki ga,nawa ki ke.. Da sauri ta sau labulen ganin ya k'wa daga Salman ya dauke kamar y'ar tsana suna dariya. Har d'aki ya dire ta suna nishad'i kamar ba su bane dazu an bar Bintu da kukan d'aki. Sai yanzu ya tuna ai koh sallama basuyi ba suka shigo. Murmushi tai mishi lokacin da yace bari yaje ya dawo. K'wafa tai tana kada kai, "kowa ya iya BARIKIN ai,in na baje tawa sai kin ji jiki Bintu. Yau da sauri-sauri yai ma Bintun sallama yana ta zumudin sun dinke da ta k'arfen. Kuka wiwi tai tayi bayan fitarshi. A gaban mudubi ya tarar ta tana g'yara gashi,kowa farin ciki fal ranshi,ta baya ya sakalo cikin yana shafawa harda sakar ajiyar zuciya. Murmushi tai mishi,tare da shafo siririn sajen shi ta bayan, sai ya k'wanto da kanshi wuyanta suna ma juna murmushi ta jikin mudubin. Yaushe rabon su kasance haka shi da Salman sa?.. Ga y'ar shagwa6ar nan yau yana shanta,duk sai ta mantarshi komai. A hankali ya rad'a mata a kunne "I love you... Murmushi tai kan ta juyo tana lumlumshe ido jin dad'in kalmar, lafewa tai jikinshi tana fad'in ''Me too.. Sosai yasha mamakin Salman shi yau,komai yi mishi take cikin kauna da kulawa, kamar farkon aurensu kamin komai ya wargaje. Hakan yasa washegari kowa fuskar nan kamar gonar audiga dan fara'a, amma banda Bintu Lol. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 28_Tun daga ranar aka dinke da Salma da Ja'afar d'inta, sam ta d'aina sanya da abinta, shima abin nema ya samu,wai ! Matar falke ta haifi jaki. Kan kace k'wabo,tuni tsohuwar soyayya ta dawo d'anya,sai ya zama kamar kamar yanzu ma tafi yawa. A cikin wata guda duk sun sauya,takanas zaice su fito aje siyayyar kayan baby,fur Bintu take kin zuwa,sai suyi tafiyarsu a kafa suna tadin su,sai jiran EDD. Kwana biyu Bintu an tsiri zaman d'aki,sai ta kule ka rasa abinda take aciki ita daya. Ranar tana bacci da safe wajen k'arfe goma taji kwkwazon maigidan yana tayi ba kakkautawa. Tashi tai ta fito parlour. "Na fita ban karya ba,yanzu ma na dawo ashe baki tashi ba, bayan tun asubar fari kika fara wannan charting din danaki jini a rayuwa,na hana kin ki hanuwa,toh ina gaf da fasa wayarnan a gidan nan Allah. Baki ta ta6e tare da tashi a hankali tayi d'aki dan fita wanka. Tana kallo ta fito wai yai hakuri ta daura mishi indomie,koh ta kanta bai bi ba yai waje yana huci. Kamar jira take,da dan gudunta ta koma d'aki ta dane Facebook cikin group din su na KI G'YARA DA KANKI. Kusan duk anyi katari masu kishiya sun da yawa, nan zatai ta samun shawarwari mey kyau da marar k'yau,dak'yar ta tashi ta d'aura jalof ta koma. "Wato sai yanzu nake hangen maganar ka abokina, dan yanzu abinda Bintu take har yafi mai na gantali ciwo,in ta hau wannan Facebook din nata,sam bata ji bata gani,abinci a kone, in ma ta samu d'aurawa kenan,sallah a kure,bacci sai biyun dare,da asuba ta d'aura a inda ta tsaya,ga in ka shigo kaji tana dariya ita kad'ai, Allah zaka zata Bintu sabon kamu ce... Dariya ya fara mishi harda k'yak'yatawa,har ya fara k'uluwa,yasan haka zata biyo baya, amma shi yanzu shawara yake nema ya zai da sabon halin Bintu?. "In ka gama kai magana sai ka bani shawarar abin da zanyi. Dak'yar Garba ya takaita dariyar ya fara magana. "A lokacin chan baya ai bakaji zance na ba,dake idon ka a rufe yake,na sanarka baka san mey wani irin hali zaka jajubo ba,kace kai fa gaji ka gani sai Bintu.. "Malam ni shawara zaka bani,in babu zanyi gida. Dariya ya cigaba dayi,kawai sai ya zuciya yai gaba. "Ma had'u in ka gama,dan hankalina yai kan Salmatee. "Wash Allah bayana,Bintu!...Bintu!!.. Tamkar ba kowa a gidan ka ke ji sai karar fankar sama dake kadawa a parlourn wacce bata hana gumi t'satsafo mata ba. Rarrafo wa tai zuwa kofa,iya karfinta ta kwalawa Bintun kira,ji take tamkar zata mutu dan azabar ciwo,tuni ta fara kuka tana ambatan Allah,tasan koh zata mutu Bintu bazata taimake ta ba,fatan ta Allah ya hankad'o mata Ja'afar koh wani ya ceceta. "Wayyo Ya Ja'afar, Innalillahi.. Bintu.. A razane ya karaso cikin gidan dan jin ta ambaci Bintu cikin kuka. "Subhanallah.. Salma.. Ina Bintun toh?.. Da sauri ta dago,tana ganinshi ta kara fashewa da kuka tana cije le6e. gaba daya ya tallafota yana aikin sannu sannu. Waya ya ciro dan neman Garba ya kaisu asibiti, tana ta ringing shiru.. Da rigarshi ya goge mata gomin dake tsatsafo mata, "Bari na ga koh bacci waccan take na taso ta. Hannunshi ta rike gam tana girgiza mai kai, Kanta ya shafa, "ki d'aure Salma,bari na kirata kinji. Dak'yar ta cika shi yai dakin Bintun, dan ji take yana tafiya zata mutu. Bata parlourn, sai ya bankad'a daki,tana mike a kan gado taja rabin bargo tana dariya kasa-kasa tana charting hankalinta yai gaba. A sukwane yai kanta,bai wata-wata ya sinketa da mari mai rai da lafiya,a gigice ta mike tare da dafe kunci,wayar ya warce, "Lalle haukar nan taki karuwa take Bintu,yanzu dama kina cikin gidan nan Salma take ta kakarin kiranki kamar zata mutu?.. "Toh ki biyoni yanzun nan waje, tana turo baki ta sakko kan gadon tana gunguni. Nishi take ta dafe d'ukkan hannunta a kasa, sannu yake mata da tausayawa,da harara Bintu ta bita da jin haushin akanta an mare ta. "Ka kira min Iya Shatu dan Allah Ya Ja'afar kar na mutu.. Bintu ya kallo dake maka musu harara, "Kizo ki kamamin ita na kira Iya Shatun, kamar bata so ta matso kusa,yana fita ta mat'sa tana jan tsuka,"aikin banza,dan kina wata shegiyar nakudarki akan hakan kika ja aka mare ni, wallahi za... "Eh dan Allah kazo yanzu mukaita asibiti.. Shiru tai jin Ja'afar na kokarin shigowa tare da matsawa gun Salman da sauri zata ta6ata tana sannu. A hankali ta janye daga hannun Bintun tai dan ciki kad'an tana nishi, da sauri ya karaso dakin yana mata sannu. Nishi take iya karfinta sukaji sallamar Iya shatu,tana dubata tace ai haihuwa ce tazo gadan-gadan, ya basu waje, ya siyo reza da sauran abin bukata. Gam hannunta na cikin nashi,ji yake tana cikawa in ya tafi zata mutu. Kanta ya tallafo yana ta d'aure, iya shatu sai k'allon ikon Allah take. "Kai hakuri Jafaru,zata haihu lafiya dan ina jin kan D'a, yanzu bazata ji komai naka ba sai adu'a. Kai ya kada harda guntun hawayenshi yai waje,yana fita Bintu ta d'aura a bayanshi. Iya shatu tsuhuwar ingozoma ce mai ritaya, da guntun hand gulf din zuwa awunta ta karbi haihuwar Salman. Allah ya taimake tazo mata da sauki inji Iyan,sai shigowa yai shi da Garba yaji ihun jariri,baki wangale zai dakin iya shatu ta fito k'ar6ar reza. Ummanshi ya fara mawa albishir sai Aunty A'i,tuni ya fesa cikin gidan su,da ance mey ta samu? Sai yace bai gani ba. Har aka kintsa komai basu kara ganin keyar Bintu ba,sai da zasu asibiti ta fito,shi kam baiya ma ta ita. Suna fita su Aunty A'i suka zo da Ummi,lokacin Bintun na t'sakar gida tana yankar farce,ita dey Iya sai mamakin karfin hali irin na Bintu take. Sallama suke ta manna musu bajon hauka,tuni Ummi taja dogon t'saki, taki jinin Bintu a rayuwa. "Banza y'ar bakin ciki kawai,toh sai ki had'iyi zuciya ki mutu ai.. Hannu Aunty A'i ta daga mata halamar tai shiru,ita k'wa da harara tabi su har suka shige. Sun dawo an duba suna lafiya ita da babyn ta,Ja'afar baki har kusan k'unne dan murna,yana makale da yarshi. "Um,Baban baby ba koh dan karar nan ma ta manyan yayu.. Kai ya sosa yana ma Aunty A'in murmushi, ba dan yaso ba ya mika mata ita. Kan kace mey gida har ya cike da dangi yan barka da yan unguwa. Sai dare ta samu tasa hakarkarinta dan hutu. K'allon babyn take mey kama da Abbanta, gashi kadai da dan _beauty points_ (dimples) tai gadonta. Murmushi tayi tana kai hannu kan kumatun babyn, Allah mai halitta. Murmushi yake musu yayin da ya shigo d'akin, sai ta daga kai ta k'alleshi, kai ta girgiza tana dan murmushi. Sallama ta uku yana musu kenan yana dawo wa,ta rasa wani irin kulafuci yake musu musamman babyn. Zama yayi yana shafo sumar babyn da farin ciki. "Oh ni kam,koh zaka je da ita in tai kuka sai ka kawo ta. Murmushi yayi yana kai baki kan dimple din babyn yana kissing. "Ba kinki barina na k'wana anan ba?.. Da kalar tausayi yace "yau dai daya naji dumin y'ata kinji? Sai ya marairaice fuska. Dariya ta dan mishi,kan tai magana ta jiyo Babah mai zamar mata tana ya fito zata zo ta k'wanta,taga sallamar bata karewa. Dariya suka sa kamin ya tashi yai waje. "Maza ki rika biye mishi ki debo ma kanki magana da kazamin goyo ai. Da rashin fahimta ta k'allota tana neman karin bayani. ***** ***** Yau suna,baby taci sunan Mama tun ran huduba amma ya 6oye mata. Sosai yau daya Ja'afar ya biya mama,harda mishi waya tana kwarara mishi godiya ba iyaka. Maijego tai ras abinta da Baby Miemien ta,sun fito sunyi k'yau sosai. By Feenat Ja'afar. Ai hakuri da wannan dan zani gidan Suna Salma.. Zuwa yamma in na dawo zakujini Lol.. 9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 29_Suna ya wat'se kalau,maijego tai goshi,ak'wati guda Mama ta mata na suna sai na baba,ga Umman Ja'afar nata daban da tazo suna,chan gidan su Ja'afar su ma sun mata karamci,sai son barka. Wankansu suke cikin g'yara na musamman da Mama ta zage yi ma y'arta, albarkacin Miemie mama ta sakko sosai. Shirya Miemie take tare da taimakon Ja'afar din suna ta nishad'in su yau za ai yawan arba'in. Ta chakare sosai kamar yau ne sunan ita da Miemie. Baya ta juya mishi yana goya mata ita, "D'aure ta dakyau,dan kinga machine zamu hau.. Kai ta kad'a tana murmushi, Sai da ya zaga ko'ina yaga yayi kan ya bata majanyi tana mishi dariya, "A'a toh in baki iya ba ni sai na goya abata kawai... Dariya tai kan tace "Da kwa kabar abin fad'i agari kuwa. Jakar ya d'au mata ta d'au mukulli sukai waje,shima yasha sabuwar shadda abinshi. Bintu na t'sakar gida tana d'anne-d'anne a wayar da dak'yar ya bata. Da harara ta bisu harda dan t'saki a hankali. "Toh mu zamu fita sarauniyar charting.. Sai kisa mana mukulli a gida dan gudun kar a dirko kina sana'ar taki koh.. Tuni ta kara k'uluwa kuwa,ita dai an mayarta borar karfi da yaji a cikin gida. Hannu Salman ta dago mata halamar sai sun dawo,da harara ta bisu har sukai waje. "Jishi kamar wani dan daudu rike da jakar mata. K'wafa tai tana tashi t'saye, "Ba dai kin fara fita ba?.. K'wanan nan zaki yabawa Aya zakinta wallahi. ** K'wana biyu yau tayi tana fita yawan arba'in, yau ne na uku,yau kuma aka tafka t'siya da maigidan,dan fur yace ba inda zata je. "Bazaki k'waso ma yarinya rana ba fa,kiyi hakuri kawai. Iya wuya Salma ta kawo dan takaici, tayi magiyar yaki kuma,kawai sai ta raya mata tunda dama taki bari ta koma hagu. "Amma gaskiya baka min daidai ba Abban Miemie in har ka hanani fita yau. "A ka'ida sati ake fita yawan arba'in fa,amma ni na yarda zanyi ukun shine har na gama shiri amma kace bazani ba... Gaskiya da sake. Gefe tai da kai tana kunkuni,tuni ta kular dashi shi zuciya kusa. "Toh ban hanaki ba kije d'in, amma ki ajiye min y'ata ki tafi ke kad'ai. Baki sake take k'allonshi,ganin yadda ya fidda waya yasha kunu ya barta. A zuciyarta tace "Eh lalle,da gani abin Ya Ja'afar yazo da wulakanci... "Kasan dai ba yadda za ai na tafi na bar Miemie a gida,dan Allah in wasa ka ke ka bari,dan kam nasa rai da fita yau.. A tunzure ya mike da niyar magana cikin masifa,sai yai shiru yana k'allonta. "Kiyi toh gaban kanki kawai.. Sai yai waje da zummar barin gidan ma dan haushi. Sai dai mey?.. T'saye yayi yana binta da k'allo galala, ganin yadda ta fara kame-kame dan ya kamata tana musu la6e ta window. "Ke kuma lafiya kike abu kamar marar gaskiya?.. Dakewa tayi tai ganin kamar bai ramfota ba. "Dama zuwa nayi ina son na leka nan na dawo ne... "Ba mai fita yau acikin gidan nan in dai ni ne mijin, wacce ban isa ba ta fita nagani.. A fusace ya fice yabar gidan,duk sai ta Salma tafi zafi. Ita kam Bintu dariya tasa harda shewa, "Yau karya ta kare,sai a za6a zaman gidan miji koh fita yawan gantali gard'i... Tana jiyota tai banza da ita tana hawayen bakin ciki. Waya ta d'auka ta kira Aunty A'i kan abinda Ya Ja'afar ya mata. "Salma kiyi biyayyar aurenki, dan Allah kiyi hakuri da fitar kawai. "K'wana biyu ai yayi ma,tunda kin zaga ko'ina ai har gidan su... "Aunty A'i ban fa wuni a gida ba kullum a ziyara muke wuni. "Ai duk fita kina zuwa,dan Allah kar ki dawo muku da hannun k'yauta baya man,kuna cikin zamanku abin sha'awa. Baki tai ta bata sai da ta tabbatar mata da ta hakura kamin sukai sallama. Haka tanaji tana gani ta hakura da fitar tai zamanta a d'aki. Koh abincin rana kin zuwa yai yaci a gidan sai gidan Garba yaje. Kawai zuciya ke raya mishi Salma ta fita,bazai so yaje gida yaga tabbas ta fitan ba,kawai sai yai zamanshi har yamma tukun ya koma gida. Dakin Bintu ya nufa har yanzu baida walwala sai ya tabbatar da Salma bata fita ba,yasan Bintu kat ce,bata t'sallaka doka akan fita,in yace A'a, toh ta hakura. Sannu da zuwa tai mishi tana fara'a, a ranshi yana aiyana da Salma ce yasan sai ta cika tai fa kan ta mishi sannu da zuwa duk akan ya hanata unguwa,amma kullum y'ar uwarta ko ajikinta. "Yau bayan fita ta Salma ta fita?.. Kai zata girgiza, sai tai saurin kwa6ar kanta, dole yadda tasa taga bakin ciki har yau itama ta gani. "Eh,bata jima da dawo wa ba ai,baka sani bane?.. Hannu ya daga mata,cike da jin haushi yace "ya isa ni,tambaya na miki kawai. Waje yayi tana binshi da g'walo, yana yin nisa ta tuntsire da dariyar mugunta. Kamin cikin sand'a tai waje jin ya zata kaya. Ba koh sallama ya shiga parlourn, ganan takalmin a gefen kofa wanda ta fitar zata sa dazu. Tana zaune tana _feeding_ din Miemie ya shigo yana binta da kallo,da fara'arta tai mishi sannu da zuwa. Kekam yayi yana k'allonta ba koh kiftawa, tabbas Salma ta fita,dan mud'in bata fita ba bazata tare shi da wannan fara'ar ba haka,yasan kayarshi. "Wato kin fita hankalinki ya kwanta koh?.. Ban isa ba ashe har yau halinki yana nan baki sauya ba koh Salma?.. Baki sake take K'allonshi da tsananin mamaki,sai d'aure ta yake da jijiyoyinta. Cikin nut'suwa tace "Ni fa ba inda naje tun fitar ka,dan Allah ka d'aina tun.. Malama ki amshi laifi kawai,kinsan nafi t'sanar musu sama da komai, koh kina nufin Bintu karya zata miki?. K'allon mamaki take mishi,a hankali ta maimaita "Bintu".. Yaki ma bari tai mishi bayani sai zazzaga mata yake kan bata maidashi abakin komai ba. Kawai sai ta sau mishi kuka,tama rasa abin fad'i,wai Bintu ce ta fad'a mishi,wato ita ba abin yarda bace sai kishiyarta indai kan fita ne. "Haka ki ke ai,da kukan rashin gaskiya Salma..sam bana son ki dawo mana da hannun agogo baya,ina ta murna komai ya wuce ashe albarkar ciki ne yasa ki zaman dole. Ganin kukanta na karuwa yasa ya fice ya koma d'akin Bintu. Har da bawa kura ajiyar nama,wai duk randa Salma ta fita dan Allah karta 6oye mishi. Tun daga ranar ya sauya mata,sam in ya shigo sai dai ya d'au ya'rshi ya fice,itama daga gaisuwa shikenan ta gama,dan a ganinta wulakanci ne wannan babba. Ga wani fi'ilin mutunci da Bintu ta koya da kissa,kullum faram faram take mata,harda gaisuwa in antashi. Ta d'au Miemie ta goya a bayanta in Baban ya d'akko ta. Ba karamin dad'i kwa Ja'afar din yake ji ba,dan yana karrama mai son Miemien shi,ita kam Salma nata ido,sai ta dukufa gun kai kukanta ga Allah. Dan tabbas tasan tai saken da har mijinta yai mata mummunan tambari. Bintu kuwa kullum rokon ta Allah duk wani sharrin da take nemanta dashi Allah ya mayar mata kanta. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/2, 2:29 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 30_Sai ya huce kamar sati ana mutunci da ta tambayi fita unguwa zai kicin-kicin,yace tai son ranta,haka zata hakura tanaji tana gani,in ya dawo kuma tasha fad'an da batasan laifi ba. Kawai Allah ya d'aura mata wani irin hakuri,daga Ja'afar din har Bintun ido tasa musu kawai. A haka har Miemie tai wata hudu Salma na zaman hakuri, musamman ga saurin fushin Ja'afar gareta,ga tai alkawarin daina kai kara gun kowa sai gurin Allah. Ana haka Maman Abba ta haihu. Ganin yau y'an mutuncin na kanshi yana zaune ya shagala da yiwa Miemie wasa tana wage mishi baki tana dariya. Da fara'arta ta zauna kusa dasu tana k'allonsu. "Abban Miemie... K'allota yayi tare fad'in yana jinta,cigaba yayi da wasan su. "Inda hali dan Allah zani barkar Maman Abba yau kwananta hud'u da haihu banje ba. Kai ya kad'a, "wace Maman Abba?.. Da zumudin zai batta ta sanarshi makociyarta ta unguwar su ta da. Abinda yake ya t'sagaita yana k'allonta ba koh kiftawa. Tuni ya zata an rufe babin y'an tsohowar unguwar su a gidan,ashe har yanzu tana makale dasu. Bazai manta dasu ba,dan sune ummul aba'isin wargaza gidanshi. Kai ya girgiza mata, "Kiyi hakuri ba halin zuwa.. Baki ta sake tana K'allonshi, a gaskiya bazata zuba ido tai ta zaman gida na y'anci ba,da takura gaskiya. Amma sai ta bishi da lallami. "Dan Allah ya Ja'afar ka barni naje,nima dana haihu fa sau biyu tazo min har suna uku,kaga ba dad'i ace ni koh sau d'aya banje ba barka ba sai suna. "Sunan ma ki fidda a ranki,dan inda mu'amular dana fi tsana,toh mu'amular ki da y'an unguwar chan ne,kin gane ai?. Kasa tai da kai,sosai take d'aure irin halin da Ya Ja'afar ya tsiro mata,yanzu da ta kara tambaya zai ce tai gaban kanta,hakan yasa tai shiru. Shi kuma yadda yaga batai gardama ba yasa yai tunanin zancen bai shige ta ba ne. Miemie ya ajiye kusa da ita ya bar mata d'akin. A hankali ta zame ta kwanta,sai ga hawaye ya zubo mata. Zaman gidan nan ya fara isar ta,hakurinta ya fara karewa. Tana ji yai ma Bintu sallama ya fice,kawai sai ta sau kuka a hankali marar sauti. Wato a dake ka a hanaka kuka?. **** Tun bayan fitarshi bayan ta gama kukanta Miemie ta fara,kukan har ya wuce kima, komai tayi taki shiru,kawai sai ta goyata tasa hijab akai suka fita t'sakar gida dan sanyin magriba. Bintun na t'sakar gida tana saita abin fad'i kan Ja'afar ya dawo tambayar Salma koh ta fita,dan komai a k'unnenta ya wakana. Jijjiga ta take tana yawo daga t'sakar gida zuwa zaure da ita,tasan Miemie ba mai rigima bace, tabbas da abinda ke damunta yau,yawan kukan ji take kamar itama tasa kukan koh taji sa'ida. Dak'yar ta samu tai shiru,sai ajiyar zuciya take halamar tai bacci. Buta ta d'auka ta shiga band'aki kenan sai gashi kamar an hulloshi gidan,fatanshi yau ya rit'sata garin satar fita. Bintu ya kalla wacce ke murmushin ganinshi,sai taunar cingam take tana kas-kas,kai da ganinta da yanayinta kaga na mai shirin kulla wani sharrin. "Sannu da zuwa.. Kai ya daga mata, kamar kullum zai tambayi Salman sai yaji bud'e band'aki. A fusace ya kallo Bintu, "bayan fita ta Salma ta fita?.. Ki fad'an t'sakani da Allah. Kwai tayi kan ta fasa tare da yin kas dashi, "Eh ta fita,mey ya faru? Yanzun bud'e dakinta ta shiga band'aki ka shigo. Gadan-gadan Salma tayi kanta da butar data cika zatai alwala anjima,kansu farga ta rot'sa mata aka tana huci,bai isa ba ta rufeta da duka baji ba gani,fad'i take "Sharrin naki ya wuce bayan idona yanzu a gaban idona ma yi.. Mari ya d'auketa dashi shima yana fad'in ta sake ta. A fusace tace bazata saka ba,ita kam tamkar wawiya ta bari Salman na jibgarta,ganin da gaske take yasa da sauri ya finciko Bintun tare da kara mata wani marin. Kunci ta rike tana K'allonshi, "ki sani na gaji da halinki a gidan nan, karan nan zan d'au mummunan mataki akanki wall... "Ka sallame ni in ka gaji dani Ja'afar.. Dan ni tuni na gaji da zaman gidan ka, ka sallame ni ka huta toh.. "Haka ki ka ce?.. A fusace tace "eh haka nace.. Tuni shedan ya shiga cikin zuciyar kowa,musamman Ja'afar da ya rufe ido tamkar bashi ba. "Ki je gida sai na neme ki toh... Cikin kuka tace ''Ban isa zuwa musu ba sheda ba,dole ka bani sheda.. Ba tare da jin komai ba mugu(shedan) yasa ya rufe ido. "Kije na sake ki toh.. Chak! Taji kukan ya t'saya sai na Miemie data tashi dan hayaniya. Baki sake take k'allonshi fuska wanke da hawaye. "Ja'afar ka sakeni kace fa?.. Muryarta na ka'rkarwa ta tambaya. Da sauri ya bud'e ido ya dawo hankalinshi kanta. K'allon-k'allo suke ma juna cikin rashin sanin abin fad'a, musamman Ja'afar dashi ya furta. Ido ta rufe a hankali, sai ga hawayen da ya makale sun zubo. A hankali ta bud'e idon ta k'alli Bintu. "Allah ya biya ki da dai-dai abinda ki kamin Bintu.. Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai dawo gun maishi.. Jiki a sanyaye ta juya gun Ja'afar. "Shikenan abin nema ya same mu Ja'afar.. Aure ya kare a t'sakanin mu..igiya uku ka rusheta Ja'afar.. Ka rushe su.. Hannu tasa ta share idonta. "Ba ka da bukatar na t'saya maka bayani yanzu kam,dan ka zuba katanga a t'sakanin mu. Cikin nut'suwa tai hanyar waje ba tare da ta koh waiwayi d'aki ba. Da k'allo ya bita, ilahirin jikinshi ka'rkarwa yake,ya kasa tattara kalma daya da zai ambata, har Salma ta 6ace wa ganinshi. 'By Feenat Ja'afar. [8/2, 10:40 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 31_"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un.. Allahumma Ajurni fi Musibati,wakhluf li khayran minha... "Salma ki ce min ba gaskiya ki ke fad'a ba Salma?.. Dan Allah ki ce wasa ki ke.. Murmushi take,wanda da zatai kukan zai fi mata alkairi, amma ta kasa,tun zuwanta gidan Aunty A'i ido ya kafe,tunani ya t'saya.. Dabara ta ka re,sai kallo da ido da murmushi da yafi kuka ciwo. Waya Aunty A'in ta d'auka dan kiran Ja'afar, tayuwu koh shi ya mata bayanin da zata gamsu tunda Salma ta zama kurma. "Ja'afar.. "Bashi bane.. Tsam tayi dan tasan Bintu ce ta d'auka. Da karfin hali ta tambayi in yana kusa ta bashi man, t'saki tai mata kamin ta kashewar. Kasa tai da wayar tana mai tabbatar da kalaman Salma na aure babu,ya ka re. A hankali ta sakko ta t'suguna gaban Salman tare da dafa kafafunta. "Salma kimin magana ba shiru ba dan Allah.. A dunkule kika bani, dan Allah kiyi magana, shin da gaske ya sake ki cikon na ukun?.. K'allon Aunty A'in take cikin ido,tabbas wannan kalmar ita ta 6acewa tunaninta. Kan ta ankara ta sau mata wiwi,baji ba gani. "Bintu ce... Wallahi itace.. Ban mishi komai ba..ya raba aurenmu.. Allah banyi komai ba karan nan Aunty A'i,ki yarda dani dan Allah, koh su Abba baza su yarda ba... Kamar karatun yara haka take had'a kalaman cikin kuka. Jiki a sanyaye Aunty A'in ta tashi tazo kusa da ita,sosai ta gane sambatu take,cike da tausayin y'ar uwartata ta rungumo ta, ta abu daya take gane gaskiyar Salma tun a yarinta, shine fad'in abin da batai ba cikin kuka. "Na yarda Salma,na yarda dake karan nan.. Ki bar kukan haka, Allahu yasa shi yafi zama muku alkairi. Ita dai kukanta take. Ina Ja'afar ya gano abinda Aunty A'i ta sani game da rayuwar Salma, da bai bawa CID na fitar ta ba, da ya fuskanci ta sauya tun sa'ilin da in yace ta fita take kuka,da ba ayi hakan ba. ******************* "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'una... Ja'afar mai ya kai ka wannan yanke d'anyen hukuncin kan ku?.. Mey ya kai ka?.. Abinda ya faru yake sanar mishi,gaba daya ya rasa abin yi. "Shin ka tambayi ta fitan koh bata fitan ba?.. Koh har yanzu kai baka hango hankalin Salma ba ne.. Kai ya k'ada mishi "Ba wannan ne karon farko ba,ni nasan Salma fiye da zaton ka.. "Ka kuma yarda da Bintu fiye da yarda ka bawa Salma yarda koh ka ke nufi?.. Murmushi yayi na takaici, "Ja'afar bakasan sharri irin na mata bane.. Da baka ba Bintu amanar aurenka sukutum ba Allah. Tayu ka tafka babban kuskure na fahimtar Salma karan nan.. Amma ka yi bincike, shine t'sarin Shari'a.. Ni na shiga gida. Da kallo yabi bayan Garban, duk maganar shi gaskiya ce,kuma ba daya daga ci da ya aiwatar kamin komai. Yau daya yaga fushin Garba karara kwance a fuska,tabbas haushin shi yake ji shima,kamar yadda shima yake jin haushin kanshi da kanshi. Jiki ba kwari ya tada machine yai gida. Dole ya tit'siye Bintu ta sanarshi gaskiya. Bata d'aki,ga nan wayarshi da ya manta da tata akan gado halamar tana sana'ar tata ta charting. A garin ya d'auki tashi ya danno screen na Bintun, haske ya baiyana halamar tana ma kan charting din tai wani waje. Kwanciya yayi da bayanshi jiki duk a sanyaye,bazai iya bawa wannan ranar suna ba. Ido ya kura ma wayar Bintun kirar _Techno_, zai so yau yaga mey ke debe hankalin ta zuwa Facebook. *Bintu U*. _"ke an saki shegiyar fa,ki tayani murna zan sakata in wataya_.. *Shining star*: _"Kai matar nan baki da dama,a bani satar amsa dan yanzu na dawo makarantarki_.. Da azama ya mike zaune dan ganin charting din. *Binta U* _"Hhhhh,tuggu dai kamar kullum nayi,sai dai na yau mai zafi ne,dan jiya an bani sa'a har gida, take ina fad'in ta fita ya d'anna mata saki,baiwar Allah harda dan guntun wa'azin ta ta min hhhhh_.. *Shining star* _"ina ma zan iya irin wannan sharrin naki dana huta, sai dai tawa tasan takan duniya,ina mata take dawo min da abu na_.. *BINTU U* _"ba gari daya muke ba,da wallahi taci karya,ni zan baki maganin y'ar banza_... "Ya Allah... Kai shafo cikin ranar jiki hawaye na zuba, da sauri ya d'anna _previous chat_ Sai gata kamar an jehota da buta a hannu tana zare idano na munafukai. Sam bataji koh dirin machine dinshi ba,sai arbawa tai da takalmanshi. Da d'ukkan hannu biyu ya dafe kanshi yana hawaye,mey zai ma Bintu ya huce da bala'in da ta jawo mishi?.. A hankali kalaman Salma ya dawo mishi, _"Allah ya biyaki da dai-dai abinda ki kamin Bintu..Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai dawo gun maishi_... Gashi tun kan a kwana ya dawo ma Bintu bata shirya ba... "Ka dawo..yaushe ka shigo..ban banji shigowar ka ba.. Da in'ina take maganar, ganin yadda hawaye ke diga a kafafunshi ga kuma wayarta a hannunshi tasan yau karya ta kare. Ido ya goge kamin cikin nut'suwa ya ajiye wayar kan gado ya k'allota. "Tabbas kinyi nasarar rabani da d'ukkan farin cikina Bintu.. Kinyi nasara,tanan kam nasan kin ma Salma fincinkau,dan ita bata sharri.. "Na baki d'ukkan wata amana,ki mayarni shashasha.. Ki nunan yau abinda Salma take gudu a kishiya,"makirci".. "Amma ki sani,wallahi!,wallahi!!.wallahi!!! Uku,yadda kikai sanadin 6allewar aurenmu da Salma kinyi naki. "Kamin nan zaki ji jiki kamar yadda ki ka sa taji t'sawan zaman ku.. Kan tai kwakwaran mot'si ya hard'o ta, ta ko'ina mari yake bata iya karfinshi tana ihun jama'a su ceceta.. Sai da tabbatar ya taga wuta dan mari kamin yana haki ya nuno ta. "Kije kema,na yanke igiyar aurena dake kanki har guda uku... "Tun kan ki kwana maganar Salma ta kar6u gun Allah... Ihu ta saka tana bashi hakuri kan ta daina, "dan Allah karka sake ni... Hanyar waje yayi yana sa waya a aljihunshi. "Ki tabbatar baki kara awa d'aya cikin gidana ba,dan saki uku na furta. Waje yayi ya ja ya t'saya a zaure,tamkar wani yaro ya rushe da kuka mai tsanin ciwo.. Yayi kuskuren da dak'yar ya g'yara shi cikin rayuwarshi.. Yayi kuskuren da ya bari Salma tai mishi nisa... Yayi kuskuren kin kar6ar shiryiwar Salman sa.. Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwa. "Allah ya isa t'sakani na dake Bintu... Ubangiji yai ma Salma sakayya akanki daga yau har ranar sakamako... Allah ya isar mata cikin sauri.. Ganin hakan ba mafita bace gareshi yasa ya d'akko waya hannu na ka'rkarwa zai nemo Garba yaga kiran Aunty A'i na dazu. Garban ya kira,dole ayi wacce za ai,Aurenshi da Salma mutuwa ce kadai zata raba. Da Allah ya had'ashi cikin muryar kuka kan yazo gidanshi yanzun nan.. "Isha'i ake kira fa Ja'afar.. "Dan Allah kazo,in bakazo ba komai zai iya faruwa... Ba'a fi minti goma ba yazo,fatattakar arziki yai ma Bintu ta bar gidan ya rufe ya fad'a mota. Da t'sananin mamaki yake k'allon abokin nashi, a iya abotarsu bai ta6a ganin koh da hawaye na Ja'afar ba bare kukanshi mai sauti irin haka. Dan Ja'afar namijin duniya ne,Jarumi, kuma jajirtacce, yasan komai ya sashi kuka ayau ba karami bane. "Gidan Aisha zaka kai ni yayar Salma.. Baki sake yake k'allonshi, "Yayar Salma kuma?.. Ido jajir ya kalloshi ba halamar wasa,dole ya tada mota suka d'au hanya. Waya yai mata kan ta fito yana kofar gida. "Malam mijina ya fita..kai hakuri.. Kit ta kashe wayarta,yau Aunty A'i ta d'au zafi ya sani,tabbas kuma Salma na gidan.. Murfin motar ya bud'e a fusace ya fice Garba na kira.. Kofar a bud'e take,kawai ya tura ya shiga, nufinshi a d'aureshi bayan yaga Salman. "Salma!,, Salma!!.. A tunzure Aunty A'i ta fito a parlourn dan tsayarahi shiga mata parlour. Yadda taganshi bata isa hana shi ba ganin Salman, dan g'wiwa biyu ya zube gabanta tamkar yaga Salman. Hanya ta bashi ba musu,da zafin nama ya mike ya shiga parlourn, bata zata ba taga mutum a kanta,da sauri ta zabura ta mike tana kwad'a kiran Aunty A'i da sauri. Bata nufa ba taga mutum zube a gabanta kanshi a kasa. Ido ta rint'se tare da kawar da kanta,koh kadan bata son kara ganin Ja'afar a rayuwarta Abadan. Juyo wa tai da niyar surfa mishi ruwan bala'in da ba shiri zai bar gidan,sai dai mey? Da t'sananin mamaki take kallonshi tana k'allon Aunty A'i. Hawaye ke malala a idonshi kamar wanda ya rasa jin dad'in rayuwarshi,abin g'wanin ban tausayi. Ja'afar?.. Kuka ma?, a namey toh?. "Salma gani gabanki, a matsayin wanda ya tafka miki laifi cikin rashin sani,da kuma sharrin Bintu..Salma kiyi hakuri,wallahi _am really really sorry.. Kar ki barni dan Allah.. Zan tagaiyyara Salma.. Zan zauce.. sharrin Bintu ne,kuma itama ta amshi hukunci,dan na saketa kamar yadda ta jawo mana, _please_ Salma _forgive me_... Wallahi _I can't live without you anymore_,ki tausaya ma mijinki uban yaranki... Baya taja da sauri ganin yana kara kusantota. Da sauri Aunty A'i tai waje jin kuka zai kubce mata.. Dole haka zata kasance dasu Salma,ranar rabuwa, rabuwar da ba a da tabbacin za'a dawo ta.. Tabbas tausaya wa rayuwar su,dan a irin soyayyar nan ita ce ake kira *Mutu ka raba*.. Gashi yanzu K'ADDARA ta raba masoyan biyu. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:24 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 32_Kuka take yanayi iya karfinsu, tabbas K'ADDARA ta rigayi fata, duk kuma yadda ka t'sara rayuwarka sai ka ga ba haka ya tafi ba,tabbas ta Allah itace daidai. Baya tai ta zube kan kujera da6ar.. Duk sunyi kuskure, kowa na da laifi,meyasa ma tace ya saketa?.. Mey yasa?.. Le6e ta cije tana mai sa d'ukkan hannunta biyu zuwa fuskarta, kuka kam yau har sunji ba dad'i. A hankali ta dago tana K'allonshi ido yai luhu- luhu,duk ya marairaice mata hawaye na zuba, tafi tausayin kanta sama dashi, Kokarin magana take su Aunty A'i sukai sallama ita da maigidan da taima waya. Fuska Ja'afar yai saurin gogewa ganin yadda Abban Aslam ya sau baki yana kallonsu,bai tunanin abin ya kai haka ba, kuka a gaban mace da zubewa g'wiwa biyu?.. Lalle yasan abin babba ne. "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Itace kalmar shima da ya fad'i bayan yaji mai ke faruwa.. "Dole aje gida kowa ya samu labari,dan wannan ba abin a 6oye bane koh da za'a nemi sulhu,saki ya cike na uku abin yafi karfin zama anan Ayush.. Zamu tafi da Salman kai Ja'afar sai ku taho da abokin ka. Har kusan goman dare ana abu daya akan zancen saki. "Ka ce kayi saki,ita tace ya zama uku, sannan kana zancen ai sulhu koh? Kai ya daga da sauri, murmushi Abban yayi,abin yaso ma bashi dariya, "Wato Ja'afar... "Malam Umar wannan zancen ba zancen da za'ai wa sakwakwa bane,kan Ja'afar ya dawo. "Kai kuma in dan baka tashi mun wuce ba zan mugun sa6a maka yanzun nan.. "Kana hauka ne?.. A wane garin ka ta6a jin anyi saki d'ai daya har uku kuma ana neman sulhu?.. "Ai baka fara ganin komai ba Ja'afar, ba dai zuciya ba?.. Za ta sa ka dana sani, "Malam Umar ai hakuri bisa wannan K'ADDARAR da ta sakko mana,zamani ne yanzu muke ciki da yara basu dauki saki a bakin komai ba.. Tashi yayi yana bawa Abban Salman hannu,kan ya kallo Ja'afar,har yanzu sautin kukan su ke fita shi da Salman. "Muje koh?.. Salma ya dago ya kalla da sunkuyar da kai, "Salma dan Allah ki basu hakuri kar su rabamu,kin san bazan iya rayuwa ba ke ba,Abadan Salma...Please. Kuka ta kara saka mai karfi, t'saki Abba yayi ya karkade riga yana nuno shi cikin fad'a. "Hauka kenan wannan, dan koh a musulunce Salma ta haramta a gare ka..ta haramta har abada,dan kai kam ka nuna mana bazaka ta6a iya rike aure ba, saki tamkar wasan yara? Itama waccan wai ka mata saki uku?.. Toh koh aure Salma tayi na fad'a maka ta haramta a gare ka har abada,kaje kaci zuciya. Da gudu Salman ta tashi tai d'aki tana kuka.. "Haba Alhaji, abin bai kai haka ba,kuskure ne kowa yana iya tafkawa a rayuwa.. Anji bai k'yauta ba,amma kar hakan yasa kai mishi baki,kai hakuri. "Hakuri shine ya biyo ni yanzun nan.. Wace iriyar haukace wannan kamar a jahiliya?.. Wani yai mishi sakin?.. Haka Ja'afar naji na gani yai waje yana waiwayen dakin da Salma ta shige yana hawaye. Tun daga ranar duk suka zama sakwa- sakwa, barin Ja'afar da baida kuzari,ga Abba ya sako shi gaba ta ko'ina.. Dan har gida iyaye Bintu suka zo sukai ma Abba rashin k'yauta wa akan yadda bayan saki uku sai da aka kumburawa ya'rsu fuska,harda ikirarin koto,dak'yar aka basu hakuri kan suka debe kayanta, ranar Abba yayi takaici har yaji ina ma da ya barma Umman shi Ja'afar,kila da baici karo da bacin ranshi ba. Sai dai yace kayan Salma koh sama da kasa zasu had'e ba mai diba, ashe ma in ya bari aka diba sun rabun kenan... Ja'afar mat'sala. Anyi ban baki, Abba yayi fad'an ya dawo lallashin amma Ja'afar ba sauki,kawai sai Abban Salma yace a rabu dashi,dole in ta tashi aure zai bari a diba da kanshi. Kullum ta Allah yana kan jelar gidan su Salma,a wata guda har kama ya sauya,ba aski,ba g'yaran fuska,ya zama tamkar zararre. Sosai Abba yake tausaya mishi,Mama kadai ke shafawa idonta toka ta hana ya ga Salman,sai dai a bashi Miemie, haka zai gaji har ya tafi,sai dai tai ta ganin text na ban hakuri,gobe ma zuciya zai dawo. *************** *************** Rayuwa irin ta kunci kam sun ganta a wata hudu da ta gabata. Salma ta saduda sosai akan Ja'afar,dan har yanzu shi yana kan bakar shi. Sam in ka ga Salma ta sauya,ta dawo shiru shiru sosai,kullum zaka same ta a daki,koh ta dukufa tunani, koh tana k'allon Miemie tana hawaye. "Salma... Gefe tayi da sauri da kanta tana goge hawayen jin maganar Mama akanta. Dole yau ta kawo karshen matsalar nan. Zama tayi a gefen gadon tana kare mata kallo. "Rayuwa fa kullum sauyi take Salma,amma banda taku, ni dai ban ta6a cin karo da kulafucin D'a namiji irin naki ba, wata hudu ba kwana hudu bane Salma.. "Lokaci yayi da za ki cigaba da rayuwarki ki manta da kashin Ja'afar.. Ki d'auka Rabon Miemie kawai ya had'a ku,ki manta da rayuwar da,dan ta wuce,ki fuskanci zahiri a rayuwar gaba Salma.. Fad'a Mama ke ta mata tana kuka, taya zata mance Ja'afar?.. Taya zata mance zaman su?..Soyayyar ta da Ja'afar had'i ne na Allah a ganinta ba wai wani rabon Miemie ba... In har Ja'afar na bata haushi bai wuce yadda ya dankara mata saki ba ba ji ba gani,amma bacin hakan,tabbas bata da sama da Ja'afar a zuciyarta kawo iyanzu.. "Nasan da kin gama iddar ki sarai... Da sauri ta k'allo Mama da t'sananin mamaki, kai Maman ta kad'a mata. "Tunda ki ka zo gidan nan ina fuskance dake Salma,kin gama iddah tun wata uku da suka wuce. Kasa tai da kai tana goge hawaye,tasan Mama gaskiya ta fad'a, dan shayarwa bai hanata period ba.. "Nasan ma hakan ne Salma,yanzu abinda nake so dake shine, "Dole ki fara fita,dan saki ba takaba bace, bazai yu kiyi ta zama a gida ba kamar matar kulle,tun yanzu zaki fara fuskantar cigaban rayuwa,bana son musu koh taurin kai Salma a zuwan nan daga gunki, dole komai nace kiyi kiyi, kina jina koh?. Shikenan kuma,ta faru ta kare,wai an ma mai dami daya sata.. Shikenan ta shiga sahu,yanzu sai jiran bazawari.. Kuka ta sa mai sauti,yi take ba kakkautawa,har ta kular da Mama ta bar lallashi ta hau sababi. Dole kam in dai ta yadda da K'ADDARA ta maida komai ba komai bane.. Dole ta daina yaudarar zuciyarta,tana biya zancen Ja'afar a kullum akan tashi ce shi kad'ai.. Hannu tasa ta share hawayenta,kan ta g'yara zama. "Na shirya bin umarnin ki Mama matukar bai sa6a shari'a ba.. Baki Maman ta washe, "Koh ke fa,yanzu naji batu,ko ke fa Salma. Kasa tai da kai tana murmushi, sosai taga farin cikin Mama. Washegari da dare bayan Abba ya dawo taje gunshi suna zaune da Mama,yai mamakin sauyawarta faradd daya,shima sai murmushi yake mata. "Abba.. Zama ya g'yara da murmushi ya amsa. "Abba makaranta nake son shiga dama... Da sauri Mama ta kallota, ji zata kwafsa musu kuma,wai makaranta? Baki ya washe dan murna. "Toh Salma,kinyi tunani mai k'yau, Allah yasa a shiga a sa'a. Kai kasa tace "Amin Abba... "Anjima ina son zan k'waso akwatina na a gidan Abban Miemie koh da y'ar makota ne.. Kai ya kad'a mata "A'a,ki bari zan ma shi Ja'afar din magana zai kawo miki har gida. Sosai sukai fira Mama na jinsu bata ce kala ba,tana shiga d'aki Maman ta bita. "Ya zaki min haka Salma?.. Wace makaranta kuma ana zaune lafiya?.. Shiru tai sai da ta gama kan tace ba abinda karatunta zai tsare mata,tai hakuri tasan zai mantar ta wasu abubuwan. Ba dan taso ba ta yarda. Ta gama da Mama, saura Ja'afar. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:25 AM - Queen Safiyyert馃憫: A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 33_Washegari Abba da kanshi ya samu Jafar din a shago,duk da yai jim,daga baya ya tuna da wannan ne damarshi na ganin Salma a yau dan tuna mata da alkawarin shi. Da yamma k'wa yasa Garba ya k'waso mata akwatinan ta da sauran sabbin kayanta marar dinki. Da sallama ya shigo gidan, ya k'wa taka babbar sa'a Mama bata nan. T'saye yayi ganin Salman t'saye a gaban famfo Miemie na mata kukan kunu tana dauraye murfin feedern. "Sam baki da jimirin yunwa Miemie,kimin hakuri yanzun zan... Itama shirun tai dan jin sallamarshi. Da dan rarrafe da tafiyar da batayi kwari ba ta nufi gun Abban da murna. Ganin Miemien ne yasa shi dawo da hankalinshi kanta,sama yai da ita kamar kullum suna dariya. A hankali ta rufe idonta tanajin zuciyarta na bugawa da sauri,kusan wata 2 rabonta da ta sashi a idonta,jin takunshi na kusanto ta yasa ta juya da sauri tare da had'iye hawayenta. Ya sauya mata,duk ba g'yara, har wata kasumba ya had'a ta dole ta rashin g'yara fuska. Da t'sananin murnar ganinta ya karaso sai washe baki yake,da sauri tai baya ganin abinda yake shirin yi tai gun taburma ta d'akko,sai ya bita da kallo baki sake, tabbas Salma batai kewarshi kamar yadda ya mato a kewarta ba.. Koh irin d'aukin nan na ganinshi t'sawan lokaci haka bata yi. Dan dukan da Miemie take mishi ne yasa ya kallo ta,da hannu take nuna mishi kan feedern dake hannun Salman. Kan taburmar ya nufa tare da zama,so yake sai ya fassara yanayin Salman,shi yasa yake ta k'allonta. Feedern ta mika wa Miemie tana dan satar kallonshi kan ta kau da kai tace "Ina wuni.. Shiru yai mata,sai ta dan kalloshi cikin ido,shima ita yake kallo,bazata iya kallon kwayar idonshi ba,zata chaza mata matsala,da sauri ta kara dauke kai tana maimaita gaisuwar. "Mey yasa kwana biyu ba k'ya d'aukan kira na Salma?.. Ba k'ya ban amsa koh na miki text?.. Gefe ta kara yi da kanta tana kallon wani waje, kan tace "Ban gani ba ne.. Da mamaki yake kallon yadda tai maganar cikin nuna ko'in kula. "Salma kin daina so na yanzu koh?.. Yadda yai maganar yasa jin wani iri da dan tausayinshi,da jihadi ta juyo ido cike da kwalla. "Ya Ja'afar, ya dace mu fuskanci zahiri fa yanzu,mu daina yaudarar kan mu dan komai ya afku..Dole nai aure ka sani,ban maka alkawarin zama ba aure ba,bazan maka alkawarin kin kula wani ba.. Yanzu haka karatu zan koma,ka d'auka rayuwar da ta shud'e a mafarki muka yi ta, yanzu mun farka... Dole akwai cigaba a rayuwa.. Kai hakuri, amma bani da alaka da daukan kiran ka yanzu,ka manta Salma dan Allah,mu fuskanci rayuwar gaba.. Kai ta kautar tana goge hawaye, shi kam k'allonta kawai yake ba koh kiftawa. "Ke nan kina nufin son da nake miki karya ne?... Soyayyar mu hasashe ce Salma?.. Zaman mu da rayuwar auren mu wasa ne?.. Kina nufin Miemie ma mafarki ce?... Da fusata yake tambayarta,kai kawai take girgiza mishi tana hawaye. "Ba haka nake nufi ba.. "Toh mey ki ke nufi?.. Shiru tai tana cigaba da kukan ta,sai ya kada kai cikin takaici. "Salma kin d'aina so na kam.. Girgiza mishi kai tai "Ina sonka Ya Ja'afar, har karshen rayuwata.. Abu daya nake son ka gane,yanzu komai ya sauya,alakar Mimi ce kawai ta rike mu... Ka cire son zuciya aciki, dan bazan iya haramtawa abinda Allah ya halasta min ba.. "Assalam Alaikum, wannan akwatunan fa a zau... Tsaye tai ba tare da karasawa ba, kai kasa ta amsawa Mama sallama,ciki Maman ta karaso,ya gaida ta kai kasa,duk shiru sukai ba mai magana, sai muzurai Mama take ma Salman kan ta shiga daga ciki. Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga ciki,a hankali ta sa kanta a kan katifa tana hawaye. Ba dan yaso ba ya tashi yai fita,tare da shigo mata da akwatunan ta. Har zauren Mama ta bishi ta sa sakata tana sababi kan tai gun Salman. "Wai ke baki da hankali ne Salma?.. Meye had'inki da wannan da har zai shigo cikin gida ki bashi taburma, har ki zauna a gabanshi kina wannan shashancin cin?.. Mey fa rabawa(K'ADDARA) ta raba ku har abada. Shiru tayi har Maman ta gama tana ta kok'arin shanye kukanta, ta sani da koh tayi bayani Mama bazata gane inda ta dosa ba. "Kiyi hakuri bazan sake ba. Kai ta k'ada tuni har tai laushi. "Ina kuje miki yaudara irin ta D'a namiji ne Salma,gaba in kina mishi haka sai ai abin kunya. Shiru tai tanajin wa'azin Maman kawai. G'yale ne kusan kala 5 had'add'u,tana washe baki ta fito dasu daga leda. "Ki zabi na za6a ki darje,dan zawarcin ki sai yafi y'an matanci a komai Salma, gobe kayan k'walliya zasu zo dan na bawa Hajiya Jidda kud'in kayan g'yaran jiki,ga wata yayi nisa da komai kin samu akan lokaci.. InshaAllah sai mun cike gurbin da muka rasa.. Ni da zakiji shawarata ma da an yaye Miemie a satin nan a mikata ga gidan su chan ya karata... Da sauri ta dago tana kallon Mama, Kat'seta tai da fadin "Eh man,bashi yake ikirarin yana kawo shi ba?.. Toh zamu mayar mishi da abarshi kawai. Kai ta hau girgiza ma Maman,Allah yaga ba mai rabata da Miemie sai aure. "Mama Miemie fa karama ce,kawai tai saurin tashi ne,koh fa wata tara bata cika ba.. Dan Allah kiyi hakuri,dan ba abinda zata t'sare min koh a makaranta. Harara ta aika mata, "Kina nufin da ita zakina fita?.. Kallonta take ta rasa amsar ba Maman. "Toh da sake wallahi, ba yadda za ai ina tufka kina bin bayana da warwara.. Zawarci da goyo?.. Toh da sake,dan ba mai gani ya kulaki alhalin kina sa6e da y'a. "Aikina fitarshi ta naga dama ce,in ma kince baza'a mayarta ba ni zan na miki renon,aje a dawo lafiya. Shiru tai tana jinta kawai. Washegari sai ga kayan k'walliya jibgi,su mascara, eye shadows,su sabulun g'yaran fata harda su man gashi,ga haddun man gyaran jiki,lalle Mama da gaske take. Shi kam tunda ya koma da yazo k'wanciya yake tuna dazu,lalle in Salma tasan wata toh bata san wata ba. Tazo k'wanciya taji karan wayanta,agogo ta duba, tasan ba mai mata haka sai mutum daya. Badan taso ba ta d'auka, sai dan jin dame yazo. "Naji kije makarantar, amma bisa sharad'i uku.. Baki ta bud'e cike da mamaki,wai koh ya manta bata karkashin ikon shi ne yanzun? Dan dai taji sharad'in tace tana ji. "Good. "Na daya kafarki toh kafar Miemie duk inda zaki shiga. "Na biyu ba zancen yaye sai Miemie ta cika shekara biyu kamin kiyi komai. "Na uku,fitar ki sai da nikaf da hijab,sannan ni zan sama miki mai kai ki a Napep ya d'akko ki in kin gama, dan ba ko wanne kato zai na d.. "Ka ga malam,ka bari ka fad'awa Miemie wannan dokar taka ba wai ni da nake Salma ba... Dan ba y'ar ka bace ni,ni nake da damar t'sara rayuwata yanzu ba kai ba. "Abu daya nasan na yarda zan iya shi,shima dan hakkin ka ne dole,shine yaye Miemie,zanyi yadda kace, sauran kuwa ba huruminka bane... Wayar yabi da kallo baki sake jin ta kashe kit.. Lalle Salma ba ta so zaman lafiya ba a garin nan, amma zata jidi mamakin shi. Dan shi tai mishi daidai ma da zata tafi makaranta. Tun daga ranar ya daina kiranta a ganinshi zata damu ta bashi hakuri ayi yadda yaso,sai dai ta daure ita. Ana haka ranar Abba yace ya batun makarantar da yace zai koma?.. Kanshi t'saye yace ya ma Abban ai ya fasa. Nan ya bud'e mishi wuta kan bai isa ba,duk haukar da yake ranar ya samu labari gun Mama,dan har gida tace ai mishi t'sakani da Salma,sai dai yazo za'a bashi Miemie in dan ita ne. Sosai yaji haushi,yasan aikin Salma ne..shi yasa ya d'auke mata wuta,sai dai ya tura k'annenshi su dakko mishi Mimi Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 4 Feenat Ja'afar Novel's Su Salma an samu gurbi a school of hygiene,da shawarar baba ta cike ba Polly ba. Ranar da ta fara fita da personal zata kai takaddun ta. Ba yadda zaka ga Salma ka gane itace da lokacin tana budurwa, yanzu Salma ta daban ce,ta gaban goshin Mama, dan ta dage dole sai tayi kara'i da zawarci. Kwanar su Ja'afar ta shawo,tasan yanzu haka yana makaranta dan sha d'aya na safe. Sosai tai k'yau cikin doguwar riga ruwan kwai mai duwatsu,da g'yale karami ta nad'a fari,ta ritaya jaka karama mai (chain),ba wata k'walliya tayi ba ta azo aga,dan wannan ma Mama na t'saye tayi ta,ta kuma rantse ita da hijabi sai a sallah. Zai wuya kace ta ta6a aure har da rabon Miemie, dan yanzu ne take shekarunta na (22) a duniya. Kanta kasa take tafiyarta cikin nut'suwa, sai dai ji take duk ta tsargu,tamkar Ja'afar na kofar gida yana kallonta. Dak'yar ta kai kanta bakin kwalta tana sauke numfashi, ashe feeling take... "Kin k'yauta Salma kenan?... A razane ta juyo jin mai maganar.. Rai had'e yake kallonta tamkar bai ta6a dariya ba. Duk da ta tsorata da ganin yanayin da yake amma ta cije itama ta ci kunu. "Da nai mey fa? Rai 6ace yace "Ina Miemie?.. Kai ta k'autar gefe,kan tace "Gida".. A fad'a fad'a yace "Wato bakiji abinda nace ba koh?.. Kalli shigar ki,kamar wacce zata party,sam baza mu shirya dake ba in.. "Tafiya ne?.. Wani mai keke napep ya tambaya, kallo irin na baka isa ba tamai, kamin tace ma mey keken "Eh tafiya ne. Tana kokarin shiga tace "ba ruwanka da shiga ta,cos I know what i'm doing.. And ni ba y'arka bace, na fad'a ma ka rabu dani. Sam taki k'allon fuskarshi bare ta sare gun taka mishi burki. Baki sake yake binta da k'allo har mai napep yaja kamin ya samu k'warin ya tanka. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:28 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/7, 11:03 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 34_Jingina tai a jikin Napep din tana sauke ajiyar zuciya. "Kai hakuri Ya Ja'afar, ya zama dole na koya ma nisa dani,kai hakuri,ina sonka wallahi.. "Hajiya magana ne?.. Kai ta dago jin mai Napep na tambaya, ashe maganarta ta fito fili. Ta gama komai Monday zata fara zuwa,kwarai taso ta yaye Miemie sai dai ba hali,dole tabi yadda uban y'ar ya t'sara. Shikam Ja'afar tun daga wannan ranar kullum zata makaranta sai yai mata maganar wani abu,koh yace k'walliya tayi yawa, koh yace uniform ya d'ame ta. Wani sa'in har ta wuce tana dariyar zariya irin ta Ja'afar, tabbas gani take ya zare. Shima kamar yadda Abba yace haka dole ya fara _processing_ dan tafiya masters a B.U.K,sai dai fur Abba yace garin zai bari,a Zaria zai yi,kar ya damu an ma kusa shirya masa komai ba koh kwandalar sa. Tamkar ya aza hannu aka ya kwala ihu yake ji ranar,yana nan ma ya ya k'are da Salma bare ya mata nisa?.. Tafe suke ita da wata y'ar makarantar su da tazo zata rakata bakin kwalta, ta gama shirinta kenan zata gidan Aunty A'i sai fasawa tayi. Tai kyau,fatar sai shining take taji mai da sabulun Mama. "Allah ba wanda zai ce kin haifi Miemie sis Salma,kin ganki kuwa?.. Murmushi tai ma kawar tata lokacin da take t'sayar mata da Napep. "Haka dai kuke cewa kullum.. Murmushi tai mata sukai sallama. Tana kula da wani mai mota yana ta kallonta ya t'saya siyan Apple. Kokarin tsallakawa yake ganin zata wuce da sauri,kai ta kada dan sarai tasan yau ma za'a tafka dirama irinta ranar chan da Ja'afar, dan tana kallon yadda yake maka mata harara a kofar gidan su suna zaune shi da Garba da wani,tasan darajar kawarta taci da yanzu ya taso bambami dan tasa g'yale a kafad'a, kai ta girgiza dan yanzu abin dariya yake bata ma... "Assalam Alaikum.. Waiga wa tayi jin an mata sallama. Da dan sakin fuska ta amsa tana mai cigaba da tafiya a nut'se. "Gunki nazo fa y'an mata dan Allah. Kai ta daga aikwa idon Ja'afar kyar kanta. Da murmushi ta juya badan taso ba sai dan yakice dan gudanta, duk da tasan baza a wanye lafiya ba. Tuni dad'i ya kama saurayin dan da har ya fara d'ari-d'arin mata magana,sai ya ga kamar matar manya ce. "In bazaki damu ba dan Allah ki ban numbern ki,wannan ne gani na biyu da na miki a layin nan yanzu ina sauri zan kira ki... Ta gefen ido ta sato k'allon Ja'afar ai kwa a suk'wane yake zuwa gun nasu. Da sauri ta karbi wayar mutumin da zummar sa mishi ya iso. Su dai su Garba ido ne nasu,dan abin Ja'afar ya daina bashi dariya yanzu tsoro yake bashi. "Bashi wayarshi ya kauce tun kan na dagargazata a gun nan.. Banza tai dashi tana cigaba da latsa wayar karya,bata aune ba taji ya warce da karfi. "Karbi wayarka ka bar layin nan Malam, koh kaga tayi sa'ar tsayuwar ka?.. Baki sake saurayi yake kallonshi,shi a tunanin shi koh yayanta ne ma,dan shima haka yake ma samarin k'annenshi baraza,dan haka bakin shi alaikum ya kar6a yana kallon Salman. Cike da tsiwa ta kallo Ja'afar din, "Malam wai ina ruwanka da samari na ne eyeee?.. "Kimin shiru tukunna, kema zan dawo kanki ne ai. Da hannu ya nuna ma saurayin hanya halamar ya ware,ba daban yaga Ja'afar din ba na wasa bane ba da ba yadda za ai ya bar wannan sankaceciyar budurwar. Da sauri ganin zai tafi tace "Malam ina zaka ne?.. Kai ya kad'a mata yana murmushi kan ya kara gaba. A fusace ta nuno shi da hannunta "Wallahi Ya Ja'afar na gaji da wannan abin fa,dan wallahi na kusa kai karar ka gun Abba ya mana t'sakani,mey ruwanka dani wai?... Shiru tai tare da matsawa da sauri ganin ya mika hannu bayan gyalen ta. "Wai kai lafiya ka ke?.. Harara ya sau mata kan yace "Tun muna sheda juna ki daina sarar nan ta sauke g'yale a kafad'a Allah... "Bazan daina ba din, na fad'a ma bani ba kai, tunda kai har yanzu bakasan Annabi ya faku ba... Shiru tai ganin Garba. "Haba Salma,haba,a titi fa ku ke?.. Tunda kinsan halin kayanki sai ki gaba ki barshi ya karata, dan Allah ki daina biye mishi. Harara ya sakar ma Garban, "ina ruwan ka toh kai ma,kowa dai yasan da matata nake t'saye ba kowa ba.. "Mtsww... T'saki taja rai 6ace, duk suka kallota.. "Wallahi you are sick.. "Ni matarka ce, amma fa a da, kai istigfari ma tun wuri,dan wallahi za kayi sa6o... "Kimin shiru fa Malama..dan kwanciyar hankalinki wallahi kibi abinda na ce kiyi,period.. Shiru tai tana kallonshi,karfin hali sai gun Jafar,tabbas sai tayi da gasken gaske,dan abinshi gaba yske,shima Garban k'allonshin yake,abu dai kamar wasa yake gani yanzu zai zama babba. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 35_Drama sosai sukai kan ta wuce gida rai 6ace duk rai a dagule, dabarar ta ta kare kuma a akan Ja'afar, duk hanyar da zai zuciya ya daina kulata tabi ba nasara,tamkar ma zigi take mishi. "Mtsww... Taja t'saki,Tabbas so so ne,amma na Ja'afar son kai ne,dan shi yaja komai.. "Ke kuma ke da wa kike t'saki haka?.. Ba tare da ta dago ba tace "Ja'afar man.. Ya hanani sakat a unguwar n... Da sauri ta datse harshenta dan jin Mama fa ke tambaya, "Au har yau yana nan yana bibiyar taki koh?... Kai ta girgiza da sauri, zarar bunu.. "A'a, ni nasan hanyar maganinshi,ki ban nan da gobe. Da sauri tace "A'a Mama ba komai bane fa,kiyi hakuri zai daina... Shiru tai ganin harar da take aiko mata. Tun daga ranar Mama ta zama y'ar rakiyar Salma hanya,sai ta tabbatar ta hau abin hawa zuwa makaranta zata juyo tana aika mishi harara,da tai na sati sai ya bar tare hanya kuma ya dawo waya. Ana haka shima admission nashi ya fito shima,tuni ya shiga kunci,dan yasan ya kusa yin nisa da Salma,hakan yana nufin komai zai iya faruwa. Ranar da yamma ana washegarin zai tafi yazo mata sallama duk da sunyi fad'a. Taimakonshi daya Mama bata nan ranar ma,dan yana ga ita kad'ai zata iya tsaida shi a yima Salma kashedi. Shigarshi zauren kenan sukai kicibis zata fito,harara ya sakar mata kan yaja ya t'saya. Fita take shirin yi ya ruko gyalenta da sauri har yana zamewa,don haka a fusace ta juyo da niyar balbaleshi ya marairaice mata fuska. "Saken g'yale toh.. Murmushi yake yaki saka, ''ka saken gyale koh na fuce... Da sauri ya cika yana tare kofar fitar. "Maganar fahimta nake so muyi dake,dan Allah ki t'saya.. Hannu ta hard'e a kirji ta k'alleshi,itama zata so su fahimci juna. "Ina wuni toh,tunda har gaisuwa kin soke dani. Da kalar tausayi ya kara yana sukui da kai har taso yin dariya kamin ta gaishe shi. "Ina Miemie?. "Da Mama suka fita,kayi kai maganarka kan su dawo fa. Tsayuwa ya gyara tukun ya kira sunanta, rai sake ta amsa,fatan ta yasa zancen azziki zai mata ba wai shirme ba. "Salma".. A karo na biyu ya kara kiranta, bai jira amsarta ba ya cigaba, "Gobe zanje Zaria kan batun makaranta da zan fara, kima Allah Salma ki yi kamar ina nan dan Allah,banda kula tsagerun samarin nan wanda har yau basu mallaki hankalin kansu ba dan Allah. "In ma aure naso kiyi ina ga ni ya dace na baki mijin aura,bare a agendar mu bamuyi haka dake ba... T'sam tai tana kallonshi da halamun ya zare tana murmushi, amma zata bishi a haka a wanye lafiya. "Toh naji,zan kuma kiyaye,happy?.. Kai ya kad'a da murmushi, "yauwa koh ke fa,dan Allah Salma ki riken alkawari nan.. Kai ta kad'a tana taji ai.. Da haka suka rabu ya bata kayan zakin Miemie, murna fal ranshi suka rabu ranar. K'warai ta samu sakewa sosai bayan tafiyar shi,tuni ta kara bud'e shafin zawarci sabo,duk da kasan ranta tausayinshi take ji sosai. A wata daya tai samari biyu irin son Mama, barin Alhaji Usman Dan chanji. Kud'i sosai yake kar mata kamar ba gobe, albarka kwa kullum samunta take gun Mama,yace shi ba yaro bane,dan haka yana so ai auren cikin k'ank'anin lokaci. Ya sanar mata yana da mata daya da yara biyu kachal,aurenshi uku,sun rabu da biyu sai Hajiya ta k'arfen. Tunda suka rabu tazo gida tana tuna abu uku, tabbas a yanzu bata da ra'ayin auren mey mata,dan taga aya akan Bintu. Sannan bata son mutum mai irin kud'in Alhaji Usman sam a rayuwarta. Gwara ma Kamal dan shi matashi ne kamar su Ja'afar, kuma yafi kwanta mata a rai,gashi da saukin hali da saukin kud'i. "Oh ni y'an nan,ashe arziki ke binki Salma a rayuwa?.. K'allon Maman take yadda take daga abubuwan da Alhaji ya bata,ita dey nata ido. "Bana jin koh lokacin y'an matancinku kun ta6a had'uwa da irin wannan, babbar harka ai tayi y'an nan... "Mama ni fa mutumin nan bai kwanta min ba sam Allah,gashi har ya fara maganar aure tun yanzu,ga yana da mata fa,ga ni sam irin kud'in nan baya... Baki sake Mama ke k'allonta,tuni ta tsayarta cikin fad'a. "Rufe baki ni sauraniyar y'an iya t'sari, ashe har yau kina nan da halin nan Salma? Arziki na binki kina zura da gudu?.. "Ina ruwanki da matarshi?.. Koh a kanta zaki zauna?.. Kai ta girgiza zatai magana ta dakatar ta. "Koh dai Salma hudubar yaron chan tai tasiri akanki?.. Kai ta kad'a, "Allah Mama ba haka bane,ni ina tsoron kishiya ne,kinaji fa wai aurenshi uku suna rabuwa sai ita ke zama... "Sai mey toh?.. Kar ki bada mata mana Salma?.. Baki sake take k'allon Maman,kamar ba ita ke fad'in ba mai zama da kishiya ba a yaranta tunda itama bata zauna ba,wace daga ce ba'aci ba lokacin auren Bintu da Ja'afar amma yanzu kud'i ya warware Mama?... Kat'seta tai, "Saboda haka komai yace ki ce toh, in ma ita ke fidda su toh ke zama daram,dan wannan ba gidan fita bane in an shiga... Hawaye ke zubar mata yayin da tazo k'wanciya tana tariyo zancen Mama, dole in dai tana son faranta mata wai ta ba wa Alhaji dama. Waya ta d'auka jin shigowar text message,tasan na Ja'afar ne. _"Salmatee,remember, a heart dat truly loves never loses hope..but always believes in d promise of love,no matter how long d time and how far d distance,at d right time,love will fine a way".._ ki rike alkawarin ki,love you.. *Ja'afar* Kukanta ne ya karu sosai bayan ta gama karantawa, tabbas in ta cigaba da sauraran kalaman Ja'afar zasu sa ta karaya har ya ci galaba akanta.. "Bani da kamar ka har kullum Ya Ja'afar, sonka gareni ba mai misaltuwa bane,amma kai kaja mana koma meye... Fuska ta goge sakamakon jin tahowar Mama da Miemie na kuka. Washegari kanta t'saye ta bawa Alhaji damar ya turo magabatanshi kawai koh ta huta da dawainiya da son Ja'afar. Sabon sim ta siya tasa a sabon wayar Alhaji da ya bata,a haka suka raka wata kusan biyu, duk da tai kewar text da kiran Ja'afar din. Shikam yana chan hankali tashe na rashin samun wayar Salma, ga Abba ya sanarshi kar ya sake ya dawo sai an nemeshi a makaranta, Duk da an sanarshi ana kawo Miemie gidansu ta yini. A jikinshi yaji abu na faruwa,duk sai yaji bai da nut'suwa sai ya je gida dan tabbatar da zarginshi. *** Tunda daga d'anno kanshi layin su Salman ya ja ya t'saya. T'saye take da dan murmushi a fuskarta, sanye cikin favorite dinshi riga da skirt na atamfa purple, tai kyau matuka gyalen nan a kafada,daga inda yake zai iya gano bakin gashinta a tufke ta chan kasan dankwalinta, tasha ado tamkar zata party. Wani abu ne yazo dai dai makogwaronshi ya tsaya,kishi... Bai san ya isa gun ba sai da yaji ana "lafiya?.. Kallo shi yayi, duk sai yaji yau baida ma k'warin g'wiwar fad'a,Salman ya kalla,da sauri ta kawar da fuskarta gefe ta had'e rai. Sai ya dawo kan Alhajin,tsaf sai ya haifi Salma,sai t'sabar kud'i da jindadi da suka 6oye shekarunshi. Kallonshi yake tun daga sama har zuwa kafa, so yake ya gano ta inda ya fishi har Salma ke mishi murmushi haka. A zuciya yace "Babu... Sai dai kud'i kawai da sa kaya masu t'sada. "Kai fa,daga ina ba koh sallama?.. Cike da haushi ya kallota, "baki sanarshi ko ni waye ba ne?.. Kan Alhaji ya dawo,ba shakku yace "matata ce ita,zaifi mana k'yau in ka daina zuwa gunta Alhaji. Murmushi yayi Alhajin,kan ya kallo Salman, "sai kinji ni kawai.. A takaice ya k'alli Ja'afar din,ba sai an fada mishi waye ba,halamu ya nuna tsohon mijinta ne,har zaga wa tai ta rufe mishi tana daga mishi hannu d'auke da murmushi, har ya kule tana daga mishi hannu kan ta d'au kayanta koh ta kanshi bata tai hanyar gida,da zafin nama. "Wato abinda ki ke kenan tun bayan tafiya ta shine yasa ki ka kashe waya? Salma mey yasa kike son ki 6ata min rai wai?.. Jibi fa shigar ki,ji gashi a waje,wace iriyar rayuwa ki ka za6a mana? Cike da fada tace "Wace iriyar ka za6arwa kanka dai Ja'afar.. Ya zaka zo kana fad'an wata iriyar magana mijin da zan aura?.. Karan nan bazan dau abinnan naka ba wallahi, aure zamuyi dashi nan da wata biyu... Sai kayi abinda zaka yi. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 36_Kan yai k'wak'waran mot'si ta shiga gida tare taru kofa harda sa sakata. Jiginna tai hawaye na neman zubo mata,daga yar bular dake jikin kofar ta leka waje,kofar gidan yake kallo jiki a sanyaye kamar yasa kuka,juyawa tayi hawayen dake makale mata ya zubo,dak'yar ta seta kanta ta shiga ciki rai cike da tausayin Ja'afar. Kusan kullum zai zo ba zuciya dan bata baki akan Alhaji tana mishi wulakanci,shi kam Alhajin har dariya yake bashi wani sa'in, dan baijin da abinda zai iya rabashi da Salma a dai dai lokacin nan,sai dai jin saki uku ne kawai sai ya bar jin komai,iyaka ma yai ta tusa ma Ja'afar din bakin ciki in ya gansu da kalamai ma Salman. Biki ya karato ga makaranta,amma haka duk week end daga Zaria zai zo kan batun Salma ta janye zancen bikin nan. Duk ya fita a hayyacinshi duk akan auren Salma. Da halamu ya fara hankalin daina zuwa gun Alhajin,sai dai in yazo ya tsaya chan gefe sai tazo shiga ya tare ta da magiya. Yau saura k'wana biyu biki, sai gashi shi da Garba,dawowarsu daga gidan g'yaran jiki kenan ita da Ummi. Turus ta ja ta t'saya ganin Ummi ta wuce ita ya tare mata hanya. "Ka ga yau bani da lokacin jin wannan mahaukatan zantukan naka,jibi iyanzu na d'aura aure, ya kamata kasan inda dare ya maka, sabuwar rayuwa zan fara,saboda haka kai yanzu ya rage ma,danni yanzu baka gabana... Kai ya kad'a mata, "Karan nan bazan hanaki aure ba Salma,sai dai ba da Alhaji ba. Baki sake take kallonshi, Garba ya nuna, "Garba zaki aura Salma,kimin wannan alfarmar. Kai ta dauke daga kallonshi ta k'alli Garban wanda shima ya cika da al'ajabin kan maganar Ja'afar. Sai ta girgiza kai da murmushin takaici. "Tanan kuma ka bullo min?.. Auren kisan wuta Ja'afar? Lalle kayi nisa ba zakaji kira ba. Bayab hannunta tasa tana goge hawayen idonta. "Wai ka zata ni din auren kisan wuta zanyi da wanda zan aura?.. Kai ta kara kadawa, "Kai kuskure toh,dan ni aure zanyi na tsakani da Allah,ba wai nayi na fito ba Ja'afar.. "A'a Salma,ba haka ne nufi na ba.. Da muryar kuka ta tareshi, "Hakane man,haka kake nufi,wato ka kawo min abokin ka na aura bayan wani lokaci ya sake ni sai ka halartawa kanka ni koh?.. Baki sake duk suke k'allonta,ganin yadda hawaye ke zubar mata. "Jahilcina bai kai nan ba Ja'afar, a bazan ta6a abinda ka ke so ba, a gareni yanzu k'allon Yaya nake ma,da kuma uban yarinyar dana haifa, bayan haka.. Kai ta girgiza, kan tace "you mean nothing to me a yanzu kam.. Jin baice komai ba yasa taci gaba. "Banzaci haka daga gare ka ba Garba,a ganina in shi ya 6ata kai mey dawo dashi kan hanya ne, wallahi auren t'sakani da Allah zanyi, ku sani kuma auren so zanyi,wanda nake fatan mutu ka raba ne,dan Allah,dan kaunar ka da Allah ka bar bibiyata,dan Allah.. Shiru tai dan ganin shima idonshi ya taru da hawaye,da sauri ta shige gida tana goge hawaye.. Har ta shige yana binta da ido ba magana, sai hawayen da ya zubo mishi shar, da sauri yasa hannu ya share. Kafad'arshi Garba ya dafa, "kaji zancenta, tai mana fassara baibai,ya kamata kai hakuri ka bar kulata in har kana wa Allahn data had'a ka dashi. Kai ya daga, "InshaAllah.. ~~~~ Taro ne iya taro,taron shedar auren Salma da Alhaji Usman, daga inda yake t'saye a chan nesa da kofar gidan yana k'allon komai har aka shafa. Juyawa yai da jaka biyu hannunshi tare da sanya bakin glass dan 6oye sirrin dake idonshi. Yasan yanzu kam Salma ta mishi nisa. "Mama taki ta bud'e dakin fa,daga ina jiyo sautin kukanta Allah. Ta window Ummi ta leka,gata k'wance ta tasa tsohuwar wayarta a akan fuska tana razgar kuka, So ba karya bane Salma. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 37_Har aka kai amarya gidanta bata bar kuka ba,dayawa sun zata kukan na Mama ta cire Miemie ne, dan basa ji koh auren farkonta tayi haka. Kowa ya wat'se sai ita kad'ai, ko'ina take kallo a dirare, gida ne iya gida,tun bata fita ba ta zaga,yau gata a gidan da ba Ja'afar, ba kuma Miemie,tuni ido ya cika da kwallar tuna baya. Anya tai ma Ja'afar adalci kuwa?.. Anya bata ci amanar so ba kuwa?.. Ta sani da takai Ja'afar bango,hakan yasa bai kara waiwayarta ba,ta yuwu yai zuciya... Ido ta goge da sauri jin motsin za'a bud'e d'akin. Ango ne yasha babbar bunjima da rike da leda, bakin nan har kusan kunne,jan mayafinta ta kara yi ta rufe fuska. "Amarya! Amarya!!.. Ba k'ya laifi wai koh kin kashe dan maigida koh?.. Murmushi ta k'akalo mishi, zama yayi a gefenta tare da ajiye ledar a gefen bedside, bata aune ba taji ya yaye mata g'yale yana kallon fuskarta. Alwala yace ta d'auro suyi nafila,dan wai agareshi babbar kyauta ce ita daga Rabba. Sun gabatar da duk wani al'ada,sai dai har ango ya d'ane gado amarya tana t'saye a gaban madubi sai sininiki take,gabanta sai mugun fad'uwa yake tamkar wacce tai auren fari. Murmushi yayi da kanshi ya taso ya karaso har gaban madubin tare da kamo hannunta. "Muje ki kwanta haka dare nayi sosai.. Kamar yarinya ya kwantar ta gefen shi yana kallo da murmushi. Salon ya sauya,tuni ta fara digar da hawaye,shi kadai yake kid'anshi yana rawarshi,sai dan sautin kukanta dake fita kad'an-kadan,wanda a gareshi tamkar zigi take mishi. Kai ta juya ta kallo Alhajin dake bacci hankalinshi k'wance,abu uku sun hanata bacci,na farko kukan zamanta ta wani ba Ja'afar ba,na biyu tunawa da Miemie, na uku minsharin Alhaji.. Har gari ya waye bacci sai jefi-jefi-jefi ke dibanta,sam taki jinin minshari kusa da ita,tsaf yake hanata bacci. Shikam da farin ciki ya tashi irin na sabbin ango,ita kam da ido kawai take binshi. Tara sai ga yaron uwargida ya kawo abinci,da fara'a ya gaida ta,kanshi ta shafo kan tace ya sunan shi? "Sunana Ja'afar".... Kallonshi take da mamakin jin sunanshi, koh dai bataji dakyau bane?... Kat'seta yai da fad'in "K'anwata kuma Nabila,Umman mu tace sai anjima zamu shigo kar mu tashe ki a bacci. Murmushi tai mishi yace ya tafi.. "Ja'afar... Ido ta rint'se jin maigidan ya kira sunan,ba shiri ta d'au abincin tai kitchen. Bayan sun gama komai yace suje bangaren uwar gida zai magana dasu. Batai zatan da kishiyoyi masu kaunar kishiyar su ta ra6e su sama da matar Alhaji ba,sosai tai mata bazata,tun tana d'ari-d'ari har ta saki jiki da ita da yaranta, musamman Ja'afar.. Yau Miemie ce tazo mata,sai murna take taga Auntyn ta. Duk babyn ta rame,yaye bai amsheta ba. ''Miemie, ga nan Abdul yazo ku tafi gun Mama koh?... Kafad'a ta make halamar taki tana neman kuka, "Yi hakuri gobe zanje gida mu taho koh?.. Kuka ta saka mata baji ba gani, sai mak'e kafad'a take tana ita "um-um. Sai ta sallami Abdullahi kan gobe yazo ya d'auke ta, har ya jima da tafiya Miemie bata bar kuka ba. Sai um-um kawai take fad'i, suna haka Alhaji ya shigo,duk yai kicin-kicin da fuska, cikin fad'a- fad'a yace ta lallasheta man,shi baison hayaniya bare ta yaro... Baki sake take kallonshi,kaya ya ajiye ya juya ya fice harda dan tsakinshi,toh mey yake nufi?... Y'arta ta d'auka ta sa6a a baya sukai kitchen tana fad'in tai shiru ba inda zata toh,kan aje ko'ina sai ga nan Miemie harda dariya tana bata labarin Mama cikin gwaranci. Har dare ba Alhaji ba duriyarshi,abinci ma sai Ja'afar ya turo ya d'auka. Suna k'wance Miemie sai k'allonta take,gani take kamar guduwa zata yi ta barta. Kanta ta shafo tana mata murmushi, "Yi baccinki my Miemie, ina nan fa tare da ke kinji?. Kai ta daga mata tana k'allonta. "Antee... Kai ta dago kan tace "Na'am Miemie nah... "Abba... Tsam tai tana k'allon Miemien,Abba? Ta nanata a ranta. Murmushin dole ta k'akalo tana fad'in Abba yana nan Miemie,bata aune ba taji ta kara fad'in Abba... Hawayen da take makalewa ne suka zubo mata,da halama yanzu Miemie ce matsalar ta,dan zata dawo mata da hannun agogo baya. Da dabara ta d'auke hankalinta daga tunanin Abban ta hau lalla6ata har tai bacci. Photocopyn Ja'afar ce Miemie,barin yanzu data kara girma, tunani take koh dai Ja'afar har yanzu baya zuwa gida, laifinta ya shafi Miemie? Dan tasan sai Miemie ta kwana biyu bata ganshi ba take nemanshi haka. Tana nan har maigidan ya shigo,sai wani k'allo yake aikama Miemie wanda ta kasa fassara shi. Tun daga ranar ya zamana in dai Miemie zata zo,toh fa zata rasa gane kan maigidan, ta rasa dalili, musamman in tai la'akari da hadithn hausawa na Duk mai son uwa toh yaso d'iyanta. Ranar har ta kasa d'aurewa tai mishi magana, amsar da ya bata ta jima tana sata hawaye. Ga Miemie da kulafuci bare tace kar a sake kawo ta,asalima duk randa tazo fara'arta karuwa take. Sa6anin in tazo mata,data gane sai take d'akko ta duk randa bata da girki su k'wana, ranar da maigidan yake da ita su wuni ai rabuwar kuka har uwar. Allah yaga Miemie kadai take gani taji sanyi a ranta. Ranar suna fira a bangaren uwar gida take mata korafi kan halin maigidan akan Miemie. Murmushi tayi kamin tace "Sai kinyi hakuri da halin Alhaji Salma,ba tone- tone ba,a'a kawai dai ya kamata ki sani, Alhaji sam baya son yara,musamman hayaniyar su,hakan yasa ya d'aurawa kansa kin haihuwar k'arfi da yaji, nayi ta zaman takaicin halin nan na Alhaji har t'sawan shekara bakwai,a lokacin aka tada kayar baya kan sai ya kara aure tunda ni sun zuba ido shiru. "Hanna ta shigo itama ta shekara biyu shiru, ni dai nasan kusan kullum yakan tasa ni da Hanna dan shan maganin daukan ciki. Ana nan ranar wata kawar Hanna tazo suna jajanta ko dai matsalar gun mijin ce,toh a ranar dai asirin Alhaji ya tonu,dan kawar Hanna taga magani tace na hana d'aukar ciki ne. "Ranar muka mishi tawaye har Hanna,in takaice miki yace shi bai shirya haihuwa ba yanzun,anan sukai baram-baram da Hanna ya bata takardar ta. "Haka sauran mata biyun kowa tazo zai fad'a mata ra'ayinshi, da taga bazata iya ba zata fice, duk kuwa da tarin arzikin shi,a lokacin muna da shekara kusan sha uku da aure,koh mai zaiyi na daina shan magani, hakurina ya kare,nan na kai kara gun Hajiyarshi. "Ya saduda muka haifi Ja'afar, yace daga nan ta isa haka,wai incigaba shan magani,a gabanshi zanyi kamar nasha, daya kauce zan zubar. Koh shekara Ja'afar bai ba na samu cikin Nabila,cikin da a kullum sai naga tasku gun Alhaji,gar da gar zai nuna bai kaunar su,barin in Ja'afar na kuka,haka nai ta hakuri har na haifi Nabila. "Yanzu kam magani sai dai shi yai tasha,amma banda ni,kinga Nabila har ta shiga shekara ta biyar. Tsam tai tana tunani bayan kammala bata labarin waye Alhaji, ita ba kullen ne yafi damunta ba sama da rashin son haihuwa.. A kalla yanzu ta doshi wata na biyar a gidan nan amma ba bayani,sam bata kawo wani abin ba,ashe wannan ne dalili?.. Bazata iya tuna ranar fitarta ta karshe a gidan nan ba,tun kwa bayan aure sau daya taje gida sai dai aukin waya koh azo mata, lalle duniya labari. "Zaman hakuri kawai zamuyi Salma,sai adu'ar shirya in da rabon zai gane, amma shawarata gareki ki rike y'arki, dan kar kiyi sakiyar da babu ruwa tun kina yarinyar ki dake,shi ba ruwanshi. Kai ta kad'a mata,Allah sarki Ja'afar, ta tuno lokacin data fara period tana kukan samun ciki yana murna. Ta tuno da abinda yace mata "Allah sa Miemie ta samu k'ani a kusan nan... Ta tuna data hau bori ya hau lallashinta, harda alkawarin shi zai mata reno in bata shirya ba... "Ba kuka zakiyi ba Salma,muyi ta adu'a. Hannu takai fuskarta, ashe kuka take bata sani ba. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 38_Ranar sakwa-sakwa ta yini tana tuna halin Alhaji, bai da mugun hali koh daya sai na bakin kulle da kin yara,bayan nan baza tace ga mugun halinshi ba. Zataso sanin wane hali Ja'afar yake ciki a yanzu,dan tabbas tasan ya zuciya da ita,tunda gashi ance koh wajen Miemie baya zuwa sai aike?.. "Mey nai kenan?.. Mey nayi ni Salma?.. Mey yasa ban iya jure zama ba aure ba a rayuwa kamar yadda yaso muyi..mey yasa?.. Juyi tayi tana hawaye, Kila rabon Miemie kadai take dashi a duniya,tasan kuma aure dai ana yinshi ne dan abu biyu,samun zuri'a na daga ciki, gashi ita anan ana son a haramta mata. Tabbas d'aukar y'arta shine babban mafita a game da yadda take jin son ta haihuwa a yanzi.. Wayarta ce tai ruri, a hankali ta goge hawayenta ta tashi, "Billy" taga a rubuce. Da sauri ta saita kanta kamin ta daga. "Sarauniyar kirki kina gida ne?... Dariya ta danyi kan tace tana nan.. "Toh ina kofar gidan ki yanzu haka. Da sauri ta tashi dan g'yara fuska tana fadin gata nan zuwa. Sai da ta tabbatar da ba mai gane tai kuka kamin ta fita kofa shigo da Billy. "Matar nan kinganki kuwa?.. Kin zama big madam da gaske fa. Murmushi tayi tana kar6an Ilham. "Kai Billy banda fa sharri.. Dariya tai tana "ba wani sharri, koh dai mun karu?.. Miemie tayi k'ani? Shiru tayi tana murmushin iya le6e. Bayan sun gaisa take ce mata ai daga wajen Miemie suke,tai ta kukan zata zo tana jin tace gun Auntyn ta zata. Murmushi tai tai kasa da kai,Allah sarki Mimi. "Yau Miemie aka kaima ziyara kenan?.. Murmushi Billy tai kan tace "ai duk sati sau biyu Abban Ahmad (Garba) ke zuwa dan dubo ma Abban Miemie lafiyarta. "Shine yau muka je tare,Miemie akwai wayo,kusan wata shida amma bata manta Abbanta ba,tana jin muryarshi a waya ta fara murna.. Shiru tai tana nazari,ba dai ace tun tafiyar Ja'afar ya zuciya ya bar garin nan ba?.. "Ja'afar kanar wasa,kinga wata shida muke nema yaki waiwayo mu,sai kulafucin a dubo mishi gudan jininshi... "Rayuwa kenan fa,kana naka Allah na nashi,in kai hakuri sai ka ga na Allahn ne dai dai a gare ka. "Amma Abban Miemie namijin duniya ne,mai ra'ayin kanshi,tunda ya jima haka nasan alhinin aurenki ne bai sake shi ba. Shiru tai tana jinta,a hankali ta fara jin nadamar wulakancin data kartawa Ja'afar, Abban y'arta. Yau Billy ta kawo fitina,dan har ta tafi bata da sukuni,har sai da ta tiki kuka son ranta taji dad'i,yanzu burinta Miemien ta dawo gare ta. Koh da maigidan yazo yaga yanayinta yasan tasha kuka,da ya tambaye ta sai tace Miemie take son gani ta d'akko ta. Anan ya tada mata bori,har sai da tai da na sanin maganar Miemie. Ba abinda yafi kona mata rai sama da yadda tanaji tana gani yai mata haramiyar makaranta,sannan Mama ta goya mishi baya,abu goma da ashirin sun had'e mata. Adaddafe akai shekara, lokacin tuni ta jima da d'akko y'arta,dan bazata iya da rashinta ba a irin yanayin da take na son yaran nan. Sai sai wani abu,fur Miemie taki jinin Alhaji, ko abu take in zai kwan dubu yana ta bari bazata koh k'alleshi ba,asalima har wani kumbura baki take in ta ganshi,Salma tai magana tasa mata kuka,ga bala'in Alhaji na wai yarinya tun kan ta girma ta rainashi shi da gidanshi, har harara wai take mishi... A tunaninta kamar Miemie wane harara ta sani bare wai kumbura mishi baki?.. Amma dan a zauna lafiya yasa kullum take kwa6ar ta. A gaban kowa har su Nabila zatai wasa harda k'yak'yatawa, amma fa koh a nan bangaren taci ka'ro da Alhaji zata d'unkume,tamkar ba ita ba,shima kwa da harara zai bita, wani sa'in harda t'saki.. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:33 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 39_"Aunty A'i na rasa yadda zanyi ne,yadda yake nuna t'sanar Miemie karara yafi damuna,abu kadan tayi sai ya hantara,t'sawa, ga kullum yai ta surutun wai tana hararar shi,koh fa wai turo mishi baki,nawa take fisabilillahi?... "Allah bansan haka agolanci yake sai gun Miemie. Murmushi tayi "bari muga,ke dai sa ido... ta kallo Miemie dake chan gefe tana mota da motar wasa. Da k'arfi Aunty A'in tace "ke Miemie... Rai had'e, itama ta dago tare da 6ata rai tana kumbura ma Aunty A'in baki. Sai Aunty A'in tai mata murmushi tare da mika mata hannu, "zo Miemie naga kitso, waya miki?.. Kafad'a ta make halamar bazata zo ba kenan. Cikin wasa Aunty A'in tace "haba Miemie ta,zo zan baki sweet fa.. Da sauri ta taso har tana dariya ta d'are ta tana kiran sweet. Baki sake Salma take k'allonta,Allah yaga banda yau ta gani da idonta bazata yarda Miemie zatai haka ba. Gira ta daga ma Salman halamar ta gani ai. Miemien na fita tace "Ikon Allah Aunty A'i, ashe dai gaske ne Miemie na mishi hakan. Kai ta kad'a, ''amma in ya mata irin yadda na mata,kila koh wasa take yana mata ne,yaro kamar Miemie dan lallabi ne,shi yasa tun farko banso kin karbi yarinyar nan ba Salma,gudun irin matsalar nan.. Ba magiyar da Abbanta bai min ba shima a waya kan baison ya'rshi ta zama agola, Gashi in bakiyi wasa ba shi kenan ta gama raina miki miji. Cike da damuwa tace "Nikam ta rufan asiri karta kashen aure Allah.. Dariya Aunty A'i tayi,lalle ma Salma,wai karta kashe mata aure? "Haba dai ke kuma,sai kace wata babba,kawai dai ita tata salon fad'an ne haka,amma zata daina. Ajiyar zuciya ta sau,kan tace "Bazaki gane ba Aunty A'i,wallahi in Abban su Nabila zai kwana yana cewa Miemie bari koh kallonshi bata yi,wannan nasan tana dashi,shi kuma sai ya kule,baya duba yarintarta,sai ma ki ga ya hauni da sababi. "Toh ki dinga sata misali kai mishi abu haka,kina kuma kula d yanayinta in yana mata magana,sai kina sata a hanya. Har magriba suna abu daya,matsalar gida Alhaji har ta tafi. Washegari a ita ke da shi,tun wuri ta shirya Miemie ta d'auke duk kayan 6arna duk dan a zauna lafiya. Chankula chankoto take mata tana dariya,ta sunkuya tana mata "aci ladan gabe" tana dan mata duka yai sallama. Kallo daya ya musu ya d'auke kai, dagowa Miemie tayi,in ba idonta ke mata gezau ba kamar harara ma ta mishi,tuni ta gintse fuska ta daina dariya. Ya salam, Miemie tai nisa a tsanar Abban su Nabila. Yake tai kan ta tashi dan binshi d'aki, "Miemie tashi muje gun Abba koh?... Kafad'a ta mak'e tana turo baki, sai tai kamar bata gani ba ta kinkime ta,a ranta tana fad'in "sai nayi da gaske a kanki Miemie. Ihu ta fara tana zazzamewa,a dole ita bazata je ba,jin suna iyowa dakin yasa da sauri yace "Kar ki shigo min kina min wannan kukan dama.. Chak ta tsaya tare sauke ta,kafadar ta kara makewa tana kallon Salman,sai ma ta fita tayi bangaren su Ja'afar. Kai ta dafe tana mai mamaki ita kam,Miemie,toh mey take so da ita?. *DAN KUKA...* ************************** Dube yake zai k'alli news amma baiga d'ayan remote ba, ga Salman ta shiga wanka, Kamar ance diba hannun Miemie dake chan gefen corridor tana wasa sai ga shi kuwa,yau shine motar ta ma. Da zafin nama ya tashi ya nufi gunta.. "Jiyinnnn" take dashi cikin tsawa yace "Wannan ne abin yin motar?.. Dagowa tai tana t'sareshi da ido cikin had'e rai, "Bani nan ni labarai zai wuce ni sarauniyar 6arna. Kafad'a ta mak'e mishi tare da yi da remote din bayanta tana zunguro mishi da baki. Cikin zafin nama ya dagota, dai-dai fitowar Salma dan jin fad'anshi, binta yake daga zaunen tana matsawa taki bashi,kawai sai ya fizgota da niyar kwata ta tun karfi, kai cikin fushi ta kwada remote din a kasa tana kuma mishi ihun kukan ya hanata wasa.. Dagashi har Salman suka bi remote din da kallo wanda kowanne part yai nashi gun battery ya cire. Da sauri Salman ta karaso ta kwada mata mari,sauke ta yai kasa yana sababin ai wai ita tasa ta raina mutane yai waje,k'allon da baiyi ba kenan ya fice. Harara ta kwada mata kan ta kamo kunnenta ta murde tana kuka, "Baki isa ki chazan matsala ba ja'irar nan,wato bakin hali ki ke son kowa koh?. Kashen aure zakiyi ne?.. Kullum baza'a aji kanmu da mijina ba sai akanki?.. Cikata tai tare da dan rangwashenta, "Toh baki isa ba,dole kizo ki koma gurin Mama koh dangin Abbanki da zama... Bata karasa ba Miemie ta fad'i tana burburwar fad'in taki,ita bazata ba. Ido kawai ta sa mata,kan tai kwafa tai d'aki,da gudu itama ta bita tana kukan bazata ba Salman ta rufe kofarta ta batta da bugun "Antee,Antee bata cho. Anan tai ta mitarta tanaji daga dakin tana "Ai sai kinje... Tuni ta kara jiniya, kuka harda shudewa amma tai burus da ita tana kwalliyarta. Zuwa chan taji shiru,sai tai murmushi, Miemie matsala. Fito wa tai dan ganin koh fita tayi,sai ta ganta kwance bakin kofa sai sauke ajiyar zuciya take tai bacci. Sunkuyawa tai ta leka,ido har ya kumbura, duk sai ta bata tausayi,batasan lokacin da ta d'akko abarta ba,batajin tunda Miemie take ta ta6a dukanta haka tai kuka. Kwantar ta tai a gado tana goge mata fuska da tissue,baki ta kai fuskarta, "am sorry kinji... kamar ta sa kukan itama,Miemie taurin kai toh,Alhaji hancini,ya suke so tayi da ranta ne? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:34 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 40_Washegari bayan la'asar tace mishi zata maida Miemie gidan Mama dan Allah ya batta taje daga nan sai tai barkar Ummi data haihu cikin dare. Da har zai hana,ganin kayan Miemie a akwati yasa bai gardama ba ya batta,kwarai tasha mamaki,dan rabonta da fita har ta manta,amma dake wacce bai kauna za'a mayar ya batta. "Ga driver in kin gama ya kaiku,kar kuma ki dad'e.. Kai ta daga tace ta gode. Rayuwa kenan,da ya batta ma taji dad'i,koh ba komai zata leka gida yau. Gidan Ummi suka fara zuwa,sai ta6e baki take tana korafin yadda ta zama matar k'ulle. "Aure sama da shekara wannan ne zuwanki na biyu gidana,wannan wace iriyar rayuwa ce,mutum sai shegen kullen t'siya.. Tana jinta tai shiru,tana tunanin hali irin na dan Adam,mai wuyar gane hali,lokacin Ja'afar mai barinta fita haka ta gurza,yanzu kuma ta had'u da dai dai kowa,ga kud'i ga cima, amma ba fita ba haihuwa.. Zaman lafiya wai yafi zama Dan Sarki. Ita kanta Miemie murna take sun fita yau,sai dai suna zuwa gidan Mama taji Salman na maganar zamanta ta d'ane cinyarta ta riketa tam. Ban6are ta Mama take ajikinta tana ihun kiran Aunty,ita kuka Salma kuka, ga magriba ta sawo kai. Suna haka Abba ya shigo, duk ta rike gyalen Salma kam tana ihu. Dak'yar ta fizge tai hanyar fita da gudu tana kuka. "Subhanallah... Ta shid'e fa wannan... Chak ta tsaya jin daina kuka Miemien,da sauri ta juyo taga Abba na jijjiga ta. Ba shiri tai gun dai dai Miemien ta kawo wuta ta kar6e ta. Kuka na fitar hankali take tana bata hakuri, ''Ni bansan mey yarinyar nan zata tsare miki ba in ta zauna achan gunki ba,kullum sai da kuka koh jinya za'a rabu?.. Ki bar y'arki a kusa dake man tunda ita mai kulafuci ce... Kai ta daga tana share ma Miemien hawaye tana tai shiru toh.. Dole tana ji tana gani ta koma da Miemie, dan yau fir taki yadda tunda ta d'andana zama da ita. Kanta take shafawa,ita kam ta tasata gaba tana ta kallo ba koh kiftawa. A hankali tace "Miemie.. Idonta a kan Salman tace "Uhmm. Kwanto wa tai a gefenta tana g'yara mata kwanciya, kamar wata babba ta fara mata fad'an ta zama mai ji dan Allah. "Ban san matsala Miemie, ki rufan asiri ki daina halin nan naki na kumbura ma mijina baki,kinji?.. Kai ta daga mata kamar gaske. Sai tai murmushi tai kan tace ta taso suje suyi girki a kitchen. Shikam Alhaji da murnar yau Miemie ta tafi ya shigo gida,shi kanshi ya rasa mey yarinyar ta tsare mishi a gidan,duba ga su Ja'afar na gidan. Sai dai tun daga bud'e kofar parlourn farin cikin ya kau. Dariyar Miemie ya fara cin karo yana shigowa ta kitchen,dan haka da sababi ya isa. "Mey ya zaunarki har bayan magriba baki dawo ba?... Mey kuma ya dawo da wannan? Duk ido suka zuba mishi,mai hali kuwa Miemie tuni ta chunno baki gaba tana mishi wani irin kallo jin ya fara sababin nashi. "Wallahi har kusan suma tayi dan kuka yau,tausayi ta bani shine na dawo da ita,kai hakuri duk ita tasa muka kai magriba. K'allon Miemien yayi da kamar harara kamin ya kad'a kai dan takaici ya fice. Ajiyar zuciya ta saka,ta tsalake rijiya da baya da k'yar,kan ta dawo kan Miemie ita tuni har ta cigaba da sabgarta. Sai dai ana zuwa kwanciya yace daga yau Miemie zata bar kwana dakin su,koh ta koma kasa. Ya ta iya,dan a zauna lafiya ta sauke Miemie kasan,dan ba yadda za ai ta luluka yarinya chan wani waje ita tana wata jahar,a ganintq Miemie nawa take. ******* Fur yanzu ta daina ganin fuska gun Alhaji, in ya shigo ba wanda ya isheshi kallo,asalima ya daina zama bangarenta sai cin abinci koh bacci. Yau dai ta d'au damarar fara koyawa Miemie sabo da Alhaji. "Abba ki ne kinji Miemie nah?.. Ki dinga mishi oyoyo kina mishi dariya kinji?, banda harara,banda turo baki,kina ji na? Shiru tai tana binta da kallo kawai,chan sai ta yak'e mata hakori. Cikin farin ciki Salman tace "yauwa,koh ke fa,be a good girl ba? kai ta daga mata tana dariya. Alhaji yai wanka ya shirya yaje parlour yana duba abu a system nashi su kuma suna daki gun shirya Miemie. Daga parlourn ya kwada ma Salma kira wai ta fito mishi da agogon shi na kan mirrior. Murmushi tai ta k'alli Miemie,tasha parking da ribbon sanye da gown ja da baka iya g'wiwa, dake fara ce sai tai mata k'yau sosai. Agogon ta d'akko ta kamo hannun Miemie, "Kai ma Abba a maza yana parlour,ki nutsu dan Allah kinji Miemie nah.. Kai ta daga tana dariya ta karbi agogo tai parlour. Bayanta ta biyo dan ganin ya zata kaya, daga yau ne zata fara koya musu kusanci da juna shi da Miemie. A dunkume ta isa gunshi yana duba abu a laptop, mika mishi tayi ba koh magana, sai ya dago ganin itace,tai mishi kyau sosai,ga sai kamshi take,ba abinda ta bari na babanta a ganin shi har dacin ran,in baxai manta ba yanzu ne zata shiga shekara uku,amma duk ta tara dacin rai wai da fitsara. Kai ya d'auke ya cigaba da abinda yake, Salma har ta fara murna ganin bai mata dan halin ba yau. Ita kwa Miemie sai ta ajiye agogo kan hannun kujera ta juya tsautsayi agogo ya fad'o kasan tiles sai glass din ya fashe. Da azama ya juya,ganin agogon akasa a fashe Miemie ta juya ta mike ya fara sababi. "Duk wani mugun hali irin na ubanta yarinyar nan ta iya,agogon nawa zaki saka da gangan ki fasa min?.. Waje Salma ta fito ganin ya yo kan Miemien a sukwane, duk tana k'allon abinda ya faru. Kumatun Miemien ya ja tare da kai mata rangwashi akai yana sababi,tuni ta hau kuka jin zafin abin,da sauri Salman ta karaso dan bashi hakuri. "Shegiyar yarinya kawai,kin san kud'in agogon da kika fasa kuwa?.. Ja Salman tai ta tsaya tare da rintse ido. Ga ihun Miemie tana kiran Aunty,ga sai zagin y'arta yake harda sheganta mata ita? "Alhaji.. Cikin fusata ta kira shi tare da bud'e, Rai 6ace shima ya dago da niyar huce haushin shi kanta ta rigashi. "A gaskiya ka daina sheganta min yarinya, dan da ubanta gaskiya,haka kawai, ina fa kallo tana mika maka ka d'auke kai,ta ajiye ya fad'o kasa,toh meye lefinta aciki har irin wannan zagi?.. A'a toh gaskiya... Kai ta kawar ranta 6ace. Cika Miemien yayi yana kallonta, wannan ne karo na farko da ya fara ganin fitsarar Salma,shi zatai wa tsawa akan Miemie? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:37 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 41_Da gudu ta karasa tana kama hannun Salman,d'aukarta tayi a ta sa6a a baya, "Yi shiru kinji.. Muje daki... "Kar ki kuskura ki shigar min d'aki da wannan yarinyar.. Chak taja ta tsaya tare da juyowa tana kallonshi. "Kema kar ki shigar min d'aki,ni zakiyi wa rashin mutunci kan y'arki?.. Toh baki isa ba,dan ba ayi macen da ta isa daga min murya ba ki sani. Cikin karfin hali tace "Toh mey ka ke nufi da hakan?.. Daga fad'in gaskiya?.. Haba Alhaji,Kullum ina fuskantar yadda ka ke tsagwamar yarinyar nan,shi yasa sam bata shiri da kai ai... "Ba wani nan,bakin halin yarki dai irin na tsohon mijinki dai,da kuma shegen taurin kanta irin nashi,koh kin zata na manta da waye shi zamanin neman aurenki? Da sauri ta tare mai numfashi harda sauke Miemie kasa da sauri, "Ba ruwan Ja'afar cikin maganar nan tamu,zai fi kyau in ka daina sakoshi ciki..kuma na fad'a maka y'ata bata da wani mugun hali,sai dai naka mugun halin rashin son yara, da kuma.. Shiru tai tare da ja da baya ganin ya zaburo kanta, "wallahi kar ma ka soma,dan ba yadda za ai in zuba ido kullum kana aibanta min yarinya wallahi, nawa Miemie take? Amma k'arfi da yaji so ake ta iya dan hali.. "Salma ni nake fad'a kina fad'a?.. Ashe baki da mutunci?.. Kai ta kad'a tare da juyar da kai, "Nikwa nake da mutunci tunda a cikin gidan ubana ka auro ni kuma... "Subhanallah,haba ku k'wa.. Juyawa tayi taga Maman su Nabila na shigowa dakin. "Tun ina shanya nake jiyo ihun Miemie da naku,bai dace ba Allah,kuna abu a gaban yarinya.. "Ba ruwanki cikin zancen nan,in ba so ki ke ya taso da kwantaccen naki ba ke ma.. Shiru taja bakinta tayi tuni idonta ya fara zubar da kwalla, ya cigaba "Yara nawa ma basa gabana bare ta wani, saboda haka akan yaro ba mai sani ciwan hawan jini,dole yau ki mayarta gun ubanta,koh ki san nayi da ita. Cikin kuka tace "Bazan iya rabuwa da y'ata ba,kai hakuri raina ne ya 6aci.. Malalacin murmushi yayi,kan yace "Daga baya kenan,amma dole ki za6a zaman dani koh da yarinyar ki... Maman Ja'afar ta kallo da itama ke hawaye tana kallonta,sai ta cije le6e da takaici. Juyawa tayi ta d'au Miemie, kan ta kalloshi ido na fidda kwalla. "Ni kam na kasance daga masu taya annabinmu kishin Al'ummar shi,dan haka ina son haihuwa,bi ma'ana zan iya rayuwa da Miemie kad'ai mud'in Annabin mu zai alfahari dani... Cikin zafin rai yace "Kimin hausar da zan gane Malama ni.. "Annabinmu yace kuyi aure dan ku hayaiyafa,domin go6e kiyama nai alfahari daku.. Kayi aure,amma baka fatan tara zuri'a, hakan yana nufin kana tarjiya a bisa umarnin manzon Allah.. A tunzure yai yo kanta, "Kimin shiru fitsararriyar kawai,koh yayarki bata isa ja ina ja ba wallahi, dole ne yau ki za6i d'aya.. Cigaba tai da batun ta ido rufe, "Nai ma biyayya ta t'sawan shekara guda ina bin yadda kaso,toh ka sani ni Sunnah na dauki aurena,kuma zan cikashi ne ta hanyar tara zuri'a, dan zanyi alfarhari idan na kasance a daya daga wanda Annabi zai alfari da ita... Mari ya de6eta dashi jiki na 6ari,da sauri ta dafe gun tare da bud'e ido,kuka Miemie tasa ganin an daki Auntyn ta, "Mutuniyar banza kawai,ni zaki mayar jahili?.. Murmushi tayi kan ta kad'a kai. "A'a,dan kuwa kafi jahili,danshi dama bai sani ba bare take,kai kuwa ka sani amma kana taya shedan rawa,dan baka kaunar.. Shiru tayi ganin zai kara mata wani,da sauri ta rintse ido tana hawaye,jin shiru bataji saukar mari ba yasa ta bud'e ido. Hannunshi rike a hannun Maman su Ja'afar, "Lalle lokaci yayi da ya kamata in tanka maka Alhaji,lokaci yayi da zan daina bin umarnin ka ina 6ata.. Ashe har alfahari ka ke cewar yaranka ma basa gabanka?.. Jiran amsa take tana kallonshi, da borin kunya yace "Cika min hannu... Ba musu ta cika, Salma ya nuno "Ke kuma ki tafi gidan ku,na sake ki saki daya,na koyan hankali,in kin koyo kofa a bud'e take ki dawo.. Ido ta rintse gabanta na fad'uwa, wai ya saketa?.. Daga fad'in gaskiya. Kan Maman su Ja'afar ya dawo, "Wato zuwan fitsararriyar yarinyar nan ta sa kin fara sauya hali Halima koh.. Kai ta daga da sauri.. "Kwarai kwa,dan yanzu na gane kuskuren dana tafka a zaman baya da nayi da kai, nima ina son zuri'a, ina son su Ja'afar sama da komai yanzu,kuma zanso wanda duk yake son su,zan kuma yi fad'a da duk mai kinsu, aciki kuwa harda kai usman... Baki ya saka yana mata k'allon mamaki "Usman?.. Babbar magana.. Halima yau ke kike kama sunana ba ma Abban Ja'afar bare Alhaji?.. Shiru tayi tana kallonshi,sai sababi yake daga karshe itama yace taje sai ya nemeta. T'saki sukai mai lokaci daya ita da Salma,duk da kallo ya bisu Salma tai d'aki. "Ai nima ka sallame ni kawai,dan bazan zauna da mutumin dake kyankyamin zuri'a ba,dole yau na barka,Allah ya yafen baya,amma yanzu kam ta kau,ka sake ni nima kawai... "Bazan saki ba,amma dole ki fuce min a gida,dan ba mai sa min hawan jini... Kuka Salman take tana jiyo sababin da Alhajin ke yi.. Hannu Miemie ta kai tana girgiza mata kai itama tana kukan,gaba daya ta rungumo y'arta tana kuka mai cin rai,ita kuma haka Allah yayi ta marar sa'a a zaman aure,gashi yau a dalilinta auren shekara sama da ashirin na neman tsinkewa bayan ta t'sinke nata. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:39 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 42_Jugum Abba yai bayan jin bayanin Aunty A'i,ita dai Salma sai kuka take,dan tasan yau kam sai ta Allah,fad'a kam sai dai ta toshe kunnenta. Amma da mamakinta sai ji tai ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Allah ya kyauta toh,dama tun farko ni mutumin nan ba wai ya mun ba ne. "Yadda naga kowa na yinshi a gidan musamman Babar taku yasa nabi yarima nasha kid'a, sai fatan Allah yasa haka shi yafi alkairi.. Mama ce ta riga kowa saurin fad'in "Amin,ni nasan naso shi,amma daga baya sam mutumin ya fice min akai,dan daga gani ba wai zaiyi wani mutunci bane,ga dankaran kulle,yanzu kuma an kara da rashin son haihuwa.. Dame yarinya zata ji?.. Kallon mamaki suke ma Maman musamman Salma, yau mama ke fad'in aibun Alhaji da bakinta?... Lalle abu ya 6aci. Da dare suna kwance ta tasa Miemie a gaba tana kallo,itama ido ta sa mata, tunaninta zancenta ya tabbata. A dalilin Miemie aure ya 6alle.. Murmushi tai kan ta gyara kwanciya. "Miemie.. Kai ta daga tare da fad'in "Uhmm.. Sai ta mirgino kusanta tai rub da ciki "Kina murna kuwa?.. Baki ta yage mata ba dan ta fahimci nufin Auntyn ba. Sai ta kad'a kai,ta rasa wane irin nishad'i ke shigarta da yamman nan zuwa daren yanzu.. "A k'ya kam yi murna,wato kin rabu da alakakai koh? Kai ta daga mata tana dariya.. Itama tana dariya ta fara mata chakulkuli su na k'yak'yata dariya har su Abba dake waje suna jiyo su. Mama ya kallo,itama shi take kallo, "kina jin mutananki koh?.. Kamar yau take Sallah.. Murmushi tai tana sadda kai kasa, sai ya girgiza kai yana tuna wani abu. ****** Tun daga wannan lokacin hankalinta ya koma kan makaranta, babban bakin cikinta bai wuce yadda Alhaji yai burus da maganarta ba,a ganinta in har da mutunci koh Abbanta ya samu da zancen.. Gashi a kalla yanzu ta kusa cinye kwanakin iddar ta. Duk suna waya da Maman su Nabila tace yana zuwar musu,sai dai ita baya samun ganinta. "Aunty!.. Aunty!!.. Da dan gudunta ta shigo gidan tana k'wada mata kira rike da leda tana ja,bakin nan har kusan kunnen Miemie. Kamar a mafarki taji kira ana ta6ata,a hankali ta bud'e ido dan bata jima ba da bacci ya debeta sakamakon ciwan period da take. "Uhmm Miemie.. Ya akai?.. Ledar hannunta ta hau bud'e mata tana mata magana duk a hard'e dan murna. Riguna ne y'an kanti masu kyau da tsada da takalma, sai teddy guda biyu da y'ar tsana mai feeder a baki. A zabure ta mike tana duben Miemien,tasan ba mai irin ma wa y'arta tsarabar nan sai Abbanta,yawu ta had'iye kamin tace "Miemie,ina kika samo kaya haka?.. Dagowa tayi kamin tace "Abba ne... Tsam tai tana kallon irin farin cikin da Miemien take,wato in zai shekara bata ganshi ba tasan Abbanta. K'allota tayi tana mata yake ganin yadda take cire feedern a bakin y'ar t'sanar tana fad'in Inya.. Inya. Da sauri ta tashi tare da zarar gyale tai waje. A kalla zataso ganinshi koh dan ganin yadda yake a t'sawan shekara guda da d'auri. Sai dai har ta gama leke bata koh hango mai kamar Ja'afar fa sai sawun mota. Zaure ta koma tana lumshe ido tare da dafe kirjinta. Babu makawa Ja'afar ya shigo zauren nan.. Dan ga nan kamshin turarenshi ciki tana iya shakarshi. Jiki a sanyaye ta juya ta koma cikin gida, a chan d'akin Mama ta jiyo karad'in Miemie na ba ma maman labari tana dariya. Da murmushi ta samu ta dan dosana tana kallonsu kamar ta sa kuka. "Na fuskanci yarinyar nan in dai tai arangma da Abbanta tana kwanan murna, haka kwanaki dak'yar na ban6areta jikinshi ashe bata manta shi ba tana kuka,shima harda y'ar kwalarshi yana daga mata hannu... Ido ta kurawa Maman ba koh kiftawa.. Ba dai Mama na nufin Ja'afar yana zuwa garin nan ba kuma har gidan nan?... Mama ce ta kat'se mata tunani da fad'in "Ban tunanin yaron nan koh a hanya ya ganni zai gaidani ba sam bayan aurenki, duba ga yadda na rika mishi fatattakar arziki.. Zuwan shi biyu gidan nan ashe makaranta ya koma kinji.. Murmushi tai Maman da iyakar shi le6e tare da daga kai. Tuni ta zurfafa tunani,har bata jin mey Mama da Miemie ke fad'a,kan ta farga har idonta ya cika da kwalla,da sauri ta juyar da kai tare da goge wa kamin su gani. Sakkowa tai tana taya Miemie rad'awa teddy suna suna dariya. Kallonsu kawai Mama take tana wani tunani, kai ta kad'a kamin ta tashi ta basu gu dan tasan Abba yana gaf da zuwa. Washegari da yamma tana kokarin shiga wanka akai mata sallama. Hijab ta zira harda shafa powder da zumudin Ja'afar ne ma,kila ya samu labarin tana gida. Turus tayi tare da chunno baki kamar Miemie ganin Alhaji da abokinshi. Baki ya washe mata yana fad'in ta karaso man kusa... Murmushin mugunta tai kan ta kalloshi "Dan bani minti biyar na fito a gida... Kai ya daga yana mata murmushi, ashe bazai yi wahalar shawo kan Salma ba kamar Halima. Ruwan da ta zuba na wanka ta d'auka da wani a buta dan tsarkake kai in tai wankan t'sarki. Tana yi tana murmushi har ta gama. D'aki ta shiga ta tsane kanta da towel kan ta dan shirya a gaggauce ta fita. Yadda take murmushi ne yasa Mama tambayar waye yazo, a tunaninta koh Ja'afar ne,tana cewa Alhaji ne ta 6ata rai. "Ki dai kama kanki ki saiwa kanki mutunci,dan sam mutumin ba nagari bane,kinjini ai? Kai ta kad'a tana murmushi, lalle Mama, yau Alhajin guda?.. Sai ta kad'a kai, "adu'a bata fad'uwa kasa banza. Bayan sun gaisa yake zungurar abokin nashi sarkin iya t'sari, duk tana jinsu tana murmushi dan feleke harda tambayar Miemie,sai da suka gama tass tana jinsu tana kad'a kai. "Ai yanzu na fita sahun matarka Alhaji,sai dai kabi sahun zawarawa na..dan nayi iddah ni... Fuska ya g'imtse yana kallonta, "haba kar muyi haka dake man,ina fa lissafi,yau watanki biyu da kwana uku rabonki da gida na, kinga ai bakiyi wata uku bare ace kinyi iddah koh ba haka ba abokina? Kai ya jijjiga yana fad'in "kwarai kuwa,dan haka muka sani a al'adan ce. Kai ta kad'a tana murmushin takaici, wato ga babyn roba,a hular a lokacin da akaso a d'auka a randa aka ga dama.. 6aro-6aro tai mishi dalla-dalla kan ita ai duk bayan sati uku take period, kuma ya sani sai dai ya take. A fafur yace shi baisan zance ba,kawai ya maida ta dakinta. Juyawa tai ta koma gida,tana ji sai kwad'a mata kira yake tai mishi banza. Da farin ciki ta shiga har baya misaltuwa, dan da yanzu dabarar yin wanka ba tazo mata ba da tuni ansha da ita an gama. "Ba dai ya maidaki ba naga kina murna tun yanzu Salma?.. Yanzu ke bazakiyi kishin kanki ba har kin bada kai daga fita bori ya hau?.. Ina laifin ya samo Abbanki da maganar in dai da mutunci aciki... "Au dariya ma na baki koh Salma?.. Ga shash.. "Mama ni fa ba aure a t'sakanin mu da Alhaji yanzu,dan tau nai iddah ta.... Baki sake take kallonta,dariya tasa ta bata labari,sai ga Mama na tikar dariya. "Lalle yarinyar nan da wayo ki ke,kwarai kinyi dabara, dan sam mutumin ya sane min, dan ban fad'a miki bane,ba'a fi sati da dawowarki gida ba muka had'u da dan talikinnan,d'auke kai yai kamar bai ganni ba fa,bayan sarai mun had'a ido.. "Shi yasa yaron nan Ja'afar nake ganin kimarshi har kullum,dan koh bayan rabuwarku yana daraja mu,musamman zai sa azo har gida abokinshi yai mana goma ta arziki in sun d'au Miemie... Shiru tayi tana sauraran maganar Mama, wai Ja'afar take ma ya6o haka da kirari?.. Farin cikinta a yau bai misaltuwa,ina Miemie na nan ta rad'a mata itama suyi tare,tasan dai duk inda take yanzu tana neman gida,dan tun dazu tai mata kwalliya da kayan Abbanta kaninshi yazo ya d'auke ta. Murmushi tai tana jijjiga kai. Lalle ne *Duniya Labari ce* By Feenat Ja'afar. feenat-jafar.my wapblog.com Feenat Jaafar's Mobile Blog feenat-jafar.mywapblog.com Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 9 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 43_Waya yake d'annawa a nitse yana duba sakon waya kamar bayaso,kamili ne,da hasken shi,sajenshi a yanzu shine sirrin 6oye kyanshi na ainashi, sanye cikin kananan kaya da glass manne a idonshi,da gani yana ji da ajinshi a dai- dai lokacin nan,dan miskili ne yanzu na karfi da yaji. A yanzu ne yake tsone idon y'an mata musamman na jami'a, dan ya iya t'sare kai da tsare gida. Rayuwarshi ta sauya,dan ya dawo ainashin halaiyar shi ta da,koma yafi da din, Ja'afar kenan,namijin duniya. Dago kai yayi yana duba yanayin garin da yadda kowanne shago suke hadahadarsu,sai ya sauke kai kan Abdull mai tahowa dauke da baby a kafad'a tana ta washe baki tun kan ta karaso. Tuni fara'a ta maye g'urbin rashin walwalar shi,kashe wayar yayi tare da ajiye ta gefe dan tarar gudan jininshi,duk Abba dake gefe kad'an yana kallo. "Abbaaa... Miemien ta fad'a lokacin da yake k'ar6ar ta,murmushi yayi mata tare da shafo fuskarta "Na'am Miemien Abba.. Sai ta washe baki. Ciro changi ya mika ma Abdull, "Kan magriba kazo ka maidata kaji?... Kai ya kad'a tare da amsa yayi godiya. Zama yayi tare da d'aura ta cinyarshi, Tasha kwalliya da rigar da ya yo mata tsaraba cotton ja da pink,kan nan kamar an mata shampoo sai kyalli yake yasha ribbons.. Hannu yakai kan dan beauty point nata ya latsa sai ta sa mishi dariya. A hankali shima yayi har hakorinshi suka baiyana. Tashi yayi zuwa gun Abba dan mishi sallama,kai ya kad'a Miemie na mishi bye-bye tana dariya. Kamar kullum nai yai ta yawo da ita suka sai ice cream suka nufi gidan Garba nan suka yada zangon su. Miemien Garban ya kallo yadda take tsalle kan Abban nata shikam sai murmushi yake mata. "Abokina ina so yau dai daya ka saurare batu na,sama da wata hud'u dana fara ma magana zaka ce a'a kai baka so.. Kallonshi yake jin inda yake neman dosa,tuni ya fara sauya kama. Ba tare da yabi ta kanshi ba Garban yaci gaba "Salma fa au... Cikin t'sananin fushi ya rufe ido tare da daga mishi hannu. "Dan Allah ka d'aina dawo min da hannun agogo baya,ina a cikin farina yanzu,banson jin sunan wata Salma chan.. Gefe yayi da kai yana chunkune fuska,kai Garban ya kad'a kan yai y'ar dariya, "Karyar banza kenan,yanzu da zance Salma tana gida an sakota da nasan ba wanda zai farin ciki a yau,kaine fa.. Baki sake yake kallonshi, "kana sanin abinda zaka fad'a man malam.. Matar mutanace fa yanzun. Murmushi yayi yana mishi k'allon bakasan komai. "Toh auren Salma ya rabu tun wata hud'u da ya wuce,sai ka kurbi ruwan sanyi ka huce.. Baki sake yake kallonshi ba koh kiftawa. Baya Garban yayi da kai yana shafa ha6a tare da daga mishi gira,ya dan jima a kame kamin ya d'auke tare da wayance wa. "Wannan bazai sauya komai ba kama ji da wai,dan ban manta abinda ta dirka min ba a baya.. Kama d'aina wata dariya.. Kafad'a Garban ya make,kan yace "Daga baya kenan kuma,chan ta matse ma,dan nasan yau sai kafi kowa farin ciki a garin nan,karyar kawai. Tashi yayi yana daukan Miemie tare da hararar shi, "Kanka ake ji,ni nayi kaga tafiya ta.. Dariya yai kan ya mike dan sauke su, "Kaima an kusa jin naka soon. Harara ya sakar mishi kan suka fice yana ta mishi t'siya. ***** "Mama zan tafi,a min adu'a Allah yasa kar na samu mat'sala kamar yadda principal yace.. "Amin kam, in Allah ya taimaka zasu karbi uzirin.. Kai ta kad'a, ''Amin toh, na tafi kan wannan ta farka. Da sauri ta fice ganin zatai latti. Allah yasota tana zuwa wata Napep zata tashi ta d'au wani da dan sauri ta t'sayar ta shiga ba tare da ta dubi na ciki ba. "Dan Allah ka taimaka school of... Shiru tai jin wani kamshi da ya bigeta,turaren da koh ajikin wani taji,toh mutum daya ke zuwa ranta. A hankali ta waiwaya dan ganin waye masanyin turaren. K'yam tayi tana kallonshi da murmushi ba koh kiftawa, shima hakan take,kan da sauri ya d'auke kai kamar ma bai ganeta ba yake nufi.. Dad'i ne..koh farin ciki a ranta a safiyar yau.. *Ja'afar* Wannan shine yaushe gamo. Kokarin mishi magana take yace da mai Napep ya t'saya. Ba musu yaja ya t'saya, da mamakinta taga yana kokarin sauka a Napep d'in, da sauri mai napep yace "Kazo gaba toh. Ba tare da ya kalle yace "Kai hakuri,bana shiga keke da mata... Gaba yai ya batta baki sake.. Kuturu,wa ya ga turnuku... Ji tai tamkar ta d'aura hannu a ka ta kurma ihu,wai ita Ja'afar zai haka?. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:44 AM - Queen Safiyyert馃憫: Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 45_Washegari kowa da farin ciki ya tashi kamar ma ance an shirya. Yau tana son ta koma Salmanta ta da ne. Yau shima yana son komawa Ja'afar d'inshi na Salmateen shi,dan haka tun wuri yaje yai g'yaran fuska,ya rage sumar kai,tuni ya hasko kamar zamanin angoncinshi da Salma. Gun Garba yaje yasha kwalliya kamar wani sabon ango. "Ya mutumina nayi kyau kuwa?鈥� banda shakiyanci pls. Daga sama har kasa yake kallonshi,yai kokakarin 6oye dariyar shi. "Kayi man,ina zuwa haka da sanyin yammacin nan haka?.. Da zumudi yace "gun Salmatee hayatee man. Da rashin fahimta yace mishi "wace haka?.. Harara ya sau mishi tare da fad'in "Ban sani ba, kaima ramawa zaka yin?.. Dan Allah ni taso muje.. Kai Garban ya juyar yana fad'in "ba inda zani bansan mace ba, haka kawai, Da zumudi yace "Salma ta fa,kar kace baka gane ba mana mun dinke.. Kunu yasha yace "ban gane ba,yaushe aka dinke?.. Koh ka manta kalamanka?.. Lallami ya fara yana kasa da kai,tuni Garban ya ware yana dillika mishi dariyar mugunta. Shi dai yau bata tashi yake ba,burinshi kawai su isa ga Salman shi. Yau d'aya ta zauna zaman kwalliya duk da bata da tabbas din ganinshi,har Mama na mata t'siyar ina zuwa?. Murmushi kawai tayi ta ciro wani arnan purple swiss tana kallo, shafashi tai tana tunano colorn da Ja'afar yafi kauna ya gani ajikinta. Riga da zani ne single, dinkin yai mata kyau tsam ya kama jikinta, da gaske yau ta fito a Salmanta. Tana daga d'aki ta jiyo yaro yazo wai Salma tazo,tana jin Mama na fad'in inji wa?.. Bataji amsar yaron ba taji Mama tace kace tana zuwa. G'yale ta rufa fari da ratsin flower purple tana k'allon kanta a mudubi,ina ma Ya Ja'afar ne man... "Ki fito ana kiranki a waje Ja'afar yanzu... 6ata rai tayi tana gunguni, "Ja'afar kuma Mama?.. Ni fa ba danshi zan fita ba fa.. Harara ta sakar mata,kan ta juya tana fad'in "magulmaciyar kawai,ni zakiyiwa alaye?.. Da gani shigar Ja'afar daban take gunki ai... Dariya ta kunshe kan ta kara k'allon kanta a madubi ta fita. Suna tsaye sun rike hannun Miemie da suka dakko chan gidan su jaafar suna mata y'ar dage tana dariya. Murmushi ta tsaya yi musu da sallamarta. Ido ya zira mata,yayinda itama take kallon sauyawarshi a yau kadai kamar sabon ango. Murmushi ya sakar mata yana daga mata hannu halamun tayi k'yau, da sauri ta d'auke kai a kallonshi tana cinkune fuska. Kai ya kad'a yana murmushi, karya kuma ai ta kare, tunda har shigarshi an mishi. Ha6a Garba yake shafawa yana kallon wani fulakon karya gun Salma da Ja'afar. "Kaganta ni dai ya kamata nayi fushi bisa abinda ta dibga min,amma kaga an dakeni an hanani kuka... Harara ta sau mishi,kan ta kau da kai, "lefinka ai dayawa,bar tunatune kawai. Kai Garba ya kad'a,kan ya kallo Salman. "Salma.. Kalloshi tai,bata tunani ta ta6a ganin Garba ya zama serious haka, hakan yasa ta bashi hankalinta gaba daya. "Nasan nima har yanzu kina ganin baki na sakamakon zuwanmu na karshe gunki. Rantsuwa ya mata,kan yace "Ja'afar baizo ranar gunki da neman auren kisa wuta ba sam,asalima yazo ne danya sadaukar miki da farin cikinshi gare ki sakamakon sanin waye Alhaji Usman.. Kai ta dago tana kallonshi. Sai ya kad'a mata kai, Ja'afar din ta kalla,shima itan yake kallo. Yacigaba, "yana son ki samu farin ciki ne Salma,wanda yasan a gidan Alhaji dak'yar ki sameshi,dan kaf halin Alhaji ba wanda ba'a karanto mana ba,hakan yasa ya gwammaci ya baki ni,duk nai imani sai ya fi mishi ciwo sama da auranki a waje.. Ya kallo Ja'afar da murmushi, "nasan abuna. Murmushi sukai ma juna,tabbas hakane,dan da Garba ya auri Salma,da yana gani bashi ba sake ganinshi bare hulda da gidanshi. "Dan haka banajin da wanda ya kai Ja'afar son farin cikin ki,ki d'aure ki bawa abokina second chance a zamanku kamar yadda bukaci haka. Nan yai ta musu fad'an rayuwa sai y'ar hakuri ce,da sanya tsoron Allah a lamari,gashi sunji dad'in tawakallin tunda suna fatan in Allah yaso su maida aurensu. Kan Garba ya tafi sai da ya tabbatar kowa ya yafe. Zaure suka koma ta sa musu taburma. Kallonta yake suna ma juna murmishin so cikin kauna. Sai wani dan sinke kai take halamar kunya. Hatta Miemie ta gane iyayen sun dinke, sai kallonsu take tana murmushi. "Assalam Alaikum.. Kai suka dago,Ja'afar ya amsa. "Aunty Salma wai ana kiranki a waje.. Kallon Ja'afar d'in tayi, Shima ita yake kallo,sai yai mata murmushi. "Tashi muje naga wane tsageren ne wannan... Miemie ya d'auka itama ta tashi tana murmushi suka fita. Alhaji ne yasha gayu da babar riga da wata katuwar mota yana murmushin ganinta. Fuska ya tsuke ganin fitowar Miemie da Abbanta suna wasan su. Tana ganin Alhaji Miemie ta g'imtse fuska,murmushi Ja'afar ya mata tare da shafo fuskarta suka karasa. Hannu ya bashi dan su gaisa Alhaji ya juyar da fuska gefe. "Gunki nazo fa. Kallonshi tayi tana murmushi, "toh Alhaji,gamu ai.. Da halamar tambaya ya k'alleta. "Ban gane ga ku ba?.. Kina nufin dashi zan ganki?.. Ja'afar d'in ta kallo tare da Miemie dake kallon Alhajin duk rai had'e daga shi har y'ar. Murmushi tayi tare da matsawa kusansu suka jeru mishi a gaba. "Alhaji, kai hakuri, kai hakuri,ka daina zuwa,InshaAllah aurenmu zamu mayar da Abban Miemie.. Ka d'auka zaman mu yazo karsh.. ka d'auka rabuwar aure na da kai da auran duk had'i ne na Allah... Ja'afar ta kalla tai mai murmushi tare da shafo fuskar Miemie. "Kai hakuri na na zauna da iyalina, ka yarda sune farin cikina, ni ce tasu,kai hakuri pls... Kai ya kad'a,tare da kallonsu,duk daga gani suna a farin ciki.. Tabbas yasan yai sake,gashi ya tashi a tutar babu,ba Halima ba Salma,ba su Nabila ba Miemie... Wa zai gane a jiya yayi nadama?.. Ya zasu gane yasan dad'in jin motsin D'a kusanshi a yanzu?.. Wa zai gane ya hakura yanzu kam yana son zuri'a?.. Murmushi yayi yana d'auke kai,kila haduwarshi da Salma sanadin shiryuwarshi ne,koh yanzu ya gode Allah. Kai ya kad'a tare da masu fatan alkairi, k'warai tai mamakin jin harda mata godiya a bisa gaskiya da take tsage mata. Hannu ya mikawa Miemie fuska d'auke da murmushi. Kafad'a ta mak'e tare da lafewa a kafad'ar Abbanta. Mota ya shiga tare da fitowa da leda cike da shopping na chocolate da ice cream.. Alawa daya ya fito dashi tare da fad'in "Zan baki sweet fa,zo mu gaisa mana Miemie.. Salma ta kalla kamar mai jiran umarninta. Murmushi tai mata tare da daga mata kai,abin kai sai taje ba musu,yau sai ga Miemie harda ma Alhaji dariya. Da zai tafi hannu ta daga mishi tana mishi bye-bye tana dariya. Duk sai Alhajin ya bata tausayi Alhajin,har Ja'afar na daga mata gira halamar tambaya. Marairaicewa tayi tare da shagwa6e fuska. "Y'arka ta rabani da Alhajina shikenan kunji dad'i.. Harara ya sakar mata kamin yace "toh bishi, Allah yai ma y'ata albarka yarinya mai kishin Abbanta koh? Kai ta daga mishi tana dariya,da murna ya shillata sama ya chafe suna dariya. Gwalo yai ma Salman,sai Miemie ma ta hau mata,tuni ta fara chunno musu baki suna cikin shagwa6a. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 11 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 46_Ba sauran jira,dan karara suke nuna ma fitsara a gidan Mama, su Ja'afar abin nema ya samu,ba guntun fulako,ba shiri ta bama Abba shawarar ayi a mayar da auren nan. Wata daya aka sa suka sha biki kamar ba gobe.. Nan take jin labarin auren Bintu a gidan mai mata uku,tana chan ta zama bora. Su Maman Abba duk sun halarci bikin nata,nan take tsurkuta mata labarin Maman Ummi kan ranar ta fita gantali miji ya dawo,bayan ta dawo yace ta nemi inda dare ya mata,karshe dai akai saki. Murmushi tayi,tasan Allah ba azzalumin sarki bane,dole yadda taga tasku Maman Ummi tagani itama. Jingina yayi a jikin bango yana kare mata kallo,fuska rufe ruf da g'yale,murmushi yayi dan tunawa da daren farkonsu a wanchan gidan. Karasawa yayi tare da g'yaran murya kad'an yana leka fuskarta. Zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya. A hankali ya kai hannunshi tare da daga mayafin da ta rufe fuskar. Tsam yayi yana kallonta ido cikin ido,tuni ya marairaice mata fuska,kuka fa?.. Hannu yasa yana share mata wani na zubowa,duka ya hayo gadon tare da janyota yana shafo bayanta halamun tai shiru. Sai da tai shiru kan ya dago kanta. Ido suka zuba ma juna ba koh kiftawa. Chan ya nisa cikin murya kamar mai jin bacci yace "Kin tuna kalaman da na ta6a turo miki na karshe cikin text message dina kuwa?.. Tunowa ta fara,sai yai murmushi tare da zamewa kan katifa da ita a kafad'arshi. Ajiyar zuciya suka sauke tare da kamo y'atsunta. "Na ce miki _" a heart dat truly loves never loses hope..but always believes in d promise of love,no matter how long d time and how far d distance,at d right time,love will fine a way".._ "Hope kin yarda da maganar ba wai soki burutsu Masoyinki bane?. Kai ta daga mishi halamar ta yadda,tunda ga nan K'ADDARAR wani zama ya kara had'a su waje daya. Yau kam ya gama gasa mata jiki da d'anyun kalaman da ya tanadesu kawai da Salmanshi,fatanshi Allah ya kare sa6ani a tsakani. Washegari da t'sant'sar farin ciki suka tashi,suna kitchen had'a break fast sai nannan yake da ita. Tashin Miemie suka ji tana kiran Aunty cikin kuka taga sabon waje. Ganin iyayen waje daya ita kanta sai binsu take da kallo, mot'si kad'an ta kallesu,kamar wacce bata so su rabu da juna suyi rayuwarsu tare. ********** Yau ziyara aka fito ta sallah ita dasu Ummi, Sun zaga duk inda ta tambaya saura gida 1 taga sun karkata zasu shiga gidan kawunsu wanda jiya sunje. Ja tai ta tsaya tare da ce musu su shiga su fito dan yau bata tambayi nan ba. Murmushi Aunty A'i tai tare da kad'a kai,a lalle kullum Salma hankali na kara zuwar mata. Tuni Ummi kam tai gaba tana t'saki. Tana nan tsaye kawunsu ya fito a gidan,bayan sun gaisa yace mata ya bata shiga ba ga y'an uwanta suna ciki? Kai a kasa tace "Abba ban tambayi nan ba ne,dan jiya munzo yini. Murmushi yayi na jin dad'i, "hakane kinyi tunani mai kyau,Allah ya miki albarka. Kai ta kara kasa kamin ta amsa. Kud'i ya ciro daga aljihu ya kirga dubu ya bata,dan sosai Salma tana wa mutane bazata,yana matukar son mutum mai gyara kuranshi. "Sannu da jira uwar y'an ka'ida... Juyawa tayi daga kallon wani a mota sun tsaya da Kawunsu da ya wuce yanzu,sai dai kan ta tantance su Ummi sun fito. Murmushi ta mata tare da basar da zancen suna tafiya. "Wannan ai wahala ce,ace duk inda zan shiga sai miji ya ban izinin shiga?.. Kai ta girgiza, "gaskiya da sake.. Hararar da Aunty A'i ta mata ne yasa tai shiru. Kallo Ummin tayi da murmushi, a irin hudubar nan a baya suka dilmiyarta,ita kwa yanzu a shirye take da yima Ja'afar biyayya matukar bazata sa6a Allah ba. Har akaje gida nan ma Ummin ta hau zaiyyanawa Mama halin da Salma ta tsiro, tuni Mama tai mata kacha-kacha,Ummi harda kukan takaici ranar. Da dare yazo ya dauke su,sai taga a motar Garba da kamar ta ganshi dazun. Taga anje gida yana kokarin rufe mota da abin rufa sai ta kasa d'aurewa ta tambayi nan zata kwana? Murmushi ya mata tare da bud'e gida. Sai da akazo kwanciya yake sanarta ai shine albishir din dazun da yace sai sun zo gida. "Ya sai sabuwa ne,sai mukai cinikin wannan dashi tawan, munyi abin hawa. Murna tai ba kadan ba tana k'allon mukullin motar. Ido ya zuba mata yana kallo ba koh kiftawa. Baki ta kai kan idon tare da hurewa. "Salma.. Hankalinta ta bashi tana murza yatsunshi cikin nata. "Daga yau na yard'e miki koh ba idona ki taka ko'ina u r free... "Dazun naga komai Salma,ina horn bakiji bane,kin sani farin ciki dazun kinsa naji ni din na isa gun matata.. Duk inda ta tambaya nan zata jefa kafarta. "Sai ganan kuma kawu shima ya labarta min yadda kuka yi sai murnar wai kin san ya kamata yake.. "Nagode sosai,yau har kawu yasan ni mai fad'a aji ne a gidanshi.. Murmushi tayi tana kara ruk'unk'umo shi. Ta gode Allah da yasa ta gyara dabi'ar ta maras kyau ta maye mai kyau. Fatanta duk wata mace mai irin halinta ta daina,dan ita taga misali akanta. Dan a yanzu rayuwarta ta fi mata dad'i da kwanciyar hankali, ta gane yanzu kulle ma wasu matan ke ja ma kansu, tana fatan kowacce mace ta guji fita a bisa sharad'in *A BAKIN AURENKI* da suke yi,dan gudun haifar da saki irin nata mai gabadaya. Alhamdulillah.. Nan na kawo karshen littafin A BAKIN AURENKI.. Ina rokon Allah kuskuren da nayi ya gafarta min. Da fatan darasin ciki ya isar masu halin Salma za kuma su gyara,Allahu ya datarmu aikin kwarai a gidajenmu. Gareku dubin masoyan Feenat Novel's, na gode kwarai da kaunar ku gareni,Feenat na son duk mai sonta, dama wanda bai yinta.. Luv you all. Sai kun sake jina a sabon littafi mai sunan... *RABO IN YA RAT'SE*... Nafisa Bashir Tanko, (Feenat Ja'afar) SAI NI ADMEEN ABDUL MUKE muku fatan saduwa da alkairi.